Sashe 168
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallama yayi ya shigo part din mommy ce ta amsa take fadin a, a ina kuma ka tsaya ai na dauka ka tafine don yaran sun fada min kazo tundazun na dauka Alh kazo gani bai nan ka tafi. Ban tafi ba dama baby ce nazo gani ina part din anty ne tundazun din da sauri mommy tace me kuma ya kawoka wurin baby da uwarta ? Yana kaiwa zaune saman kujera yake fadin akan sha,anin bukintane don dazun ta sameni gida nace tazo zanzo na ganta shine yanzu nazo. Wani kallo uwar har yan uwanshi ke masa yace ba wani abu bane dai nine nace tayo min list don abinda take so shine ta kai min daga haka yaja bakin shi yai shiru bai kara magana ba kuma. Idon ta kara zuba mai tana fadin ka fitar da kanka cikin zancem nan don koni uwarka ba,a saka a cikin shi ba banga dalilin da kai zaka wani zake ba haka ? Ta manta cewa nima idan Allah ya kawo lokacin gani dasu har uku a gaba dama tayi hakanne don kawai ta kumsa min bakin ciki take tunane . Ta nuna yaran nan basu da farin jini gashi har yarta ta isa aure ta samu manemi su suna zaune a gida shine kawai sai kuma dan kudin da yaron ke nuna masu yana dashi yanzu kuma. Haba mommy ki daina damuwa da irim kananan maganganun nan don Allah suma din ai lokacine baiyi ba idan lokacin yayi yi zasuyi ai. Yana fadin haka ya mike yana fadin zan koma mommy sai dai gobe in Allah ya kaimu don zan tafi abuja din a goben nan idan Allah ya yarda. Ya kara mata sallama ya fita ba tare da ya fadi abinda yazoyi wirin su hjy katima dinba yana fita Nabila tace aiso nayi mommy ki tambaye shi muji ko wani abu ya basu ai. Haba kema ai kin sani tunda kikaji ya fadi hakan aikin gama ya gama ko kwanan zakiga anfara sha,anin bukin nan gadangadan ke nan ashe hauwa ta fada daga inda take zaune. Tsuki mommy tayi tare da fadin koma me zai basu indai wanan matarce ba zai taba haske ko ta wani so shiba indai itace. Mommy shifa yaya ba don ta yayi ba ai kinji abinda ya fada baby din ce ta tafi wurin shi dazun ta ganshi yayine kawai don zumunci hauwa ta kara fada uwan taja wani irin tsuki tana jin wani iri a zuciyar ta. Office din yai shiru dan dakikun mintina ba zamu zauna a yau ba don lokaci ya danja yanzu sai dai gobe idan Allah ya kaimu yanzu a samu wanda zai bude mana da addu,a bayan nan sai mu fita ga baki dayan mu zuwa cikin kafanin muga abinda mukazo zama a kanshi na fada. Kallon kallo aka fara a tsakanin mu dasu jin abinda na fada wani daga cikinsu mai dan tsawon gemu ya fara da sallama. Takardan dake hannuna nake karantawa har lokacin da suka shafa nima na shafa din na kallo inda felix yake nace yai muna addua ya dan kalleni ya fara. Gaba daya muka mike muka fita wanan da yai muna addu,a shine ya jagorance mu yake nuna muna wuraren ai kafin kace me har an samu wanda yaje ya rsuguntawa manager ga abinda aka hangomu munayi a lokacin. Don me ba zamu takawa yarinyar nan burki bane rankayadade haka kawai mu zauna karamar yarinya tazo tana kokarin juyamu muna zaune. Nima abinda na gani ke nan ai gara mu nuna mata nan fa arewane ta shigo ba kasan su ba ita din me don Allah oga bala. Kyautane zai rudemu ko shigarta na banza me akayi akayita ma da har take batun bude muna zani a kasuwa muna kallon ta in abin nan yayi nisa fa duk kan mu nan zai shafi kowan mune wallahi. Shafa kai don duk masu laifi muke ai manager ya furzo iska waje daga cikin bakin shi yana fadin don me ba zamuyi wani dabara na sallon sayenta ba mu gwada mu gani idan hakan zai yuyu. Da nawa kake ganin zamu saye ta a wuce wurin daga milliyon daya zuwa sama zamu fara kaftawa mu gani amma muddin muka bari wanan abin yai boosting wallahil azeem kowan mu nan sai ya raina kan shi cikin mu yanzu meye abin yi ke nan. Abin yi na farko shine duk wani wanda ke da hannu a cikin harkan nan a sanar dashi ya kwana a cikin shirin kota kwana don fitana idan an san farkon shi ba a san karshen shi ba. Tunda nake ban taba kawo sense ko yarda akwai wani abu a kaina sai wanan ranan tawa ta farko dana ziyarci company nan kai rayuwan nan ina zaki damune wai. A yanzu yan Annabi a baki Fir,auna a zuciya sun fi yan son abi a zukatan su yawa don zaka ga mutum har mutum amma kada ka tona kaji aikin da yakeyi a bayan kasa. Meyasa tsoron Allah yai karanci a wanan zamanin hakane har kafiran masu bautan wanin Allah suna sun sufi musulmi gaskiya. Nace hakan ne don zamana a cikin su ina rayuwa sai kadan dinsu ne ke saka ransu ga abin wani idan kaji sunce dakai i swea to god iyakar gaskiyan ke nan suke fada lokacin. Amma a yau sai dan musulmi ya rantse ma da Allah bisa kan karya koda kuwa yasan gaskiya yake karyatawa a kan karya saboda rudin duniyan nan ubangiji Allah kasa mufi karfin zuciyar mu Amin. Don naga abinda basu zata ba a filin Allah saidai zan bisu a yadda suke son mu tafi din har mukai karshe dasu hakana. Kaci nawani ka raya kanka da iyalan ka yaya kake zaton diyan ka da ka tayar a cikin haramun zasu kasance suma zakaga mutum yana kwalliya da haramun yana tunkaho a cikin ta kamar ba ranan haduwan mu da Allah. A gajiye muka gama zaga ko ina muka dawo office din mu zaman mu ke nan saiga abin sha an kawo muna masu sanyi da cake. Yemisi na zama take fadin duk ta gaji ta mika hannu zata dauki drinks din nace don't ta dago kai ta dan kalle ni kai na kara kada mata alaman a, a dai tayi saurin ajewa ta daga. Sabbin abokan aikin nawa suka zuba muna ido don rashin fahintar abinda ke gudana a lokacin. Harshe na juya da yarbanci ina fadin duk wanda zai sha ko yaci ya fita nisa da wanan wurin yasai duk abinda yake bukata don wanan din hanyar dauremune aka dauko haka. God forbid ta fada tana fadin iam testing let me go and find something to drink . We can go home now sai gobe don Allah kowa ya fito da wuri na fada na juya wurin wa yan nan mutum uku din ina fadin mun gode da lokacin su da suka bamu da fatan zasuyi hakkuri a cin ma manufar wanan aikin a tare dasu. Tare muka fito zuwa haraban aje motocin company ina kallon yadda mutane sukayi gungu gungu suna gulman mu a lokacin kowa ya shiga motar shi muka nufi gidajen mu. Da yake azahar tayi tun muna hanya muke jin kiran sallah a wurare don haka ina shiga gida gaisawa kawai mukayi da umma na shiga dakina nayi shirin sallah. Na idar ban fito ba karatun alkur,ani na soma yi sosai cikin daga murya duk wanda ke gidan zai iya jina a lokacin. Har lokacin la, asar yayi na mike nayi sallah na shafa na fito na samu umma zaune tare da maniya suna hira muka gaisa da ita take fadin ashe ba barci nakeyi ba don shi maigidan ta tun shigowan shi ya kwanta barci wai yau ya gaji da yawa yace. Murmushi nayi ina fadin na dauka zai fitane zancen karatun yaran nan amma yanzu yamma tayi ni zan fita gobe kafin in shiga office mu nema masu inda ya dace dasu. Abinci fa umma ta fada muniya tace bakici abinci ba tun lokacin da kuka dawo Sahiba ai ita wanan yemisi din nan gidan mu tazo ta karbi abinci taci. Tausayi yemisin ta bani kamar ba ita ba yadda tayi laushi a yanzu tun zuwan mu nan arewan don itama taso tazo tare da mahaifiyar ta sai sukai shawara kan ta fara zuwa taga yanayin wurin ita. Abincin na debo na dan fara ci a lokacin kuma muniya ta fita daga part din mu tsakuran abincin nayi na kai na aje a kitchen waje na fita don kallon yanayin sabon wurin namu. A hankali nakai hannayena saman kirji na sauke ina lumshe ido tare da shakan iskan dake kadawa mai sanyi a lokacin. Dan takawa nayi na jingina jikina kan dan adon da akaiwa kofan shiga gidan namu wanda kusan ko wani gida akwashi a wurin. Bin gidajen wajen nayi da kallo sabon wurine da gani saboda ba mutane sosai a gidajen kusan ma mu din ne nake ganin farkon shi gidajen da aka gina su ko muzo na biyu don yaran dana hango dan nisa damu sun fito a cikin shirin islamiyan su lokacin sai kuma naga wani ya fito ya bude mota sun shiga . A gabana sukazo suka wuce na dan bi yaran da kallo hakan yasa na nasa a raina cewa zan samu lokaci in masu magana game da karatun su Amar don yanzu yana secondry ne a matakin farko. Na dade a wurin don har nakai ga kaiwa zaune ina nazarin wurin kafin magariba yayi in shiga ciki don sanyi ya kara saukowa sosai a lokacin. Sallah nayi na samu wuri na kwanta kasa a falon ina tunanen mai gobe zai haifar garemu in Allah ya kaimu gaskiya karatu yana da dadi ga dan adam sai dai idan Allah bai nufi bawa da yinsa ba. Da badon jajircewan da Allah ya nufeni da yinsa ba na dage har na cin ma wanan manufan da ko wace uwa take gurin ganin haka ga abinda ta haifa da muna can wullakace ina faman tallah da neman dakon abinda zumuci. Rana na farko ke nan danaga aikin alherin da ya Abubakar yayi min a rayuwana don shi mutumin daya dorani a matakin farko tunda da har