← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 193 OF 337

Sashe 193

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ikon Allah mommy ta fada tana ajiyan zuciya takai kallon ta ga hauwa data aika tana zaune har lokacin ki kira min ita nace dake da sauri hauwa ta mike don zuwa kiran Nazifa din a kofan ta suka hadu hakan yasa hauwa ta juyo. Kusan tare suka iso falon da Nazifan don batayi mata magana ba itama haka ta iso tana fadin sannu da zuwa ashe harkun karso ta samu wuri ta zauna saman kujeran dake fuskantar na mommy din. Idon shi ya lumshe cikin jin kuna da zafin rai bayan na ciwon dake damun shi a zuciyan shi yace bai ci komai ba tun safe mommy ta fada tana kallonta wai abu mai dan ru, , , , Ke baki iya gaida babba bane ko bako ya fada yana kallonta ido jajir a lokacin saida ta wani kalleshi kamar tana mamaki da maganan shi kafin tace. Nima ai naga ba a gaidani ba kuma ni akazo aka sama a gidana ai nagani wani irin zabura yayi daga saman kujeran zakace bashi bane mara lafiya dake takawa da kyat ya fito a lokacin. Wa kike fadawa hakan mommy dince zata gaidake ko wa a cikin su ke kin gaida mahaifiyar sune balle kiyi mutumcin da za a gaidake ? Har kina fadin ke aka sama a gidan ki inane gidan naki ki fada min yau idan na hada kudi da wani naki nagina wanan gidan ? Modibbo mommy ta fada da dan karfi cikin bacin rai ya kallo mommy tace koma ka zauna tana da gaskiya don gidan ta muka zo ba karya ta fada ba ta mike tsaye tare da duban yaran tana fadin ku taso mu tafi Allah ya baka lafiya. Mommy ina kuma zaku akan wanan da ko dabba yafita sanin darajan dan adam a wurinta yaja wani irun tsukin takaici da bakin ciki wanda shi kadai yasan zafin da yake ji a zuciyar shi lokacin. Eh ai gara mu tafi irin hakan ke hana ko yaran nan in turo gidan nan wallahi bana son diban albarka ke kuma ki sani wuri daya na fito da mahaifin ki don haka na wuce raini a wurin ki ko wanin ki. Ni yanzu me nayi kawai sai mutum na zaune kalau za a samu sherin da aka lakaka mai nima ai hakan yasa bana zuwa gidan naku. Kada kije mana dama wake son ganin ki ko zuwan yanzuma don dan uwan mu mukazo gidan nan idan bashi ba wa zaki gani a gidan nan Nabila ta fada. An daiyi hasara a koma gida a koyi ladabi wurin gyatuma hauwa ta bada a daidai inda zata wuceta cikin kashe murya ba tare da kowa ya jita ba. Bani nayi hasara ba sai ku da kuke zaune a gida ko kare bai taya ba kece kika buda muna hanya indai kwantai ne saida aka roki yaya ya daure ya dan jona ki jaka. Fau taji ta gwauce dukan bai sameta sosai ba mommy ce data dawo da baya bayan jin fada ya kaure a tsakanin su takaiwa hauwa din duka ta noke ta samu bayan kanta har dan kwalin kanta yana batun faduwa kasa. Ke kuma Nazifa zaki biye mata ku zubarwa kanku mutunci idan ita bata da hankali aike kina da hankali ko ? Saidai ta zubarwa kanta da mutunci don ni tasan nafi karfin ta ga komai takoma can tayiwa wa yanda ta saba yiwa bani ba nan don ba zan kyale yarinya ba. Mommy ta gane metake nufi hakan yasa ta juya rai bace tana fadin Allah ya sauwaka kai kuma Allah ya baka lafiya tafita daga gidan sai bayan sun shiga motane suka hango shi ya dab tako yafito daga kofan falon ya rike da hannun sa daya . Saida yaga tashin sune ya koma zuwa cikin gidan har lokacin Nazifa tana tsaye tana yankan kauna bata da niyar bari daga kofan ya dagata yana fadin ke ma yanzun nan basai anjima ba ki fice min daga gida. Akan wanan maganan zakace na fice ma daga gida ba inda zan tafi dama abinda ya kawo su ke nan yanzu don suja min matsala tsakanina dakai kuma sunja din don haka babu inda zan tafi. Haka kikace yau idan kika bari na fito na sameki a cikin gidan nan sai rayuwan ki yayi bala,in baci fiye da tsamanin ki yana fadin hakan ya sakai zuwa dakin nasa . Ba zai iya kwanciya ba a lokacin din haka kai tsaye ya bude wardrobe din shi ya ciro kaya daga ciki yana sakawa a jikin shi. A can ko yar aikin tane take fadin hjy tunda kinji abinda ya fada gara ki sameshi ki bashi hakkuri son ba,a hakan da kikayi din . Kamar kinci masa fuskane fa ga mahaifiyar shi a tsaye kike jefawa yan uwan shi wanan kalamin haka kiyi hakkuru ki bisa daki ki bashi hakkuri zai fi. Wani irin kallo ta watsa mata kafin ta kawar da kanta takai zaune bata hakkura ba dai ta sake fadin hjy yi hakkuri ki sameshi a dakin shi don Allah. Idan namiji ya fadi hakan yana nufin haka har cikin ranshi ne mikewa tayi zubur ba tare data kalli matar ba ta nufi dakin shi. Agajiye na dawo gida bayan wucewan ogan mu na zauna ina cin abinci ina ba umma labarin zuwan shi da abinda ya fada game dani. Yaushe zai koma ai ya tafi ko ba kasan nan dama yazo ba kawai ya ratso yaga aikin mune dukan kofan da akeyi ne a lokacin ya dakatar damu duka. Ammar ne ya mike don hankalin shi na kallon ball da yakeyi ga kuma littafi a gaban shi nasan ko nayi mai magana hankalinshi zai kasu biyune a lokacin yasa na kyale don nasan da an gama ball din zaiyi abinda ke gaban shi. Yana bude kofan ya Abubakar ne tare da yaran shi a kofan da sauri ya kara ja baya daga kofa yana basu hanyan shigowa ciki. Nima dai da mamaki nake kallon shi daga inda nake zaune umma ne ta samu bakin fadin a, a yau da baki kake muna tafe ashe ? Yayi murmushi yana kaiwa zaune tare da dora yaran saman jikin shi ya fara gaida umma tana tambayan shi ko lafiya ? Ya dan dago yana murmushin dole tare da fadin bana jin dadin jikina wallahu mama shine kuma kafito hakan yace wallahi umma. Inda nake ya kalla yana fadin Sahiba ko zan samu abu mara nauyi in ci yanzu ? Umma ke fadin tashi maza ki duba a samu abinda akai masa yaci na mike zuwa kitchen din na dan tsaya ina duban kayan dake kitchen din kafin na dora ruwa saman gas. Abincin mai sauki nayu mai hade da kunun gyada na kawo mai a dinning da kyar ya dago zuwa dinning din tare da yaran da nake satan kallo yan mata su duka biyun . Ba laifi gaskiya yaran kama da yan uwa sukeyi suma sai dai na kasa tuna fuskan Nazifa balle na tantance fuskokin nasu kowa suka biyo ga kama. Muryan shi naji yana fadib kizi ki dauke su a nan zan barsu in zan tafi da sauri na juyo ina kallon shi da mamaki umma sai cewa tayi lafiya ko modibbo ? Dan murmushi ya sauke kafin yace lafiya mama nakawo su nan ne kawai dai ya fada sai ya mayar da hankalin shi wurin cin abincin dake gaban shi faten wake yaji kayan hadi a cikin sa dama mun jika wake kamar yadda mukan jika shi yayi awani idan zamu dafa saboda saukin dahuwa a saukake. Da alama yaji dadin dahuwab sosai don idan kin jiki yafi dadi a wurin ci da daukan kayan hadi bai kara magana ba saida ya gama. Ya dawo saman kujera ya zauna yana fadin mama a nan zan bar yaran nan su kwana biyu tare daku don nasan babu wanda zaisan suna gidan nan. Meke faruwa umma ta sake tambayan shi nan ya fara jero mata irin cin mutuncin nazifa dabai tsaya a gareshi ta hada har mommy da yan uwan shi. Nima dai sam banji dadin hakan ba gaskiya don nariga da nasan ko waye Nazifa akan kujeran ta taci min mutunci a baya don haka ba zan manta da ita ba a rayuwana gaskiya. Sai kuma yaran suka ban tausayi don laifin uwarsune yanzu yake kokarin shafan su ke nan saidai naji umma na bashi baki yana fadin yana son ya horata ne umma tayi hakkuri don Allah. Zai tafine yabada kudi wai a saya masu abin bukatan su sai idan ya dawo da sauri nace no ka barshi kawai yaya zan saya masu komai insha Allahu. Har yakai bakin kofa nace kira sunan shi yaja ya tsaya wuri daya ba tare daya juyo ba nace ya Abubakar kana ganin kawo yaran nan gidan nan yin hakan ba zai jawo wani matsala daga baya ba ? Saida yaji nayi shiru ya juyo yana fadin Sahiba shin akwai wanda yasan kuna garin nan ne bayan ni ? Kai na girgiza mashi yace OKey ta yaya kike zaton wani zaiyi tsamanin a nan suke ga gobe zanyi tafiya nima don haka kada kiji komai a ranki saidai idan zasu damekune a nan din in canza masu wani wuri. Kafin inyi magana umma tace haba dai koba diyan ka bane modibbo ai zamu rike ma balle diyan cikin kane wa yan nan kada kaji komai a kan zaman su a nan din. Yace yagode yasa kai ya fita muryan yarinyar ne yayi sanadiyar juyowan mu ga barin kallo mamakin da muke mashi na ya tafi ya barmu da yaran a gidan take fadin. Ina daddy mu ta fada kamar bata magana da farko irin haka idan kaganta don karantan su ita dai karaman har lokacin tana jikin umma a lafe da alama bata da rikici. Fuska kumshe da murmushi nace daddy yaje ya sayo maku alawa yanzun nan zai dawo na fada ina mika mata hannu tazo wurina. Kin zuwa tayi ta makale a jikin kujeran daya tashi a kai tana wasa da hannayen ta mikewa nayi daga inda nake na shiga dakin umma na dauko masu biscuit da sweet din amar masu dadi na kawo masu. Abin mamaki sai
Chapter 193 · 0% Book details