← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 337

Sashe 59

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma kan abin duniya ya isheta yakai mata inda yakai don bata taba tsamanin za,a iya gano su din ba da sauri haka sai lokacin da yaranta suka isa idan girma ya kawo masu zata kwashesu su koma gida. A cikin wanan jimamin na umma ne kuma washegarin dawowan su gida daga asibiti sai kuma ga mota da jiniya har kofan gidan. Kai bayerabe bai iya samun abu ba a rayuwan shi don su basu raina abin gulma gashi kuma ko banza umma ta kasance ba yar kabilan su bace ita. Din wurin namu Ajata sunfi yawa wa yanda akewa kirari da (eleyele) ma,ana farar tatabara da harshen su na yaroba ke nan. Hakan yasa basu tsayawa umma din ba saidai su taru suna kallon abinda ke faruwa idan sun watse su samu abin gulma gun hausawa. Yauma suna jin motan ta tsaya a kofan dan gidan namu na icen bamboo tree sukayo wurin caaa suna kallo. Shugaban tawagan ya fito ya shiga wurin umma sun dan dade tare suna ganawa duk lokacin yan gulman na wurin tsaye sai kara yawa da sukeyi a wurin kowa da irin karyan da yakeyi a lokacin. Acan cikin gidan kuma ummace da Ladi a dakin bayan sun gaisa yana bin ko ina na dakin namu da kallo a cikin tausayi da jimamen yanayin rayuwan da muke ciki a gidan yake fadin a ranshi koda ya kasance basu bane nake nema din. Wa yan nan mutane abin tamakawane matukar ba harkan banza sukeyi a garin nan ba son yawancin hausawa abinda suke bata rayuwan su dashi ke nan idan sun bar gida. Sai gashi kafin yai magana ya fara tsuntar wani abu ga bakin ladi dake ffadin mairo ki fada mai koda ya kasance bakr din duke nema ba. Don ki ceto rayuwan yar ki daga ukuban nan da kuke ciki keda diyan don Allah ya gani yau kusan shekara goma sha da zuwan ku garin nan baki cikin kwanciyan hankali daga ke har yaran ki. Don ma Allah yayiki natsatsa daga ke har yaran kin kama kanki da mutuncinki Allah kuma ya tsaya maku yana duban ku tunda baku raina mashi ga dan abin da kuke samu ga rayuwa ba. Wahalan ya isa haka mairo Allah shike kashewa yana rayawa ba wani ba har idan Allah ya kadara rayuwan ki dana diyan ki a hannun yan uwan mahaifinsu yake ko nan ida kuke sai sun biyo ku sun kashe ku din. Wanan kalamin yasa ya dago kai ya kalli Ladi din dake magana yaga tsohuwar yar barikice ita rikakka da ita don tsoro ya mutu a idon ta ko a yanzu. Kai ya mayar wurin umma din dake duke ya dan saci kallon ta hjy maryam ya fada a zuciyar shi da sauri ya tunota ya gano ko wacece ita din a yanzu duk da wahala da girma yasa a yanzu kamanim ta yadan sauya sosai bisa ga yadda yasanta din. Ga mamakin ta taji yace babba maryam wai dama kece din kuma kuna raye yan uwa suka shiga halin kuncin rashin ku a kusa daku , ? Itama umma din kai ta dago tana kallon shi da alama har lokavin bata gane ko waye a gabanta ba har lokacin don koda ta barsu bawai ta wani sanshi bane sosai a lokacin. Itama kai ta dago tana kallon shi don jin yakira sunan ta kamar yadda yawancin yan gidan suke kiranta da wanan sunan . Duk da kasancewan ta karama sa,an yaran don da wa yandama suka haifeta a cikin su amma darajan kanin mahaifan su tace suke kiranta da wanan sunan a ko ina. Bam, , shedakaba ta furta kafin tace dashi kuma dan wajen yaya DCP ko yace nice baabba. Tace da kama nayi amfani na ganeka amma badon na sheda ka na gane ka ba ya dan murmusa ya gyara zaman shi tare da fadin. Baabba me yasa kika guji gida kika dawo wanan wurin nisa da yan uwa kika zauna anan cikin kunci haka ga talauci da gatan ki baabba? Har yau gidan ku na nan ba kowa a cikin sa kamar yadda kuka tafi kuka barshi ba wanda ya taba ko tsunke a gidan kullun ana duban zaku dawo ko wani lokaci. Kaiya dawowan mu ai yana da wuya a wanan gidan sai dai wani ikon Allah dai kuma idan Allah ya nufi komawan mu gida ta fada a cikin hawayen daya gama wanke mata fuska ko a lokacin. Wani irin ba dadi yaji har cikin ranshi don a matsayin shi na jami,in tsaro ga maganan umma din ya gane akwai wani abinda ta sani na boye da kowa bai gane dalilin gudun nata ba daga gida. Umma din tace dashi ya wajen mahaifana ko sun saura a raye yanzu ko suna wani hali. Kai ya dukar kasa don baisan amsan da zai bata ba a lokacin sai cewa da yayi duk kowa yana lafiya baabba. Sai dau yau gaskiya ba zan kara barin ku kwana a cikin wurin nan ba zamu tafi daku can inda nake in yaso idan kun huta sai muyi magana don naga har yanzu akwai sauran damuwa a tare daku. Amar dake gefen umma din a tsorace yace cikin yarbanci umma tsoron wanan nake ji sosai ya kallo yaron da yai magana yana fadin ya kake abokina yana mika masa hannu Amar din ya make yana labewa bayan umma din. Ladi dai ido ta zuba masu cike da mamaki a ranta na ashe umma din dai mai gatace haka tazo nan ta zauna a cikin rashin galihu. Kai koma meye wanan dalilinn yana da zafi da daure kai gashi sun dsakartar da zancen data so taji don umma taki furta komai ga kowa tun ranan da ta shigo lagos din ta zauna dasu har wanam rana. Yazun kan maggi ya kama kan zabo don hjy karima ta samu gidan a yadda take so don a dan kankanin lokaci ta samu kan kowa na gidan kamar yadda take son samu din. Yanzu kan daga ita sai diyan ta kaje ji bakin Alh din abu kadan ya hau hjy Adda da fada ko zagi ido rufe. A takaice dai yanzu gidan yana kamar under control din hjy karima ne a yanzu duk biye suke da ita a gidan abinda wasu mata da dama suke butin samu a rayuwan su ke nan saboda dan zaman duniya na lokaci kadan mace zata iya sayar da lahiran ta kan hakan a banza. Abida komai yawan shekarun ki a duniya ba zaki tsufa irin na duniya ba a rayuwan ki akan wanan dan zama na lokaci yar uwa zaki yarda ki halaka kanki da kanki don kawai huduban shedan da shedanun yan adam ? Ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu akoda yaushe mu tuna kidhin nan fa na dan lokacine don baki san abinda kika debowa rayuwan ki ba zaman ki na duniya. Shin yar uwa idan har kin mulki kishiya da miji da yayansu zaki fitane ki mulki duniya ko garin ku baki daya ? Kin gani muyi kishi irin na wayewan kai mai ma,ana da fahinta kada ki yarda a cutar dake ke kuma kada ki cutar da abokan zaman naki don rayuwan yar kalilance a tare dake. A irin wanan halin ne da daman da ta samu sa,a gun bokanta a yanzu take taka kambon ta a dakin tafito tana tako daya daya daga part din ta a cikin shirin kwaliyan ta na fita unguwa wanda a yanzu kusan kullun sai ta fita a gidan. Ga idan akace gari ya waye da sabon iya shegen da zata tsiro wa mutane na iskancin kada dai a zauna lafiya don kawai ta musgunawa yan gidan ta nuna ita din itace dai a gaban komai. Har yakai yanzu yan uwan miji da suke yan uwa ga ita hjy Addah suna kokarin juyawa addah din baya don sai su shigo gidan ba tare da sun shiga part din hjy Addah din ba harsu fita. Don kawai a nasu zaton ita zata iya sa mijin su yai masu abinda suke so ko ya biya masu wani bukatan da suke dashi da sauri. Saidai kaiya yan adam basu gane hakan ba don irin matan nan da kansu kawai suka sani sai yayan su akarshema sune masu hana miji yaiwa yan uwasa alheri din don tsaban bakim ciki dake cin su a jini. Wasu kuma zasu dinga amfani da yan uwan mijin suna tatsar dan uwan su wurin ya bayar idan an bayar din sai su rage su tura a aljihun su. Su Nabilane zaune da kawayen su da suka zo gaida dija da bata da lafiya satin nan duk bata fita school na don fever dake damunta a lokacin. Gaida ita suka fara a cikin dan shaku tare da fargaba suma dai kawayen hakan har ta dan wucesu tana karbawa sai kuma ta juyo taja ta tsaya tana fadin. Amma dai baku da hankali duba yadda kuka bata falon nan kamar anyi fada a gidan gala kalo kalo suka fara a tsakanin su. Ta sake fadin ke kuma Dija daga ke har uwar ku da baku san ciwon kanku ba yanzu kin zauna a gida kince baki da lafiya baki fita school . Amma gashi yanzu muryan ki yana tashi har kofan gidan nan don kawai baku san zafin kudin da ake kashewa a kan ku ba ko me ? Oya yanzun nan ku gyara falon nan tasa ku kuma ta juya wurin abokan nasu da fada tana fadin maza kuzo ku fice a gidan nan tunda ba gidan holewa bane nan din. Tashi sukayi a cikin fushi don zagin barnan sunan da tayi masu din ransu a bace Nabila ta dago kai a cikin takaici ta kalleta tana fadin. Anty sunzo gaida Dija ne ba wani abu suka zo yi ba dama nace su fita ta dakawa yar mijin nata tsawa don kawai ta disgasu a gaban kawayen nasu ta nuna su din ba kowa bane a gidan nasu. Nabila da zata bisu ta basu hakkuri itama wani ashar din zagi da ta samu a wurin ta din jin hakan yasa hjy Addah cikin dakewan zuciya ta fito daga dakinta dayafi kusa da falon tana tambayan meke faruwa ne hakan
Chapter 59 · 0% Book details