← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 337

Sashe 200

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

zancen yarinyar nan kai da mommy sai ku dinga fadin cewa yar uwanmune su ta ina muka hada dangi da jikan yarbawa wata kila dai mahaifiyarta ce yar uwan su daddy ta can wurin dangin danga kawai ace wai muna da hadi da wanan mai zubin larabawan don dai yanzu na daina kiranta da jikan Oduduwa ai . Jiya Allah yaya don baka ganta bace ta fito kamar yar wani kasa ba yar nan Nigeria ba shigan da tayi jiya din kasan mutane da gulma ina jin wasu na fadin ko yar abokon business din daddymu ce sukazo kara. Nabila da bakinki kike fadan haka kan Sahiba koda yake ba laifin ki bane yanzu don baki san yaya alakan ku yake da ita ba shiyasa . Amma ki daina don watarana zakiji kunyan hakan da kanki wallahi idan kin san su din ko suwaye gare mu da kuma abinda kike takama dashi a yanzu zakiji kunyan kanki a ranan yana fadin hakan ya mike ya fita kawai ya barsu suna binshi da kallon mamaki. Tsuki nabila taja tana fadin shike nan don ta zama dan wani abu a yanzu sai ayi kokarin danganta alakan mu da ita kawai haka ranan naji Mommy ta fadi hakan har da muna fada a kanta nifa na tsani yarinyar ne kawai wallahi. Don tafiki kyau yanzun kuma kinji ance ga cigaban data samu a rayuwa ko me hauwa ta fada daga gefenta me zata nuna min wurin kyau nima inada nawa dirin sai me kuma ? Shi arziki yanzu yin shi ai baida wuya idan kana aon yi ga hanyoyi nan na samun arziki lokaci daya ga mutane bila,adadin ba sai kayi wani wahala ba can. Suka hada baki suka kwashe da dariya lokaci guda suna kawar da kansu gefe daya lokaci guda don sanin halinta da sukayi wurin yaba kanta da nuna ita tafi kowa aji. Daddy yana zaune a kasa saman kafet ya mike kafafuwan shi yana amsa waya lokacin ne anty amarya ta shigo falon ta zauna don ganin waya yakeyi a lokacin mai muhinmanci sosai. Ya dago kai fuska ba yabo ba fallasa a cikin fuskan nasa ya juyo inda take yana sake dan murmushin dole da baikai cikiba yace . To ya taron naku na yau dai an watse lafiya ko ta gyara zama tana lumshe idanu tare da fadin wallahi Alhamdullahi Alh jama,a sunyi kokari sosai wallahi. Wai kasan har da Sahiba tazo daga lagos kuwa saboda bukin nan ai bansan yarinyar nan tana kaunan mu haka ba sai yau wallahi bakaga irin alherin data kawo muna ba ni ai takara jamin girma a garin nan sosai wallahi. Tarin daya sarke mijin a lokacin shine ya hanata karasa maganan da take son fadi a lokacin shi kuma sosai yake son tarin ya tsaya mai lokacin ya tambaye ta wai wace Sahiba take magana a kaine ? Ruwa ta mika mai ya amsa da sauri ya kurba kafin yadan ji sallama itako ta tsugune a gefen shi ta kura mai idanu cikin mamaki. Sannu ta kara mai bayab taga ya samu saita numfashin sa a lokacin tana kokarin kawar da kayan abincin da yaci a gabashi. Ta kara fadin wai sannu Alh irin wanan sarkewan haka wata kila yajin ne yayi ma abincin yawa don naji su hjy suna korafin hakan yace umm,umm. Saida ya dauki yan mintina suna shiru a falon kafin ta mike tana fadin zan koma wurin baki dama nazone in fadama zancen sahiba din ne. Wai wace Sahiba dai kike maganane tun dazun haka ta koma ta zauna tana mamaki tare da fadin a, a Alh akwai wata Sahiba da muka sani da wanan sunan bayan Sahiban maman Ammar na lagos da suka zauna gidan nan shekarun baya. Ita nake nufi wallahi sai gata kwatsam a wurin taron Alh wai kaga Sahiba ko yanzu kuwa wallahi idan bata fadi ba kokai daka santa baka ganeta yanzu Allah ko. Ni ai yau naga abin mamaki sosai kuwa Alh duk yaushe Sahiba tabar nan ne amma gata da gani a cikin daula take rayuwa yanzu gaba daya komai nata ya canza wallahi saita fadama itace zaka tuno da fuskanta na baya can. Sallaman modibbo ne ya katse maau hiran ya shigo falon don ya gaida mahaifin nasa anty Amarya ke fadin a, a ashe ka dawo ke nan masu tafiya babu sallama kabar hankalin mutane a tashe. Ya danyi murmushi yana kaiwa tsugunne tare da fadin mun samemu lafiya ya taron jama, a Allah ya sanya alheri yasa wurin zamantane har abada suka amsa da Amin anty baki har kunne tana washe shi don dadi. Sam sam a gidan basu kula da abinda aka rubuta ba a cikin jug din da kofunan sai ga kira a lokaci daya ya fara shigowa a wayan daddy kiran baffa Abdullahi ne kanin daddy ya dauka . A zaton daddy zance zai mai akan daurin aure amma sai yaji Baffa din na fadin yaya kana gidane wai ? Eh gani nan zaune a falo ya bashi amsa yace kajirani gamu tafe da salau yanzun nan muna hanya ya amsa da to ya kalli modibbo yace dashi . Tsarin da kuka dauko dakai dame dakin ka baku dauki tsarin kwarai ba ace mutane kullun babu zaman lafiya an fada maku kowa ba hakkuri yake da iyalin shi ba yanzu ina amfanin biye matan da kayi ka kwashe yara ka tafi dasu ka kuma kashe wayan ka ba a samunka ka tayarwa mutane kawai da hankali haka ? Kanshi na kasa yana sauraren mahaifin nasa ne yaji sallaman kanin mahaifin nasa a kofan falo har lokacin Anty Amarya tana wurin a zaune. Kowa kallon kallo aka fara a tsakanin su ganin yadda suka shigo falon a lokacin kamar a firgice ina yar uwanki Baffa ya tambayi anty Amarya tana ciki ta bashi amsa yace kira min ita kizo da wanan abin bukin da kika ba matana dazun a gidan hari. Ta dago tana mamaki kafin tace wani ciki yace wanan anbin me kamar flask ma da akace watace tazo dashi kika basu akan sai gobe zaki raba saura. Oh nagane jug din da Sahiba ta kawo ke nan a raba gaban daddy ya bada ras ras haka na modibbo din yace ko bata nuna maka abinda muka gani a jug din rubuce bane ? Yanzu dai take fada min an kawo mata gudunmawa sai ga wanan ya shigo shiya hana ta karasa fada min to bari a kawo kaga abinda muka gani a ciki na firgici. Kai bamu wuri Daddy ya fada da cewa ya Abubakar ya fice ya basu falon sai baffa yace inafa zashi tunda wanan abin a yanzu ai ya shafi kowa a nan nake gani sai ga hjy karima ta shigo dauke da samfur din jug din dauke a hannun ta tana bude ledan tare da fadin. Koba wanan ba ai Sahiba ta kashi kudi a nan wallahi shiko ya Abubakar sai fadi yake a zuciyar shi me sahiba ta aikatane yanzu ? Mikawa mijin ki Baffa yace da hjy karima daidai mommy na shigowa falon ke nan suke wanan magana tana gaida su hannu kawai baffa ya daga mata yana nuna mata wurin zama . Kafin ya juya yanacewa daddy ka duba daidai kasan inda akai rubutu zakaga me aka rubuta a jikin kofin nan na hannun ka COURTESY, SAHIBA SAMBO NAMADI & AMMAR (YUSUF) SAMBO NAMADI, , , , , , , , , ,
Chapter 200 · 0% Book details