← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 337

Sashe 120

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akwana biyun da nake aiki a wanan wurin baifi sati biyu da fara aikin ba duk da ba fulltime nake zuwa ba sai yamma idan na dawo daga school in taso goma dare sai kuma gobe idan Allah ya kaimu zan fito. Amma hakan bai hana jikina canzawa ba don nayi wani itrn kyau na murje haskena na boye ya kara fitowa yanayina kanshi ga baki daya ya sauya a yanzu. Dole ina gilma mutane su bini da ido ga uniform din official din ya karbi jikina don bujena har kasa yake sai dan hijab da nake dorawa a sama.wanda iya fuskana zaka iya gani. Zan iya cewa a yanzu kam masha Allah zamana shagon nan don kudi baya katse muna gaskiya don akwai alwas da ake bamu don suturorin aikin mu kawai shine lissafi idan ko wani part na kaya sun shigo da kudin su. Anyi gulma anyi jininin hakan don ban isa wanan matakin ba tsakani da Allah sai manager yace wanan umurnin oga mai wurin ne dawa dani wanan part din. Don har kungiya akayi aka samu manager da zancen yayi masu bayanin irin umurnin daya samu daga samane dole sukai hakkuri suka saka ido don ba mai ikon zuwa wurin maishagon koshi manager da yake jin kanshi yana hura hanci idan yana gaban shi dole ya kwanta kasa don biyayya a gareshi. Bayerabe bai raina abin jifa dan uwan shi, kan dan abu kadan don hakan saida suka gwada sa,ansu gareni sai dai sun makaro don akwai tsarin Allah a tare dani badai mutum ba saidai Allah. Suit din aikin baki ke jikina na dufaro kamfani a cikin motana a karo na farko da Abdulhamid ya matsa min da hakan dole na koya na fara tuki har yakai ranan na fita school a cikin ta na dawo kuma na shirya zuwa wirin aiki duk a cikin motan. Umma kan tana jin dadin hakan ganin irin baiwan da Allah yayiwa yar ta irin wanda bamu taba zaton samun shi ba a rayuwa . Yau gashi Allah ya tarfawa garin mu nono Allah ya gwada mata yar ta a wanan matsayin da bata taba zato a garemu mu ba rayuwa ke nan inda ranka baka debe tsamani a wurin ubangiji. Na fito na kulle motar kamar yadda Abdulhamid yayi warning dina dayi akan in kula in dinga rufe kofa idan na fita daga ciki zan shiga wani wajen. Abinda nayi mafalki da darene na fara cin karo dashi duk yana cikin alamomin iskana zanga abu a mafalki washe gari kuma sai ingashi zahiri. Nasan akwai masu wanan baiwan da yawa a cikin al,umma duk alamane na farfarun mabiya ga mutum da wuya aiwa irin su asiri ya kama mutum irin masu wanan yanayin. Funke ne tsaye kamar dama ni take jira ina shiga sai gata da fara,anta ta nufoni tana washe min baki tare da fadin hello miss Sahiba. Na dan ce hi ina tafiya take fadin you about to let todaya sai kuma ta miko min hannu tana fadin good evening jere . Kallon hannun nata nayi na dan sake murmushi kafin na amsa mata da evening missFunke ina fadin hakan na girgiza kai na wuce zuwa sama inda office din mu yake yanzu. Da gudu ta kara biyo ni a dole sai tayi abinda tayi niyar yimin na taba jikina a lokacin saidai na fahinci hakan danaji muryan ta a bayana yasa ban dakata na haye zuwa office din da sauri na murda na shiga. Yeh tace tana bin kofan da kallo don yadda nayi mata din ban tsaya ba tana fadin i don dead wooo if i no touch dis gurl twoday. Ina shiga na gaida manyana dakr zaune office din kafin na hari wurin zamana ina addua a bakina lokacin nakai zaune takardun list din da aka tara min na shiga duba ina rubutawa . Kafin can naji rikici ya kaure a tsakanin manyan nawa na kudi akan lissafi har suna kokarin daga hammata a lokacin. Stop it na fada da karfi ina fadin ba haka aka bashi ba gaskiya yake fada an turo maida kudi kazane a ranan kaza da karfe goma na safe ya kuma tura a ranan banki har replay ya dawo gare ku a nan aka samu matsala kudin sun shiga cikin inda ba ayi niyar turawa bane mistakene. Tsaye sukayi kowa na kallona nace babban accounter din ya duba sakon wayan shi ai baka goge ba ko yana nan ciki ? Da sauri ya tura hannu cikin aljihun shi ya ciro waya ya shiga duba sakon daya shigo mai saiga bayanin a wayan shi ya dago kai da sauri ya kallo inda nake kafin ya sauke wani irin ajiyan zuciya ya dago kai ya kalli shugaban wurin ya mika mashi bayanan wayan shi. Lokaci daya suka dago kai suka kalloni inda nake tsaye nima na kura mashi ido ina sauraren abinda zai fada a lokacin. Fuskan su karara baiyane da mamaki a fuskokin su daidai lokacin na juya na koma na zauna tare da kifar da kaina saman taburina. Smart girl we have to be carefull with u in dis place Sahiba u are very talent girl . Ban dago kaina ba duk abinda yake fadi ina dai dan jin shi sama sama a lokacin na bude jakana na dauko maganin da Alfa ya ban in shaka idan naji alaman ciwon kai zai taso min cikin ikon Allah a hankali naji ya lafa min ba kaman yadda ya saba min ba. Sai office din yayi tsit bayan kowa ya natsu ya zauna manager ya shigo kan maganan a yadda ya samemu a office din kowa na aikin gaban shi yasa mamaki ya kamashi na ganin ba wanda ya damu haka ana fadin kudi sun shige. A kofa ya tsaya yana kare muna kallo a wurin kafin yace meke faruwa ya samu ba wani bincike da akeyi ? Ogan mune ya dago yana fada mashi cewa an gane komai anyi solving da taimakon Sahiba tayi muna lissafi har yadda kudin ya shiga. As how ya tambaya da mamaki akai mai bayani komai ya girgiza kai ya fita ba tare da yayi magana ba sai da muka dawo gida Abdulhamid ke fada min yana ganin fa zan bar aiki dasu abinda kawai ya fada min ke nan ba tare da bayanin komai ba. Nayi mamakin jin hakan amma kuma ban tambayeshi dalilin korana wurin su da za ayi ba kawai na fara tunanen abinda zanyi nan gaba a rayuwana. Jirgi Emerate ya sauke passenger daya dauko a Abuja daga cikin su harda Nazifa da yaran ta biyu daya yar shekara biyu sai karaman jaririyar yar wata biyu data haifa a lokacin. Yan gidan su ne da sukazo daga Kaduna don taronta suka tarbesu a gidan wani abokin baban su suka sauka saida suka huta washegari suka kama hanyar Kaduna. Bata sauka a gidan su ba gidan iyayyen ta ta sauka inda akai dafifi ana murna da zuwan ta don gabaki daya ta sauya ta kara zama wata babban mace yar gayu sai wani izza da isa takewa mutane. Yaran basa jin hausa basu ma yarda da mutane bata samu ganawa da mahaifin su ba sai washe gari da safe ta sakeshi a falon shi zaune. Yana saye da babban riga babu yar ciki a cikin rigan ya zauna ya baje saman kafet yana shan ferfesun kifi a gaban shi ta shigo da fara,an ta ga yaranta dauke a hannun ta. Fuska ya daure ganin yaran sai dai hakan bai hanashi ya tareta ba don an dade ba,a haduba a tsakanin su saida takai kasa take gashe shi ya amsa tare da tambayan ya hanya ta amsa da lafiya. Yake tambayan ta karatu tace ta hada a can bai tambayeta mijin ta ba kuma baiyi magana a kan haihuwan data samu a can kasan ba don bai iya tambayan ko daya don bakin hali irin nasa yana bakin ciki a zuciyar shi na hada iri da zuri,an daddy dayayi. Har zata daga take fafin baba gafa matan ka nan suna gaida kai ya kalli yaran a lalace yana fadin nagan su ai saidai kinsan bana maraba da zurian Aliyu gidana. Keda gwaggon ki kunja mun hada iri dasu don nacin uwarki badon ta nuna ra,ayinta kan son ki auri wanan dan iskan yaron ba ba abinda zaisa na hada zuria dasu a gida. Jikin Nazifa ne yai sanyi saboda maganan mahaifin nata ga yayan nata da take so kamar ta mutu a rayuwan ta hakama mahaifin su ya Abubakar yake kaunan yayan nasa sosai. Ganin yadda yanayin ta ya canza ya sake fadin nifa ban kaiki gidan nan aure don ki share kafa ki zauna har kina zuba masu yaya haka ba. Na fada maki tun farko cewa ina da manufa ga auren nakune shiyasa har na yarda da hakan idan bashi ba ba abinda zaisa in daukeki in mika wanan gidan da raina a duniya. Mijin ki da mahaifin shi sune ke son su ja dani a cikin dangi nayi alkawari kuma duk wanda yace zaija dani sai naga bayan shi a doron kasan nan. Shi Ali idan ba rigima ba har me yake takama dashi a duniyan nan me yake dashi meya tara da yake ganin wuyan shi ya isa yanka har zaice zaija dani akan dansa ya saba maki nayi magana shima yayi ? Wanan lokacin ta kasa rike kukan ta don Allah ya gani tana son mijin ta ita don ko huduban da yayi mata kancewa da wata manufa da yasa zata dan zauna a gidan nan ta dauka yanzu data hada zuria dasu komai zai wuya a zuciyan mahaifin nata ashe tunanen ta bai bata daidai ba. Yanzu ta fara shedawa gaskiyan mutane da suke fadin shi din maison kansa ne kuma mugune a cikin dangi dolene kowa ya bishi a yadda yake so. Yanzu kuma tasan ta kara sheda kowama ya shiga tarkon baban nasu sunan shi sorry ke nan do ko ita ya zama dole tayi taka tsantsan da yaran nan tunda har ya iya furta hakan a gaban ta yanzu. Muryan shine ya dawo da ita ga tunanen ta da yake fadin ina son ki sani komai dadewa sai na rabaki da gidan yaron
Chapter 120 · 0% Book details