← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 266 OF 337

Sashe 266

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

mata ya part din ta haka ta juya tana kallon kayan dake gaban ta a cikin babban leda guda hudu wanda sayayyan Faiza yafi yawa daga ciki. Sahiba yarinya ta kwaso halin mahaifin ta ke nan da halarci za a ce bata fahinci irin rikon da nake mata a zuciyana ba ? Wayan tane yai kara ta dan juya a kasalance tana duban wayan da wanda ke kiranta a lokaci guda sunan hjy harira ta gani da hjy Hari ta mika hannu ta dauki wayan tana karawa a kunnen ta. Gaisawa sukayi tare da jajanta zancen rashin dawowan daddy cikin su har tsawon mako biyun nan kafin hjy hari din a bangarenta tace wai kinsan me tace sai kin fada. Yarinyar nan Sahiba fa ina ganin ranan duk abinda muke fadi a kunnen tane saida ta gama sauraren mu tayi sallama ta shigo gidan ku. Meyasa kikace haka hjy hari ta fada tana gyara zaman ta tace bari kedai sako ta bani ta wurin Alh cewa ya tambayani abinda na fasa kanta da the boy ranan a gidan ku ? Ita sahiban ta fadi hakan da bakin ta hjy hari ta amsa da wallahi abinda ya fada min ke nan yau da safen nan don gaba daya yaron nan yaki daukan wayan mu sam tun ranan daya bar kasan nan. Shine shi Alh yace yasan abinda zaiyi nasan ya kira layin ita sahiban ne sukai magana kan shi boy din ta nuna masa hakan. Idan ko har haka wallahi abinda ake fadi kan yarinyar nan na shu,imanci gaskiyace hjy hari wai kode da gaskene ta mugun kungiyan mayu ne irin na kudu bamu sani ba ? Yarinya kamar aljana kowa yasata a gaba sai taga bayan shi hjy hari tace aina gani don ni abin ya ban tsoro sosai wallahi. Wai mema muka fada a ranan game da itane wai don ni har na mata da anyi wanan zancen shi nake son tunawa a yanzu ? Ba wani abu bane illa man ta kara tuna mata abinda kowa ya fada game da sahiba sai kuma suka koma kame kame a tsakanin su. Bayan na gama shiri na na juya zan filo wurin umma wayan ta sake daukan kara na juyo zuwa inda take na dauka Sir oga Shaaban ne a layin lokacin. Sai lokacin na tuna da yace zai kirani da kuma zancen motan dana bari da sauri nayi receiving din wayan karya katse. Muryan shi naji a dan sanyaye yana mun sallama na amsa tare da fara gaidashi ya amsa har lokacin muryan shi yana a yadda najita da farko. Bayan mun gaisa dan shiru ya gitta a lokacin kafin yace dani naso nazo da kaina saidai hakan bai samu ba don nazo family house din mune da yamman nan. Ya zancen maganan mu ya tsaya dake don ina son yin aure a cikin dan kwanakin nan kada koda yake wanan ba zancen yi a cikin waya bane zanzo har gida in sameki muyi shi don aure nake son yi dake Sahiba. Nervetheles motan ki na a waje yanzun nan a kofan gidan ku idan kin fito zaki gani zan saka subada key a hannun Abdul. Ok nace a cikin wani yanayin dana shiga saboda zancen daya gama yi yanzu daya zo min a bazata don sam ban taba tsanmanin irin wanan maganan ba a bakin shi. Wai dama da gaske sir Shaaban yakeyi ne da wasan da muka hadawa mommy shi a can kasan da mukaje komu ita din ta dauka kusan gaskiyane zance. To wai ko a kanshine yanzu yake son juye abin ya zama gaskiya a idon jama, a ko kuma wani abin ne ya sashi haka gareni. Don sam ban taba jin wani mahalunki da namiji a cikin raina da sunan so ba har wanan rana ta yaya zancen aure har mutum biyu zaizo min a rana daya kusan lokaci guda kuma. Fitan da banyi ba ke nan zuwa wirin umma na dinga jin bacin rai a zuciyana dole na samu wuri na kwanta na share zancen ga baki daya don ina son natsuwa.
Chapter 266 · 0% Book details