← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 337

Sashe 187

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasa wasa hakana kwashe har kwana hudu a zaune ba umm, ba umm,umm agida zaune saidai inta bin mutum da idanu saidai kallo daya zakai min ka fahinci ina cikin bakon yanayi. Hankalin umma ya tashi sosai da hakan dole ta daga waya ta kira ya Abubakar tana sheda mai halin da nake ciki a yan kwanakin. Yaji hankalin shi ya tashi don zaune suke falo lokacin shida Nazifa da yaran su saiga kiran umma ya shigo wayan shi ya dauka da sallama yana gaida umma din. Abinda yasa Nazifa dan juyowa ke nan ta kalleshi don jin mama daya ambata bata gane ko wace mama bace alokacin suke waya da ita. Yadda ya zabura yasata fadin lafiya wacece kuke wayan sai lokacin ya dan saita kanshi yana fadin gani zuwa mama yanzun nan insha Allah . Ido Nazifa ta kura masa har lokacin daya kare wayan nasa idon ta na a kanshi don bata fahinci dawa yake wayan ba. Mikewa yayi a daidai lokacin da yake kokarin saka talalman shi dake gefe yana daukan makulin motan shi daya aje saman table gaban shi don dama yana da niyar fita a lokacin. Wacece ta jefo mai tambaya tana kallon shi a tsorace don sanin cewa yan gidan su na asibiti har lokacin don haka takai zuciyar ta can ko wani abune ya samu yanuwan nata . Mamace ya fada kawai yana kokarin fita daga falon wace mama ke nan fa ta sake tambayan shi kai tsaye yace maman su yusuf da cewa Ammar kanina don yasan ba zata gane ba yana fadin haka ya fice daga gidan ya barta zaune tana maimaita sunan maman yusuf wace maman yusuf kuma ? Sai kuma taja tsoki ai tunda ba yan gidan su bane shike nan ko wace mamace su karata can yanzu kila wani case din shinecan har ya dan ruta da hakan taci gaba da kallonta kamar ba kanwata ciki daya ke kwance asibiti ba a cikin tashin hankali. Tuki yayi na tashi hankali yan mintuna kadan ya sadashi da gidan mu ya fito zuwa ciki misalin karfe biyar na yamma a lokacin. Yana shiga falon dani yai arba a zaune na hakince irin zaman da manyan mutane keyi a da can baya na sarkuna kafafuwana biyu suna lamkwashe a tsakina duk da sama kujera nake zaune. Ummace data fito kitchen rike da plate din dake shake da apple a cikon shi suka hade ta dan saki ajiyan zuciya tana fadin Abubakar har ka karaso ke nan ? Yace eh mama fuskan shi a kaina yake gaisawa da ita kafin yakai zaune yana fuskantana umma ma zama tayi bayan ta aje plate din a gefena tana fadin gata nan wallahi yau kwana hudu ke nan na rasa meke damunta haka ? A lokacin Abdul dayaga shigowan shi shima ya shigo don shi ya ba umma shawaran a fada mashi kada su barni a hakana don har yayi waya da oga Sha,aban yace su mayar dani lagos saidai ta yaya zasu daukeni a haka Abdul ya tambaye shi ? Don hakane shi Abdul din yaga garafa su fadawa yan uwana tunda ina dasu a garin koda shawaran da zasu bayar a kan matsalan nawa don sun fahinci akwai sabon sauyi sosai a cikin lamarin. Idon shi har lokacin yana a kaina koda yake amsa sallaman Abdul din ya shigo ya zauna shima idon shi dai har lokacin yana gareni. Umma taci gaba da fadin mun rasa gane meke damun ta sai bakon yanayin da take muna komai a hakince ko a kwantace zatayi muna magana baki yaki budewa har yanzu. Gaban shine ya fadi ras ras ya fara ambato innalillahi a fili tare da fadin dama nasan wanan aikin zai iya jawowa Sahiba matsala sosai don wallahi shu,uman mutane ne mutanen nan sam banu Allah ga al,amarin su ko kadan. Su dai burin su shine suga sun gina kansu sun halaka mutum ko da gaskiyan shi don nayi bincike na gane wa yanda sukazo aiki a kansu a yanzu. Abdul ne daba hausa yakeji sosai ba yake fadin yanzu meye abin yi ke nan yana tambayan su sai ya gyara zama yana fadin kuma gata da lafiyan ta balle muce aje asibiti ko ? Abdul yace munce zamu tafi tayi muna kashe din hakan tun shekaran jiya ya kara zakudawa yana fadin innalillahi baya ko kitbta idon shi a kaina. Yace gara kubar aikin nan nake gani don yana da hatsari sosai ga yinshi idan ta dan samu sauki sai a koma can lagos din zaifi. Sai a lokacin Allah ya bude min baki a cikin wani irin muryan daba nawa ba kamar na maza na fara fadin a kansu zamu dakata ai basu ida ba basu isa suyi min komai ba don suna tare dani. Shifa sarki ne gaba daya yake zaune haka a kaina sun taba ganin inda sarki yaja baya da yaki hutu kawai suke son nayi su tafi ba abinda zasu iya indai an yarda da Allah da kuma aljanni akwaishi to sune tare dani. Kuka umma ta sake lokacu guda mai ban tausayi tana fadin shike nan yar nan abin nan ya tabbata gaskiya a kanki ina daukan hakan kamar dai baiwane ashe da abubuwa saman kan ki. Baiwane mana shi shifa ba a kowani kazami yake saukaba sai a inda ya dace kuma ya kama yazo da kanshi ai da yaran shine saman kaina amma yaga ya dace shi yazo yanzu da kanshi. Zakace wani babban sarkine a zaune yake magana da isa da izza kafin na juya na dauki apple din har cizawan irin na sarakuna nayi shi na aje a gefena. Falon yayi shiru tsit kafin muryan Abubakar ya amayo yana fadin Abdul ya biyo shi akwai inda zasu tafi wanan ba abin su zura ido bane kawai sai lokacin da sukaga daman sake ni din. Nan suka fita suka barni da umma zaune wacce ta kura min ido na lokaci guda tana mamakin budan bakina a yau din don ko ba komai zuwan Abubakar din ya taimaka mata ai tunda yazu tasan magana na yana nan bai dauke ba. Gidan wani malami suka tafi can cikin kabala sai gasu tare dashi sunzo gidan da yar jakarshi bayan sun gaisa da ummane suka dan fita don yin sallah lokacin magariba ya kawo jiki. Sun dawone lokacin duk munyi don ina sallah na daidai saidai murya a bayyane irin ta maza nakeyi a lokacin saida suka jira na idar malamin ke fadin da sauki lamarin don gashi har tana ibadan ta saidai inaganin kamar namijine a kanta yanzu idan kun lura da yanayin sallahta a yanzu. Dama ya fada muna shi na mijine ai kuma sarki Abubakar ya fada don shi har lokacin mamaki yakeyi a zuciyar shi yadda yaji muryana ya canza a lokaci guda. Jakkar dake gefen shi ya dauko ya ciro kur,anin shi tare da wani turare ya dan yayyayafa a gefen shi ya fara bissilah da sauri na daga hannu ina fadin ba sai kajaba malam. Suratul sulaimana ko barin ja maka ya kalli littafin da nisan dake tsakanin mu ya girgiza kanshi kadan yana fadin kwarai. Amma duk da haka barin dan ja kaji abinda Allah ya fada ya fara jawo ayah uku falon yayi shiru ana sauraren shi ya dago kallon shi nakeyi a natse . Yace tunda kai musulmine muna son jin meya kawoka jikin boyar Allah nan kuke bata wahala haka yace wahala haram muke dai bata hutu a yanzu don ana son cuta matane. Muyi hakane don masu son cutawan su dauka ko sunyi nasara a kantane malam yace na,am amma ai koda baku shiga jikinta ba zaku iya taimaka mata din. Yace malam ba yau muke tare da ita ba tun ranan da aka haifeta muke tare da ita don haka idan zamu cuta matane da mun cuta mata tun lokacin. Mahaifiyar ta bata da ganewa data gane tun a lokacin irin kukan da takeyi tana karama wanda hakan alamane wani abu zai faru dasu ai. Ko ranan da aka kashe mahaifinta ya kasance watan azumine bamu aiwatar da komai a watan ibada saidai duk da hakan mun nuna mata alama saidai bata gane hakan ba. Lokacin magariba a lokacin da ko wani mugu yake samun sa,anshi ke nan ya aiwatar da nufin shi a kan wani ko ya aika da sheri akn abin nufin shi. Mun saka tayi ta kuka sosai har dare amma sam basu bar gidan basu kuma gane akwai kulli tafe a kansu ba sunyi nasaran hakane don irin sharadin bokan su ya basu a kan lalai su tun kareshi a wanan ranan . Sauran basuje da niyar a kashe shi ba saidai a turasasashi a kan dukiyan daya tsone masu ido wanda suke ganin bashi ya dace ya mallaki wanan dukiyan ba a cikin su. Malam yace umm,umm yana kada kai nan dai ya basu labarin komai tiryan tiryan sai lokacin da suka fara baiyana a kaina ya kare da fadin cewa yanzu duk wanda yace zai tunkareni a kwai aiki a gaban shi sosai. Har yanzu da Nuhu ya turo danshi yazo ya illanta rayuwan Sahiba din da suka mayarda aniyar hakan a kanshi shine mafarin baiyanan su a yanzu don Nuhu shu,umine sun zauna a jikinane koda yayi aikima ba zai gane koni wacece ba a yanzu. Dama nasan da hakan ya Abubakar ya fada don ni naji da kaina yana waya nayi kuma tunanen hakan tun lokacin kai kuma a kwai aiki Abubakar din a gabanka ya nunashi da yatsa ya nuna kanshi yana fadin shi shikan ai bai tare da wani aiki a yanzu mai yawa. Dan murmushi na sake yace abinda kake nema nasu yana karkashin kulawan mahaifin kane don da hannun shi akai komai. Wani irin zabura ya Abubakar din yayi lokaci guda yace kwarai kuwa amma idan na fada maka zaka yarda ka je office din su na tsohon ajiya bayan bakar kanta can kasa layi na uku daga barin hagun ka idon ka zai sauka a wani tsohon jan file zaka samu duk abinda kake nema kake wanan wahalan haka. Yace ya gode ba don ya yarda da hakan ba har kasan zuciyarshi ya dauki abin shirmene shi amma a fili ya
Chapter 187 · 0% Book details