← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 337

Sashe 129

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya nufa na zana exam dina na karshe a makaranta saura jiran jerabawa a garemu da fatan alheri yanzu kan sai kuma godiya a wurin ubangiji mai komai mai kowa daya nufeni da gamawa lafiya ba tare da samun wani tangarda ba a cikin karatun. Yanzu fadi barnan lokaci shiyasa ake son iyayye su dage sosai a wurin yiwa yayan su addu,a musanman ke uwa don addu,an ki karbabane a wurin ubangiji ga yayan ki. Tabbas ko rantsuwa nayi bana kaffara akai don adduan umma akan mune ko yaushe shine kuma ke bibiyan mu ba zama rokon abin duniya takewa rayuwan ta ba hakana. Sahibat kan ba sahiban da yan kaduna suka sani bace a baya yanzu wanan sahiban idon ta ya bude sosai ta zama first clasa ko a cikin lagos din a yanzu. Ba sahiba kawai ba har mahaifiyarta da dan uwan ta cigaban Sahiba suma ya jawo masi cigaba a yanzu. Shagon sana,an mu shi kanshi ya girma ya zama babban shago wurin sarin yan guwa don kudin da nake samu idan ogan mu yazo kasan na aikin yawo da mukeyi dashi ga shago da karatun mu sai abinci kuma idan mun saye da yawa abincin zai daukemu har wani lokaci mai tsawo din baci mukeyi ba. Yau ma ogan mu zai shigo kasan kamar yadda ya saba lekomu idan zai shigo din akan yo min aike a sabon wayana da yanzu ya canza min shi na ajewa umma nata ko ince na sai mata wanda yafi wanan sosai har Ammar. Don canza wayan ya samo asaline ranan da mukai wani fita zai gana da wasu abokan sana, an shi dole mota biyu akai amfani dashi zuwa wurin meetung din. Muna mota zamu tafi wurin ne aka kira layina naki daukan waya wani ya gani da kiran ya matsa na dauka yakai idon shi ga wayan . Ammarne ke nacin kirana wai nabar gida ban aje mashi kudin exam din shi da nace zan bashi ba a cikin hausa nayi magana kada wani yajime muke fadi a lokacin. Don in nayi turanci suna ji idan yarbanci nayi hakane zasu jini yasa na canza yarena da hausa ina fadin haba Ammar ka suba dakina karkashin filo suna nan na je maka kuma ka maida hankalinka wurin jerabawa kasan dai bamu da kowa Allah ne gatan mu a duniyan nan nima kaga karatu na dage nayi sosai Allah ya taimakeni ka daina wanan shegen game da kakeyi, karshe nace ka gaida umma kace mata mun fita ko, A gaban mota nakan shiga tare da wanda ke jan mota idan zamuyi irin wanan fita daya kama na gaba dayan mu idan zamu fita sai in koma gaba suna baya su biyu. Sam bai taba kullani ba ko ya nuna damuwan shi a kaina don da wuya inyi magana ma ya bani amsa direct yadda ya dace har na soma tsarguwan kaina da hakan. Abin mamaki sai naji ana fadi idan zakiwa yaro fada ba haka ya kamata ki nuna masa ba ai ki daina ce masa baku da kowa mahaifiyar ku da dan uwan ki suba kowa bane a gareki ? Saida na dan juyo nace dashi sorry sir a dan gimame daga hakan bai kara cewa komai ba tunane na lulayi na ashe duk lokacin dana canza harshe ina yaren hausa yana jina ke nan ban sani ba don bai taba nuna shi din ma yana da jinin hausawa a jikin shi don yafi shiga na kananan kaya ko ya saka irin jallabiyan nan mai tsada har wandon su na larabawa. Lagos ce fa duk yadda ka dauko karyan ka sai kaga abinda ya rinjaye ka ga gani a wurin wani yasa idanuwan su ko dan wanki da gugane su a bude idon su yake a can. Tunane na ya katse ne da yakecewa Felix ya tsaya wani shago sayar da waya ya fada mai ya fita ya zabo wayan mata iphone mai kyau ya sayo. Felix din ya fita ya shiga shagon ya dan dade muna zaune saukin abin bai kashe mota ba AC na bugun mu a lokacin don haka ba wani damu . Can sai gashi a lokacin har oga yaja tsukin dadewan shi yakai sau biyu sai gashi ya fito daga shagon rike da leda a hannun shi. Yana shiga motan zai mika mai sai cewa yayi No give it to her ina zata bini da wanan matacen gwagwanin nata wai waya abin kyama kawai. Mutuwan zaune nayi na kasa motsi kafin na mika hannu ina karba felix din yana min dariya don duk cikin su shine karami da Adnan sune kuma nawa yazo daya dasu. Da kyat bakina ya budo nayi mai godiya da addua irin na musulmin da akaiwa alherin da bai zata ba ga wanda yai mashi kyautan. Jin cewa zasu shigo aiki ranan tallata yasa na fito falo na samu umma a zaune nima zaman nayi ina saye da rigan barci mai sulbi sai zani dana daura daga sama sai hula baka iri mama cap din nan da akeyi a lagos yanzu a kaina. Baki barci ba ashe umma tace dani na danyi murmushi ina fadin banyi ba umma yanzun suka turo min da sako wai ranan tallata oga yana gari zamu fita. Tau aikin ya tashi ke nan wata uku yayi ke nan har zai shigo nace zai shigo umma ni aikin nan nasu ya fara fita min a rai yanzu umma. Da Allah zaisa na samu aikin gwaunati zan daina wanan din tunda ba na dindindin bane shi na kama na gwaunati din zaifi. Wanan din ma ai yana kokari sahiba ina laifin hakan da muke samu mutanen nan sun taimakawa rayuwan mu sosai a baya har ina zargin aikin da wani manufa kukeyin shi sai daga baya na gane aikine kawai dai na taimako Allah ya kawo muna a rayuwa. Hakane umma mun samu sosai a wanan fammanin shiyasa nake son kada in shagala dasu zan fara neman aiki na dindindin a yanzu gaskiya. Yanzu dai dole gobe in fita na samo dan rigunan da zan saka wanda zai fiddani nayi amfani dasu a wanan aikin ke nan don ban son tsarguwa ga hakan. Akwai kudi a hannun ki ke nan ko na dauko maki wanda ke hannuna ajiye umma ta tambayeni nace da ita a, a umma wanda ke wurina zai isheni ai don ba wasu masu tsada kwarai zan saya ba. Wani mai kudin idan kana tare dashi yana maka yafi son ka nuna yana maka din don haka ko kwara biyune dai ki sayo masu tsadan zaifi ummata fada. Washe gari na shirya da dan rana misalin shadaya da rabi na fita naso zuwa shagon mu nayi sayayya a can sai kuma na fasa na nufi wani sabon shago dake Agege na gown din mata wata bazabarma ce bude shagon daga ghana tana shigo da irin gown din nan na dubai dinkakku. Na shiga wurin suna haba haba dani aka ban wurin zama da drinks da ruwan gora yan matan dake tsaron kayan suka fara zuwa suna gaidani. Saiga wata mace gajera kamar ta taba ganina ta nufoni a cikin fara a tana fadin sannu da zuwa kanwata barka da shigowa gidan nan. Me za ai maki gyaran kai da kafa da yatsun hannu ko dress ga kikazo duba kawai na dan murmusa sai naji sha,awan gyaran kan ban san lokacin dana bude baki nace kai zan gyara da jikina sai dress din. Wasa wasa sai gani a shagon nasu har uku na rana suna min gyara an gama ta fara nuna min kaya tana fadin kinga ke mysulmace wanan zai fitar dake da addinin ki zaki haska sosai month dinga ne suka fito ba kowa yasan su ba a kasan nan. Kala hudu kawai na zaba a shagon na biyasu kudin su na fito har mota suka rakoni da kayana na shiga naja zuwa gida. Wasa wasa saida ya share wata kusan biyu bai dawo kaduna ba yana can aiki ya hanashi dawowa a kuma tsakanin an kwasa tsakanin iyayyen Nazifa da nasa don kowa ya hau a lokacin wanan ya kara bude sabon babin kiyayya a tsakanin su sosai a lokaci. A cikin wanan haklin ranan ya dawo gida duk daya gaji gidan su ya nufa kai tsaye an tareshi taro mai kyau duk da bai samu mahaifiyar shi a gida ba ta tafi barkan haihuwan kanwar hjy karima ita da hauwa da fa,iza sai Nabila ce kadai a part din don haka bayan ta bashi abincine ta kira mahaifiyar su a waya tana sheda masu zuwan yayan nasu. Hjy tace ya jiramu gamu hanya tafe yanzun nan kafin su dawone Nabila ta tsegunta mashi duk abinda ya faru tsakanin iyayyen su da iyayyen matan nasa . Amma kuma ta rokeshi kan kada ya nunawa mahaifiyar su cewa ta fada mai komai don zata yi mata fada saboda tace kada wanda ya fada mai wanan zancen idan ya dawo. Ko lokacin daya fada cewa zai dawo ba abinda zai fitar da mommy din a wanan lokacin koda suka dawo din ma ta fara zargin Nabila din tana tambayan ta yace ban san ida ta shiga ba tunda ta ban abinci ta shiga ciki. Zama tayi suka gaisa dashi da yan uwan shi kafin ta dauko mai zancen matar shi da cewa ka samu ganin ita Nazifa din kuwa. Hannu ya cire a goshin shi daya dafe yana jin zuciyan shi na masa kuna a lokacin yace da mahaifiyar su din daga airport nan nanufo direct. Basu san ka dawo ba ke nan yace yanzu ne fa saukana mommy ba sune a gabana ba dama a yanzu barsu can su zauba su huta nima a yanzu aiki yayi min yawa ai. Horon ya isa haka duk da nasan sai kakai kanka garesu sun fada ma abinda sukaga dama yadda suke so don sin dauka da zafi. Murmushi ya dan sake a fuskan shi ba tare da yayi mata magana ba ya mike yana fadin zan isa gida in watsa ruwa a jikina. Yaushe zaka tafi ka dawo dasu yace sai naje gidan ya fita ta bishi da kallon tausayi don tasan donta yake daurewa komai da ake mashi din. Haka ta zauna a
Chapter 129 · 0% Book details