Sashe 31
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan kwana biyun nan duk a shiririce nayi shi ba walwala ga kuma yunwa na batun kasarani don tsanda na kasa cin wani abin kwarai a cikina yanzu tun zuwan mu semi din komai ya tsaya mun cak. Ina ganin yan iska da yan duniya saidai wanda nake gani yanzu a semi boda ya cunawa wanda muka baro a baya can. Zaka ga yarinya da shigan kafirai amma idan ta juye harshe tana hausa sai kin rike kanki don mamaki. Hakama diyan su maza duk wani iya shege ya kare a wanan wurin ko yan Agege da Alaba rago da can ne dalilin hausawa kamar kana arewa da zama sun dagawa yan seme boda kafa wurin iya shige. Haka yasa fitama bai ban sha,awa yanzu haka zalika banyi gigin fara wani sana,a ba can da zan dan dogara muna dashi inda kudi zai shigo muna. Ga wanan hiran da naji umma da ladi sunyi ya kara min wani irin natsuwa a yanzu ga baki daya na koma wata shiru shiru dani a nan din. Yau kan na kudiri fita in zaga ko ina na garin inga gari gari ya ganni in sama muna abinyi don sai dan kudin dake hannun mu ne umma ke zara muna dan sayen abinci dashi dasu sabulun wanki dana wanka. Wani dogon rigana mai kama da kaki na saka sai takalmana da na ciro a cikin kaya ina goge kuran shi don in saka. Umma ta kalleni yau yarbancin take ji tace dani enbelolo ma,ana ina zanki tafi sai dana dan bata fuska nace i wan worker round to see d town b4 i start bussines . Don mind ur self here uno go enjoy dis place well, na bad people de stay round d place . Umma why we come here now why choose d place dan stay there at Ajagule me i no pit stay here woo na fada ina mike wa tsaye. U don no anytin dat worry us at dat place since i no peole don familier wit u naw at Ajagiule. Na mike tsaye ina fadin na yim u carry us come dis yeye place when person go die for notin haba pity us naw umma. Wani tsawa ta daka min har saida na gigice tana fada a haka har na sulale bata sani ba na fita daga gidan na fara tafiya. Kamar yadda kowa ke tafiya a wurin haka nima nake tafiya ba tare da kula kowa ba balle ma ban san suba balle na tsaya kula su har nakai titin su na zaga ko ina ina bin garin da nazari. Ba laifi don garin akwai shegen girma kamar sauran unguwanin lagos din da cinkoson abin hawa sosai ga yare kala kala a wurin har nazo iyakan layin na zaga wani layun shima na kewayo da zan dawo na tsaya wani shago na auni filawa da sauran kayan hadi har roban da zan saka kayan a ciki duk na saya na juyo zuwa gidan mu ban wani sha wahala ba wurin gane gidan don na saka shedan da zan gane hakan. Na samu umma a cikin damuwan rashin sanin inda na nufa sai gani kwatsam da yan kayan dana sayo na shigo gidan . Suna tsatsaye dasu Ladi cirko cirko sukaga shigowana ladi din tace ai na fada yar nan tana da wayayyen kai ba zata bata a garin nan ba. Kinbi kin tayar da hankalin ki ga hakan, nikan gaidasu nayi ina kokarin shiga dakin mu da kayan naji ladi na fadin meta sayo ne take kokarin shiga daki dashi ? Kamar ban jita ba na shige abina dakin ina fadi may ur evil eyes back to u, uno de see dis tin today. Daddy ka bari zan ga yarinyar na bincke ta wasu abu kafin ka ganta wai duk yanayiwa mahaifin nasa hakane don ya kwantar da hankalin shi. Saidai mahaifin yaki don cewa yayi idan ba zaka kaini ba zan kira Haroon ya kaini tunda tare dashi kuka je gidan yasan wurin. Shike nan daddy sai mu tafi taren ya fada idan kaji sauki sai mu je lagos din a tare in hakan zai fi ma sauki zaifi Alh ya fada. Haka ya fita daga dakin cike da zargin mahaifin nasa don gaba daya abin ya kulle mai kai a yanzu ya kasa gane meye hadin shi da wayan nan mutanen da yake nemane wai har yake zatin yarinyar nan nada alaka dasu yanzu. Dakin mahaifiyar su ya nufa ya samu ta fito wanka tana gyara jukin ta ya shigo kallo daya tayi mai ta fahinci damuwa a tare dashi take fadin. Zaka sakawa zuciyar ka damuwa akan wa yan nan mutanen ni yanzu na bar sakawa kaina damuwa kan lamarin wayewar karima na shashanci. Mommy anty kuma ina ruwana da lamarun ta a yanzu tunda ba zamana takeyi a gidan nan ba shi daddy da yaji ya gani shi suke ba kunya ai. Ido uwar ta bishi dashi tana nazarin sa kafin tace ai dole muma mu damu da haukanta tunda ta sakamu gaba a gidan har ku. Don tsaban samun wuri karima zatace wai idan wani abu ya samu Alh kaine silar hakan don dakai kukai waya ya shiga wanan halin don haka kaine silar. Kai innalillahi haka ta fada yana kallon mahaifiyar nasu da wani irin kallo na mamaki kafin yace. Zato zunubi don koni bansan dalilin da yasa daddy din shiga wanan halin ba daya shiga yanzu. Har kuma da damuwa da har takaishi kwanciya asibiti kan wanan zancen da mukayi dashi kawai a waya din ban san hadin shi da wanan mutanen ba. Wasu mutane ke nan kake magana a kai wai hjy ta tambaya a cikin mamaki tana kallon dan nata da shima ita yake kallo. Wallahi hjy ban san ko suwaye ba su na dai san a lagos suke zaune daga kawai naba daddy din musalin su yace wai yana son ganin su. Matane ko maza hjy ta tambaye shi ya dago kai ya kalleta kafin yace da ita a sanyayye wata yarinyace da mahaifiyan ta da sukai bala,in kama da yan gidan malam na tudun wada. Wai malam mahaifin mu ko wa yace malam dai namadi naku hjy ya kara fada wani kallo tayi mai ta mike tsaye tana saka hijab din ta tare da fadin kana da photo sune a wurin ka. Ban dauki photonta ba tunda nidai nasan ba wani hadin da ake dasu kamane kawai na yanayi sukayi da yan gidan. Ikon Allah ashe har yanzu zancen iyalin Badaru na cikin zuciyar Alh don nasan su yake hasashen ko sune aka gani a can din. Wani ne hakana kanin mu mana daya bata har yau ba a samu labarun shi ba ita kuma matar da yarta an nemesu ko kasa ko sama ba asan inda ta shiga ba ga ciki koda ta bar gida har ya fara tsufa a jikinta don cikin zaikai wata hudu da dan kai a lokacin. Shiru yayi yana tunane kafin yace anya wa yan nan sune kuwa do naga uwar yarinyar kama wata yarece fa. Ina fa za,a gansu tunda tunda yanzu kusan shekara goma sha wani abu ke nan da batan su ya dauki zancen tsawon shekaru yasa a zuciyat shi. Shima dai Abubakar din yasa zancen a ransa yana faman tunane kala kala meyasa sai daddy ne zai damu haka bayan ga yan uwan su nan suna harkokin gaban su basu damu ba. Washe gari tun cikin dare na tashi na kwaba filawan yadda nake so don na iya kwabin washegari da safe ina idar da sallah na shiga soyan da wani murhun tsoho dana tsinto na gyara a bayan dakin mu. Take kamshi ya karade ko ina na gidan mutum zai gane ana suyan wani abin filawa a lokacin. Sai ga yan gidan dake fitowa suna wucewa wurin sana,oin su suna tambaya na sayarwane nake cewa eh. Sai gashi tun ban fita ba na sayar ga baki daya a wanan gidan har ma bai isa ba don ban samu aje muna ba don mu karya dashi. Daga wana ranan sai na samu sana,an yi idan nayi na safe ya kare saina kwaba na ran da zan fita dashi waje in sayar. Sai ya kasance ina suyan umma nabawa mutane masu saya ni kuma nakan mayar da hankalina akan suya . Sai gashi har wasu wure an gane shigo a saya, muka kwasa muka koma wajen gidan ga badaya don abinka da dan Adam. Sai gashi an fara nuna muna hasada ga sana,an tamu har mun samu wa yanda suka fara irin sa a unguwar duk da dama sunayi saidai ba a lokacin da muke namu ba din. Yau ina son zuwa cikin garine don da shirin haka na kwana a raina ba kuma komai zai kaini ba can don saro kaya da sauki don yanzu kan mun wuce sayan mudu mudu da muke saye a da. Sun shirya tafiyan kamaan yadda suka tsara bayan sati biyu a lokacin har Abubakar din yayi tafiya zuwa onicha ya dawo lokacin daddy ya murmure ga baki daya. Duk yadda hjy karima taso jin dalilin tafiyan su a tare ta kasa gane komai sai ta dauki hakan da wani abu zai kaisu can din tare. Tafiyan safe sukayi suka shigo cikin gari haroon ya dauko su daga airport din zuwa wani hotel inda zasu huta suci abinci. Bayan sun gama ne suka shiga mota sai tsohon gidan mu da muka tashi haroon dinne ya fada masu mu suka zo nema da cewa wanan shine mahaifina. Mamaki sukayi suke fada masu ai mun tashi daga unguwan yan makwanin da suka wuce mun koma wani wuri na daban suma bamu fada masu inda muka koma ba. Ran Alh ya baci sosai da jin hakan sai ya dauki laifin ya dora gaba daya kan Abubakar da yaki yarda ya kawo shi tun lokacin da yaso zuwa din. Basu gane komai ba legas kuma ba karamin gari bane da zasu saka cigiyan mu har a samemu a cikin sauki don haka suka bada lamban wayan haroon da yafi kusa idan an ganmu a kirashi akwai kyauta da zasu bayar. Haka Alh ya dawo gida ranshi a bace duk da bai tabatar da cewa mu din