← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 337

Sashe 166

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yana fadin ki rike wanan a wurin ki ki fadawa anty saina shigo mu zauna da ita. Duk abinda suke fada Nazifa na jin su don tayu masu zaune a wurin taki dagawa tana son taji meya lawota wurin dan uwan nata. Mata a kula a dan dagawa maigida kafa a duk lokacin da yake ganawa da yan uwanshi na jini ko aminan shi irin wanan zaman da kikeyi yana ja maki bakin jini a wurin al,umma haka kuma yana hana maigida yayi alheri wa masu bukata idan yana kallo idanun ki don wata kila kin rokeshi bai samu baki ba har wani ya kawo nasa bukatan a lokacin daya dace ya bayar. Yar uwa kada ki zamo cilin silar hana alheri ki kasance mai karfafa kafan a yi zumunta don ki tashi da hasken hakan a goshin ki ranan gobe kiyama ubangiji Allah yasa mu dace amin. Nazifa bata so hakan ba duk data dan dauki haske amma kuma rashin ganewa ya hanata fahintan komai a lokacin. Itama hjy karima tana gida tana Allah Allah yar nata ta dawo taji yadda sukayi da yayan nata a lokacin. Bayan baby Summay ta gama labarta wa uwar sai cewa hjy karima din tayi burgan banza dama ai nasan ba zai iya bamu abin kwarai ba don wanan munafukan uwar nasu bata bari yayi alheri ko kadan dama ta kara jan tsuki tana fadin aikin banza da wofi idan ma sirina suke son ji basu taba gane hakan wallahi. Zato zunubi koda ya zama gaskiya da yamma sai gashi gidan direct part din ta ya nufa kuma Amira taga shigowan shi itake fadin ga yayan mu nan yazo. Fatima na fadin tare da yaran sa ne yazo Amira tace ban tsaya ba ina shigowa na ganshi basu gama magana ba sai jin sallaman shi a kofan su sukaji. Ya zauna an gaisa yake fadin anty baby ta sameni dazun a gida ta kawo min list din yanzu ga wanan sai ayi hakkuri dashi. Nan hjy karima ta fara fadin kai modibbo wanan kanwar taka ta azama lalura haka har ka biye mata kai kuma. Dan shafan fuskan shi yayi yana fadin hakan ai shine daidai anty ku godewa Allah daya nuna maku hakan kuna tare damu addu,an kune ke aiki a kanmu . Wani iri taji tana kai idon ta kan takardan daya basu din saida ta dago kai da sauri tana fadin anya modibbo kudin nan basuyi yawa ba haka ya mike yana fadin bakomai anty kayan gado dai da sauran su nayi magana da Fatima ventures zasu shigo da kayan da komai na sakawa a daki a haka mata su sai a duba dakuna nawane a gidan yanzu don sun tambayeni hakan . Shiru hjy karima tayi gaba daya jikinta ya gama mutuwa da bayanin ta sai ji tayi yana fadin na barku lafiya anty ya mike ya fita yana kadawa baby din data dago tana kallon shi hannu ya fice. Yana fita yaran sukayo kan uwar suna fadin mama nawa yabadane mu gani summaya din ta fisge takardan a hannun ta. Ihu ta sake tana fadin mama miliyon biyu fa ya bada tace bari kedai baby aini na kasa magana wallahi don na rasa mezan ce ga baban kunan muna kai ruwa rana dashi kan dan abinda na bukata. Ashe yaron nan yana da kudi hakane Allah sarki mama har kina zagin sa dazin gashi ya baku abinda bakiyi tsamanin samun a wurin sa ba fatima ta fada daga gefen su inda take kwance saman kujera. Harara uwar ta watsa mata tana fadin kaji yar baki na zageshi din duk cikin hakkin mune wanan din yaji dadin mahaifin ku cikin ku kamar shi ? A wani matsayi kuke yanzu a nan din tambayan dana jefo masu ke nan bayan na zauna na dan bi office din da aka ajesu din da kallo. Adnan ne ya dago kai yana fadin a cikin dariya ai shine muma har yau bamu gane ba madam don munyi tambaya bamu gane komai a nan din ba. Ba gaskiya bane na fada ina mikewa a nuna min office din manage din yanzu na fada ina barin kujera. Sahiba kibi wanan zancen a sannu don mutanen nan basu da kyau wallahi na fahinci hakan tun jiya da muka fara tambayan su Abdulhamid ya fada. Ai ban tsaya sauraren shi ba nasa kai na fito daga office din ina bin rubutun office din da kallo. Idona ya kai gana manager din ban tsaya jiran komai ba na nufi kofan zan shiga da sauri dan tsohon dake zaune a kofan ya taso yana fadin . Hjy ina zaki ba a ban ikon barin kowa ya shiga a wanan lokacin ba don manya ke ciki suna meeting na dan kalloshi na sake mai murmushi komey ya gani oho naga ya jaye min da sauri na shiga ya biyoni a baya. Jin an bude kofan an shigo yasa gaba dayan su su wurin goma suka juyo suna kallon wanda ya shigo office din. Binsu nayi da kallo daya bayan daya har nakai kan manager din na tsaya a hankali na tako baka jin komai a lokacin sai karan takalmana dake fitar da sauti. Good morning manager ya dan amsa min da sauri sauri files din dake gaban shi na kalla ina fadin zamu fara aiki akan wa yan nan now now. Da niyar wullakanci ya dago ya fada min magana ko me ya gani kuma sai ya kasa baba kazo ka taimaka min mu kwasa zuwa office din da aka bamu muyi aiki a cikin sa. Ina kallon tsohon nake magana shima dai ni yake kallo kamar kowa sai kuma na koma fadin zamuyi aikin da wasu daga cikin ku zasu taimaka muna . Af kuyi hakkuri fa ban gabatar maku da kaina ba nazo na fara aiki kai tsaye kada ku damu don haka nake ni ban wasa kan abinda ya kawoni a wuri. Kwana biyun nan ban fito ba saboda dan gajiya daya dameni sunana miss Sahiba daga lagos na fada tare da rokon su su yi hakkuri da shigowan da nayi masu kai tsaye. Zamu iya daukan files din kun gama dasu na juya ina tambayan shi tare da kallon shi na tsure shi da ido OK zan baku minti talatin a kawo muna muna jira na juya na fara tafiya suka bini da kallo. Har nakai kofa na juyo ina fadin saidai kada ka manta ka fito da wayan nan da kuka boye kai dashi na nuna mai dayan mutumin. Daga haka nasa kai na fita shiru office din ya kara daukan kafin manaja ya cire hullar kanshi yana fifita dashi a kanshi da fuskan shi. Yau naga shu,umar ya lalai mutanen nan basu zo muna da wasa ba a wurin nan saida suka shiryo muna amma barsu in sun san wata ai basu san wata ba. Kafin su rike baki na turo kofan kai dakai dakai a tare zamuyi aikin daku sai ku samemu da files din muna jiran ku yanzu. Wacece ita din wai wani dan kyamusasshe a cikin sune ya tambaya a cikin hausa azaton ba maijin ko zo in kashe ka acikin mu kaf, wa,iyazu billahi wanan mutumin ta nan ya biyo muna kuma yanzu ban taba kawo hakan ba wallahi ? Suyi duk abinda zasuyi mana kudi daine sun shige bamu san inda suka shiga shike nan mana fakat . Dayan su ya fada yana wani ware hannayen shi na dan sake murmushi daga inda nake tsaye din yaci gaba da fadin zai dauko muna kafirai suzo fitgita mu kome ? Alhassan kabi maganan nan sannu don Allah kai ka cika danye kai kada abin nan ya dawo ya juye damu fa kana magana haka. Ta kwabe din mana wake tsorin hakan yanzu duk iya binciken su dai ba zasu taba gano kudin nan ba tunda ba a hannun mutum daya suke ba yakarsa fadi a hasale na dan saci kallon shi da wutsiyat ido. Kai manager din ya fada har lokacin yana fitara da hular kanshi yana fadin su Alh dai yanzu ai dole mu nemosu su sanda zancen nan gaskiya. Office din na koma ban zauna ba sai bin ko ina na office din nayi da kallo suma abokan aikin nawa kallona sukeyi ba wanda yai min magana a cikin su. Widow officen kawai nake kallon haraban wajen a tsaye kafin muji an turo kofan office din an shigo wa yan nan mutanen dana nuna ne su ukku dauke da takardun company a hannsu su. Kallona abokan aikina suka fara yi kafin su shigo suna gaisawa dasu na nuna masu table din akan su zauna saidai kuma wurin ba zai ishe mu ba dole mu koma babban hall din taron cikin wurin da aikin mu na fada yes madam Adnan ya kara fada suma suka bini da kallon mamaki.
Chapter 166 · 0% Book details