← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 221 OF 337

Sashe 221

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Kwana hudu a Dubai banga giccin Oga Sir Shaaban ga idona ba tun zuwan mu kasan saidai dadin kan muna samu shi har nake tunanen wai dagaske ko hutun da yace din mukazo yi ke nan ashe ?
Kai gaskiya idan kana dashi dai ka huta a rayuwan ka don bakajin kyashi ko zafin yiwa wani na kasa dakai idan Allah ya horema zuciyar alheri don irin wanan halin dace ne.
A rana ta biyar ne a garin don munsha hutu har mun fara jin zaman dakin ya fara isar mu don bama komai daga kallo sai charting ko karatu.
Sai hakan yai min dadi nikan don wanan wasan kwaikwayon da Oga keyi dani gun mahaifiyar su shi da nasan yana matukar biyayya gun mahaifiyar shi.
Don duk abinda zai mata wanda zai bata mata zuciya nasan baya so a dan zaman da nayi dasu a gidan su lokacin bukin tunawa da mutuwar mahaifin su.
Amma yanzu na rasa ko meye dalilin shi nayi mata hakan ga wanan hadin da Alaja din keson yi a tsakanin shi da yar aminiyar ta yanzu.
Yanzu kuma da Alaja bata tare damu bai kara nemana da nuna irin kulawan da yakan nuna min agabata din yanzu ko ina cikin dakin da aka sauke mu din ina tsabgan gabana.
A haka muka samu sako kan cewa mu shirya zamu shiga cikin gari muga yanayin gari da tsarin sa.
A zuciyana nace wani garin zan gani a yanzu makka kawai ya rage naje gani tunda naga england da ban taba zaton zuwan shi ba a wanan lokacin yanzu saurana makkan kuma.
Sai dai ina fatan umma ta fara zuwa kafin ni shine nake kokarin tara kudi a yanzu in kaita ga dan abinda muke samu daga aikina da kuma shagon mu insha Allahu shine burina kawai a yanzu gaskiya.
Don ni babu zancen soyayya ko wani mu,amula da wani da zai dauke min hankali balle ma ban taba bada fuskan da wani namiji zaizo ya nuna min soyayya ba sai wanan karon da muka nuna hakan da Ogana hakan kuma sai yake min bambarakwai don rashin sabo da hakan.
Haka muka shirya don fitan a daidai lokacin da suka aje muna time din fitan kafin lokacin kowan mu ya shirya don fitan da zamuyi din.
Sai a wanan lokacin ne kuma na sanya Oga a idanuna tun ranan da mukazo da ban kara ji ko ganin shi ba ko inji wani abu gareshi ba.
Yana tsaye a haraban wurin da wasu yan kabilan chana suna magana muka fito zuwa wurin motocin da zamuyi amfani dasu bisa jagorancin felix da ya fito damu zuwa wurin.
Gaidashi muka fara yi a cikin ladabi bayan ya iso inda muke ya fara umartan Felix da ya kula damu tare kuma yi muna bayanin cewa zamu dan shiga garin mu zaga muga gari muga yadda al,amura kasan ke tafiya a nan din.
Duk wanan bayanin da yakeyi kaina na kasa ina kallon wayana da nake charting da ya Abubakar a lokacin don haka ban yarda mun hada ido dashi ba.
Yayin da duk second shi sai ya dago ido ya kallo inda nake tsaye ina saurarenshi a lokacin da yake bayanin nasa har dai ya kaiga kiran sunana yana tambayan ina ko tare dasu ?
Sai lokacin na dan dago kai ina fadin yes Sir a gajarce har muka dauki hanya zuwa wuraren daya fada zamu kai ziyara din shi felix ya saba zuwa don kusan shida oga din akwai dan dangantaka saboda mahaifin felix din shine babban yaron mahaifin Ogan mu a lokacin da yake raye .
Yanzu ko mahaifin Felix din ya tsufa sosai shima ya koma kasan su na igbo a kauyen su da zama .
Wanan yasa yanzu shi kuma yajowo Felix din suna harkokin su a tare don yaci gaba da tallafawa rayuwan ahalin nasu Felix din.
Don haka kusan shi felix din yasan komai akan ogan namu saidai baya zama can Labeno a tare dasu yana zama a gida Nigeria ne sai in bukatan tafiya waje ya taso yaje.
Shine dalilin zaman Felix din na hannun daman shi sosai kamar yadda shima oga Jimoh suka hada halaka tun na kurciya idan sunzo Nigeria duk da Jimoh ya girmeshi amma suna tare koda yaushe dashi kasancewan su makwabtane a lokacin suna yara.
Shine abokin shi nakusa a nan Nigeria bai kuma manta dasu ba har wanan lokacin da suke komai a yanzu yana zaune tare dashi a karkashin shi.
Saida muka dawone daga fitan da mukayi nasan Alaja da Ganiyat sun iso Dubai din don ganin su tare da mukayi a haraban hotel din muka hade dasu sun fito shan iska.
Nan dai aka shiga gaisawa dasu ana masu bangajiyan taro da muka barsu sunayi a can tare da bakin ta data gayyato a bangaren ta.
Kamar yadda ta hade rai muna hada ido nima hakan na hade nawa a lokacin sai Ganiyat din ne ke fadin Oni wan kweb wa !
Tani ? yemisi ta fada tana kallon ta don son jin wanda yake magana dashi din a cikin mu don kanshi yana duke baka dauka ma yayi wani magana a lokacin.
Tace boda me wan kwebwa Sayiba na dago na dan saci satan kallon shi a inda yake tsaye a cikin fararen kaya irin na yan, kasan Pakistan
kayan su mashi matukar kyau sosai a jikin shi.
Yemisi ta dan zungureni tana fadin ke ake kira nace no ke dai amma ai yasan ba zanzo ba wanan wurin ga uwar Alaja a tsaye yadda ta saka min ido haka.
Ganin ko gezau banyi ba daga inda muke din yasa shi ya dan tako zuwa inda muke din tsaye zaikai tako biyu zuwa uku tsakanin mu dasu tun bayan gaisawan mu da Alajan .
Sai dai ina mamakin rashin ganin mutanen ta da sukazo mata ma,ana abokan tafiyan mu wata kila sun komane daga england su, sun juya zuwa Nigeria.
Kara gaida shi mukayi daya karaso wurin da muke din ya amsa a cikin sakin fuska yana fadin.
A kwai meeting da zamuyi a nan gobe karfe goma na safe ki tabbatar da kun shirya ke da Ad,nan da Jimoh nake bukatan muje tare don akwai abubuwa masu muhinmanci da zaku sani.
Allah ya kaimu goben lafiya na fada a cikin girmamawa daga hakan ya dan yi magana da yemisi kafin ya juya ya bar wurin.
Ajiyan zuciya na sauke tare da bin bayan shi da kallo na juyo ina kallon yemisi da niyar fadin mu shiga ciki sai na samu itama shi din take bi da kallo.
Tafiya na farayi ganin haka ta biyo bayana da sauri muka shige ciki a nan muka bar sauran suna magana da Alaja da su jimoh.
Kowa a falon yayi shiru yana sauraren abinda da daddy din ke fadi bayan ya gama sauraren shima inda ya soma da fadin yana kallon fuskunan su a daure yace.
Da ace kusan kowaye wanan yarinyar da kuke zancen ta haka a kanta da ko wanen ku a nan ya kama kanshi a yanzu ko kuma dai ya dawo mata da duk abinsu daya karba a baya.
Ko kuma mutum ya tozarta a idon jama,a kamar dai yadda ta soma maku a yanzu kan dukiyan wani hakan kuma zatayi a kan nata koma fiye da hakan.
Au kai zaga zugota ke nan tazo taci muna mutunci ashe idan ba haka ba har ina zata ji abinda ya faru a baya waye zai bata shedan wani abin da sai mu kadai muka san yadda ya faru ko kai daka shigo daga baya baka san yadda abubuwa suka kaaance ba a lokacin don gudun irin hakan muka rufe maka gaskiyan zancen.
Murmushi yayi wanan karon ya mike yana fadi ni zan barku saidai shawarana shine kowa ya hado masu dukiyan su baki alaikum mu basu.
Ba za a bayar ba Alh Nuhu ya fada a fusace yau kaci arzikin abu daya a wurin nan da ba haka ba da fita wurin nan gareka yau sai Allah .
Nasa zaka iya saidai ku sani mutum baya mutuwa idan kwanan shi bai kare ba koshi wanda muke zance akan iyalin shi yanzu kwanan sa ne suka kare a lokaci.
Don haka ni dai yau ashirye nake a duk lokacin da suka bukaci komai nasu in basu don dama ba karba nayi don naci ni kaina ba.
Ni na barku lafiya ya fada yana juyawa karya kake wallahi kayi kadan kace zaka juya muna baya a yanzu wanan ba mai yuyuwa bane a wurin ka yanzu don ya zama dole kamar yadda muka rufe komai a baya mukayi shi tare yanzun ma hakan zaka nuna baka san komai ba a wanan zancen.
Murmushi yayi ya gyada kai kafin ya juya yana tafiya tare da godewa Allah da yabi shawaran da zuciyar shi ta bashi kan yaje da security din shi.
Da Allah kadai yasan yadda zasu kwashe dashi a wurin nan tunda ba imanine dasu ba don su sam basu tunanen sun girma yanzu su koma ga Allah.
Ido ya lumshe yana tunanen wautan daya tanka a baya duk dama dai yasan yayi hakan ne da wani manufa wanda suma basu san da hakan ba.
Gidan sa ya nufa kai tsaye sai dai suna shiga get din gidan nasane ya hango hjy karima ta fito daga cikin gidan da sauri tana kokarin shiga motar ta sai gashi.
Kallon ta yakeyi a cikin mamaki inda zata fita haka hankali tashe bata fada mai ba itama din ganin shi ya dawo yasa ta dakata daga kokarin shiga motarta da takeyi.
Ta dagakata har motar nasa ya tsaya ta karaso wurin da yake fitowa daga cikin motan ta sameshi ya daure fuska lokaci guda tare da tambayan ta ina zaki haka yanzu kuma ?
Alh ba lafiya fa baby ce ta bugo min waya yanzu a cikin tashin hankali wai yaron nan yayi mata tsinanen duka ko tashi bata iyayi.
Kallon ta yayi cikin mamaki sai kuma ya fara takawa don ya bar wurin ja yayi ya tsaya yana kallonta yace sai ke kuma zaki tafi yin me gidan nasu yanzu ?
Ah zuwa zanyi muyita dashi wallahi tunda tace yanan gida yanzu zanje in sameshi in nuna mai karyan iskanci yakeyi shi.
Ki sameshi fa kikace ke da kanki karima keda kanki zaki fada gidan suruki haka idan kinje kice masa me to
?
Kallon mamaki itama tayiwa mijin nata tace in fada mai duk anin da yayi min dadi a cikin wani irin haushinta da takaici yace ke da dan karfi ta juyo yace koma gida.
Yanzun ne baida hankali ko mashayi ai kaqai ku koma ko kin manta da kikace kunyi bincike kun gano duk sheri akai mai kawai.
Chapter 221 · 0% Book details