Sashe 335
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon fuskana tayi itama da kyau wanda da alama mamakin karfin hali irin nawa take mamaki wai har itace karamar yarinya ke fadawa irin wanan gatsen a gidan mukhutar yau gidan mijinta da take da iko da ko ina na gidan. Hannu takai da niyar figar key din daga hannuna amma sai taji kamar wani abu ya soketa a kafadanta haka kuma hannunta ya rike a wuri daya taji bata iya mikashi. Acikin mamaki ta dago kai ta kalleni kamar zatayi magana sai kuma ta kara kai hannu da niyar ta karba da sauri naga taja baya ta juya da sauri ta tafi tana dan sauri a lokacin. Binta kowa yayi da kallon a cikin mamakin abinda ya hanata karban key din daga hannuna a yadda tayi niyar fisganshi da karfin dole. A lokacin muryan mama kanwar hjyn su mukhatar ke fadin duk iya shegen mace da shu,umancinta ai tazo karshe yanzu. Duk yadda akayi akwai abinda tagano kukaga ta juya da sauri haka mama din ke fadi cikin takaici da bacin rai ga irin halaiyan falmata din. Idan kaga Allah yayi halittanshi ga bawa to kabarshi kawai da abinsa ko kabi shi da addua don Allah kadai yasan dalilin yin bawanshi a hakan daka ganshi. Naga biyu ke nan a rayuwana wana matsalan jinnun na sahiba ga inda zaiyi ranan nasa a yanzu haka a baya kuma ya taimaka mata wurin kareta daga sherin yan uwan mu. Yau, da,ace badon mutanen dake saman kan yarinyar nan ba masu karfine haka da yanzuma an share tarihin ahalin yaya sambo ga baki daya a duniyan nan gaskiya. Saboda ko irin sherin dasu yaya Nuhu suka shuka a doron kasa ko littafi baya daukan shi kai tsaye haka don a lokacin har muna ganin ta tarowa kanta mutuwa sai gashi yau sune suka kare a tsare a gidan wakafi suna daure don kawai son abin duniya da suka kwallafawa rayuwan su. Ga na biyunshi yanzun ma na gani a gabana don wanan matar tana ganin kawar da sahiba ba aiki bane a wurinta yasa tazo har nan da niyar tozarci da kazafi a gareta. Sai gashi farat daya ta fara raina kanta da abinda ta taka lokaci guda don tsafinta baiyi tasiri akan sahiba ba kenan a yanzu yadda alama ya nuna hakan nidai na fahinta . Don kila dama da shirinta tazo garin nan don kawai tayi tashin hankali da fitina ta batawa mutane zukatansu don irin su haka suke da jan fitina ga abokan zaman su dama dan kada a zauna lafiya. Allah sarki aida tasan kanta kawai su zauna lafiya shine alheri yanzu a gareta don ba kowane sihiri yake kamawa ba don wasu baya tasiri a jikinsu amma tsafi ko wani shirka da takeyi can sam ba zai taba tasiri a wurin yar mu ba gwaggo ta fada. Abinda hjyn mukhutar ke nan ta fada itama har ta dage saida akai auren nan nasu gashi yanzu kuwa abin yazama alheri a yanzu tunda har ga rabo an fara samu na diya. Falmata ta shuka tsiyataku iri iri a gidan mukhutar tana ganin ba wanda ya isa yaja da ita tako ina saiga Allah ya kawo yar nan a cikin rayuwan su a yanzu. Har yakai hjy da kanta data haifeshi bata isa ta tashi taje gidan danta da sunan ziyaran kwanaki ba haka kuma bata isa a kawo mata diyanshi gidanta ba kai abubuwa dai da dama na nuna isa da gadara boyar Allah nan ta fuskaceshi a wurin falmata . Yanzu kinji sherin da tazo dashi bawai murnan arzikin samun yaran nan bane ya kawota, tazone da wani sheri da zata kafa don tayar da hankalin mutane kada a zauna kalau, shine tazo wai yaran rikonsu aka dauko a gidan marayu ba haihuwan yaran sukayi ba. Wanan kan da hankalinta kuwa gwaggo Amina ta sake tambaya don mamaki daya cikata lokaci guda a wurin tana kallon al,ajabi a filin Allah. Tsab take shedanane irin nata tana ganin uban kowa tana iya yiwa wullakanci balle wanan da take kallo a makiyiyar ta a yanzu fiye da kowa. Umma dai suna daki da yara ita da Fatima duk wanan abinda akeyi a katon falon gidan su basu sani ba don haka duk yadda hjy falmata taso taga yaran a lokacin abin bai yuyu ba gareta. Da yake gidan babban gidane bamu san wainar da suke soyawa ba a inda suke sai gashi mun gansu sun fito sun tafi ko magana basuyiwa kowa ba a lokacin. Lalai kin haifu Sahiba a cikin iyayyen ki yau Falmatace tayi saurin saduda haka har ta iya barin gidan nan kamar yadda kika fadi ba zata kwana a nan ba ba tare da wani hayaniya ba haka. Zaune yake a office din shi suna aiki wayan shi yayi kara ya dauka yayi mamakin ganin kiran yar babba yasa a lokacin da sauri yakai hannu ya dauki wayan. Yana ambatan sunan ta yake cewa ya suke ? lafiya daddy ta fada kafin ta soma fadin na dawo na samu mommy mu wai ta tafi Hong a yau din nan da safe ita da Anty Nafy. Hong ya ambata hankali a tashe yana fadin ina office yanzu zanje gidan na duba idan sun shigo OK daddy ta fada tana kashe wayan yasan yarinyar bata da hayaniya kamar ba falmatace uwar data haifeta ba. Yadda ya shigo gidan zaka gane hankalin shi a tashe yake lokacin haka ya karaso yana kallon fuskana ko zai gane wani abu ga yanayina. Bai fahinci komai ba don kamar kullun yadda na saba taron shi na taryeshi da sannu da zuwa ina gaidashi da aiki kafin na gabatar mai da abinci duk da nasan baya cin na rana a gida. Baiki ba yace yagode bai zauna ba su gwaggo ya duba suka gaisa yayi masu ya gida kafin ya juya zai koma falo yaji muryan kanwar mahaifiyar shi tana fadin. Falmata tazo yau din nan da wani sabon zance da mukaji a bakinta wai yaran nan ba diyan ku bane daukosu kukayi gidan marayu don ku tayar dasu . Daga inda yake tsaye yake ambato sunan Allah har yakai ga dafa bango yana fadin wanan wani irin zancen banzane haka mama ko dai falmata ta haukacene wai ? Shina gani don kishin ya koma mata kamar hauka yanzu kuma mama sunana falmata take son batawa kome don wanan ba fatima tayiwa sheri ba ni kaina tayiwa sheri ai a idon mutane don ta sheganta min yaya ko me mama ? Ina tsaye bakin dinning din ya fito da yanayinshi da gabadaya ya kara sauyawa a lokacin fiye da yadda ya shigo da farko gidan. Zama yayi ya kurawa waje daya idanu na dan lokaci kafin yace ya kukayi da Falmata data zo ? Kallon shi na danyi kafin nace nothing naci gaba da abinda nakeyi da wayana nothing bayan yanzu mama ke fada min abinda tazo tayi a gidan nan ina son jin komai daga bakin ki yanzune. Ban boye mashi komai ba har abinda na fada na kwashe tas na fada mai yana saurarena har na gama fadi ya jawo wayanshi da sauri na dan rike hannun shi ina girgiza kai. Kallona yayi nace kada ka kirata don Allah ka barta wanan fadan tunda bata sakaka a cikiba fadane namu na mata so ka barni da ita kawai. Falmata bata da kirki don hakane nake son nayi mata iyaka akan diyana duk Iskancinta zan iya hakuri na daure da komai da take min a kaina amma wanan sam ba zan lamunci hakan ba. Ina son diyana fiye da komai dana mallaka a rayuwana don haka zan iya sabawa kowaye yake son sheganta min jinina zufana da nayi wahala a wurin samun su. Kaina yana duke duk yake wanan maganan ina nazarin abinda yake fadi watau dai ko ya kuke dashi zai iya sabama idan ka taba mashi diyanshi. Jin yayi shiru yasa na dan dago kai na kalleshi yana zaune ya hada hannayen shi biyu saman kanshi ya dafe sai naji tausayin shi ya kamani lokaci guda haushin matar nasa zanji kome a yanzu ? Don na fahinci ashe ba karamin zance bane ta fada sai a lokacin nake nazarin zancen na gane me hakan yake nufi mikewa nayi daga inda nake zaune a hankali. Na taka zuwa inda yake zaune din cikin yanayin damuwa hannuna nakai a hankali saman kanshi ina fadin uncle kayi hakkuri mu bita da addua a yanzu. Da sauri ya dago kanshi ya dubeni idanuwanshi nagani sun kade a lokaci guda sunyi jawur dasu alaman bacin rai karara a idanun nasa. Da kyar ya bude bakin shi yace Falmata ba iri mata nan bane masu saukin kai hakana tana da matukar wuyan sha,ani sosai sam bata da fahinta abinda tasa a gaba shi take gani daidai a gareta. Ina mata ragowa da farko don mahaifiyatace amma daga baya saina fahinci su basu san hakan ba don a yanzu suna ganin kamar sunfi karfinane bata san ina raga mata bane a yanzu don hjy din da kuma yayan mu a yanzu. Bana son yarana su shiga cikin damuwa idan na sabawa mahaifiyarsu dolene abin ya damesu amma sam ita bata duban hakan tana ganin kamar duk abinda tskeyi fin karfina tayi yanzu din. Ta manta da cewa nine sillar mayar da rayuwanta haka cikin inganci ta manta cewa a innuwana take shan iskan rayuwan da take taka kowa dashi yanzu. Idan kayi hakkuri ka lalabata zata daina wanan tanayin shine yanzun a cikin zafin karin auren da kayi mata don haka ka lalaba ta ku fahincin juna ku zauna lafiya. Shiru yayi yana saurarena kafin ya nisa yana fadin fatima you are wonderful and best among the best mm agode da baki kasance irin matan nan masu hali irin nasu falmata da ace wanan halin kike dashi yau nasan sunana zai baci a idon jamma,a. Babu macen da za a zo har gida a batawa diyanta suna haka kuma har ta shanye hakan ba tare da ta dauki wani mataki ba haka . Idan ma na dauki matakin ba zaikai wanda Allah zai daukar min ba idan na kyaleta da halin ta idan kuma tana da rabon shiryuwa Allah ya shiryamu baki dayan mu amin muka