Sashe 23
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hankalin shi ya tashi matuka na rashin ganin wayan nasa daya fado gurin mayarwa a aljihu bayan sun gama waya an fada mashi wanda suka zo nema baya gidan ya bar kasan ga baki daya. Yabi ta ghana ya fita har yabar kasan ghana din a lokacin shine dalilin da suka bar yan gidan mu din suka koma bincike ga landlord din gidan ta yaya ya bashi gida haya a ina kuma suka hadu dashi har ya bashi hayan ?. Ko dana dawo kowa na dakin sa wasu kuma sun gudu sun bar gidan a lokacin fita na sake yi na je nemo muna abinda zamuci duk da mun dawo da abincin da hjy ta bamu kafin mu bar asibitin. Sai dai shi Amar yace tea zai sha shi yasa nafita wurin nema kayan hada shayin a hanya ne wayan ya fara vibration a cikin aljihuna sai dan kara har hakan yasani firgita. Don sam na manta da zancen wani waya dana tsunta ga baki daya sai lokacin har kiran ya katse ban san yadda zan dauka ba ashe tun wurin diban ruwa ake ta kiran layin ban sani ba ina can ina daga bohol. Ashe hjyn su modibbo ne take kiran layin dan nata tunda ya bar gida basu samu wayan shi ba sai wanan lokacin shine hankalin su a tashe ta samu aka dauka kuma ya katse Aka sake kiran layin nayi sa,a na danna daidai na dauka naji muryan mace tana fadin haba modibbo ka daga muna hankali haka ? Nayi shiru ina sauraren hausan matar da muryab ta ta sake fadin wai bada kai nake magana bane ga daddy kuma yana ta kokarin neman ka tun dazun. Ba mai wayan bane na fada tare da fadi me ego hausa kosi hausa fa hausa kadan kadan mama don jin danayi tace daddyn ku. Who are you aka fada wanan karon muryan namiji ne nace iam d one who found d phone i don't know d owner self. Kinji me take fada aka fada a cikin wayan ina ganin wayan ta fadi maine watace ta tsunta nace eh na samune a cikin gidan mu dazun. Ke wacece ni ni sunana sahiba na fada kai tsaye a cikin hausawa gwari gwari mai kama dana yare wani unguwa na fadi sunan unguwa . Na karashe da fadin a fada mai yazo ya karbi wayan shi idan kun same shi nakarashe da nagode. Allah yayi maki albarka nace amin woo nagode kada ki kashe aka fada a kausashe nace oyah oda Yan tambayoyi ya dinga min ina bashi amsa a cikin irin hikiman su na tsufin ma,aikata har ya gane komai da yake son ji a wurina ban sani ba . Muna gama wayan dasu na kali wayan ina jin dadin jayi waya mai tsayi a cikin yaren hausa duk da bansan da wanda nayi wayan ba a lokacin. Shi kuma daddy su neman layin wani abokin aikin dan nasa yayi ya fada mai ya nemi moddibon ya fada mai yadda mukayi. Kodana shigo gida nake fadin ni bazan sha tea ba wanan abincin zanci wanda ya saura muna na rana. Har na fara ci na tuno nake ba umma labarin wayan dana tsunta din har iyayyen maishi suka kirani. Da farko kirji ta buga amma tana jin har nayi kwantancen inda za a sameni a karbi wayan sai ta dan sake take min fada dana tsunta me yasa ban bata ba a lokacin ? Nayi shiru kafin ince umma naga kowa a wurin ne lokacin kin san kuma gidan nan da tsunce. Modibbo yana kwance daki abin duniya ya dameshi na rashin ganin wayan shi gashi kuma bukatan abinda suke ganin zasu kawo karshen shi ba samu ba a garesu. Yaji anyi nocking din kofan dakin shi da alaman akwai wani a kofan lokacin dake son shigowa wurin shi . Ya mike daga shi sai dogon wando da fari singlet a jikin shi haroon ya gani tsaye a kofan mamaki ya kamashi. Sun gaisa ya bashi wuri ya shiga dakin suka kara gaisawa da shi yace oga yace na zo na fadama anga wayan ka a hannun wata yarinya Sahiba. Sunan ya maimaita a cikin mamaki Sahiba a ina ta samu wayan ya kwashe yadda mukayi da mahaifin shi ya fada mai. Nan ya nufi wurin dan jakkar kayan shi da sauri ya dauko riga ya zuru ya dauki bindigan shi ya soka a bayan shi suka fita a waje yake fadawa security din da su biyo shi anga wayan shi a wanan gidan hannun wata yarinya. Suka biyo shi da sauri baya suka shi shiga motocin su zuwa gidan mu basu samu isowa ba sai sha daya da wani abu duk yan gidan sun dawo a lokacin sai yan kalilan ne basu dawo ba. Mukan har mun kwanta sai jin jiniyan mukayi a kofan gidan naji umma na fadin kai innalillahi wanan masifa yau da me yai kama hakane ? Kamar mahaukata suka shigo duk abinda suka gani a gaban su suyi ball dashi ina yarinyar da ake kira Sahiba suka fada. Ga kowa ya fito hankali a tashe matan daga su sai daura gaba wasu kuma sai dan guntun wando a jikin su . Umma na kokarin budan kofan aka bamko kofan da karfi tace subbanallahi wetin we do again ? Sahiba are you ? Sukace wa umma ta girgiza kai kafin tace na my daughter be Sahiba sukace ina nake ? Sai gani na fito daga dakin ina mutsukan idanu aka tambaya a bayan su kun ganta eh ya bada amsa tare da fadin karamace fa ogo. Ku kawo ta nan ya fara tunkudani na juyo ina fadin na wetin i do ? i no be criminal woo stop pushing me like dat. Ai kafin yace me gulma ya fara tashi a gidan kowa da abinda yake fadi har gaban ogan nasu aka kaini naja na tsaya gaban shi kim kam. Where is my phone ya tambayeni nace saka hannu a cikin aljihun riga na dauko na mika mai ai sai gida ya dauka olusi omo buruku. Na dis smal rat stil d officer phone ? smol girl like u shame on u omo kowa dai yan gidan namu da abinda ke fitowa bakin shi lokacin . Wani tsawa ya daka duk aka natsu yace yarinyar nan ta tsunci wayana ba sata tayi ba don ta kira parents din na ta fada masu da inda zamu same ta. Kuma mahaifina yace nayi mata alheri don wanan halin nata na kirki data nuna ba wanda zai tsunci wayan nan ya maida min shi kamar yadda ta mayar min a yanzu ba tare dana sha wahala ba. Don haka ga wanan ki rika ya fada yana miko min kudin da sai lokacin ya kalleni ya gane yarinyar nan ne ranan ashe ? Yasan ban shedashi ba don irin yadda yayo shiga ranan ba zan taba sheda shine ba a yanzu gabana tsaye . Ya juyo ya kara kallona yana miko min kudi na gurgiza kai tare da fadin i no de colete ur money i just do wam becouse of Allah. Tsuki yan gidan suka fara suna fadin olopopo see d person wen no get any tin de reject d money now . Eh i no go coletem my religion no teach me like dis wani officer ne daga bayan shi ya amshi kudin a hannun shi yana fadin where ur mama. Na nuna mashi kofan dakin mu yace ur mama go colect d money naw yana dan washe baki. Shiko yana tsaye ya soka hannu daya cikin aljihu ya kura min ido a cikin mamaki hali irin nawa. Suko yan gidan namu sai fadin suke ehh givan to her mother she will colectam, suna wani bubuda mashi hanya don ya wuce. Su kuma na fadin haba dis enosent girl can do dat may she found it some where mafi yawan su haka suke fadi suna kallon yadda za a kwashe tsakanin mu dasu. Har guntun dan sandan yayi nisa a cikin muryan shi na kasaita yace dashi look Samuel called d mother for me first. Duk mama na tsaye a kofan mu a cikin tashin hankali tana jin abinda kowa ke fada lokacin kafin ma ya karaso itace ta fito suka juyo tare. Sunzo wurin ta dan tsaya a inda nake tsaye itama tana kallon yawan su duk wai a kaina suka zo can yace da ita. Yarki ta tsunci wayana ta kuma kira azo a karba shine nake son bata alheri don halin data nuna na kwarai taki karba. Ai domin Allah yata tayi hakan ka tambaya nan kaji idan mun taba rigima da wani tsakanin mu da kowa a gidan nan sai mutunci. Daga gefe suka shiga fadin gaskiya ne kwarai kuwa hakane don baka sanin ma suna gidan nan idan ba sun fito ba agansu. Oya ki karbi kudin nan don hakan umurnine na tabbatar da na baku alheri don yaba abinda kukai min don kinga wayan nan duk wani baiyanin sirina yana cikin sa kuma tunda ta dauka bata taba shi ba. Woman colet d money u be luck woman to born pikin like u knowadays with good heart wani tsohon iyamiri dake sayar da kayan part na mashin din hawa ya fada daga gefe inda suke tsatsaye. Woman colect de money now iyamirin ya kara fada sai umma takai hannu ta karbi kudin don iya shegen bariki sai suka ihu da tafe wai har sun manta wa yanda ke zagaye dasu a lokacin . Nan dai gulma ya kare bayan sunga sunyi godiyan hakan da akai musu suka shiga motocin su suka tafi. Tafiya sukeyi amma hankalin shi baya tare dashi duk da yana bin wayan shi da bincike a lokacib don ya tabbatar ba a taba mai ita ba bayan batar ta. Saidai hakan bai hanashi shiga zurfin tunanen da yakeyi ba tare da tantama ko a ina yasan wanan fuskan a baya. Haka nan a bangaren mu sai bayan wucewan shi ne umma takai kudin a hancin ta tayi saurin cirewa da sauri don irin kamshin da taji kudin nayi. Nima a daidai lokacin kwakwalwata ta hasko min kamar shi da wancan guy din daya taba ban kudi a cikin mota