← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 337

Sashe 152

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya is gidan suna zaune a falo suna kallo bai tsaya komai ba sai inda hauwa take zaune ya daga hannu yakai mata naushi ta gwauce bai sameta sosai ba ya kara kaiwa zai buga . Da sauri Nabila tace a, a yaya ka tsaya mana kaji ba,asi zaka kama dukan ta haka bayan matar kace ta zagi mommy don me ba za a zageta ba itama ? Da wani irin mamaki ya juyo yana kallon Nabila din tare da fadin ta zagi mommy fa kikace nabila tace kwarai yaya shine ita kuma hauwa ta tura mata da sakon zagi din. What ita Nazifa din ta zagi umma how comes har ta iya zagin mommy akan me zata zagi mommy din ? Kan abincin mana wai mommy idan ita ke auren ka taci da baka abinci idan basu saka kafan wando daya da ita ba. Ita Nazifan ta fadi haka ya tambaya a cikin mamaki yana lallon kanwar tashi Nabila tace wallahi yaya itace ta kirata ta fadi hakan a gaban mu. Yayi wani irin juyawa zai bar falo lokacin har mommy dake ciki cikin damuwa abinda surukar nata tayi mata yana cin zuciyarta tafito don jin hayaniyar su da tayi a falon. Wai meke faruwa ta tambaya daga inda take tsaye tana fito zuwa falon hauwace ta turawa nazifa zagi shine yaya yaji yazo yanzu. Na fada maku kada inji an tayar da wanan zancen ya fita baku jiba watau har saida kukayi yadda kuke so ko ? Au da gaskiya ke na ma ta bugowaya din ya sake tambaya cikin mamaki nabila tace ta bugo mana kai baka yarda bane dama yaya. Kai yasa zai fita daga falon mommy ta dakatar dashi da fadin kada kaje kace mata komai kyaleta iskancin kurciya ke cinta ai itama mace ce zata haifa. Baice da ita komai ba yasa kai kawai ya fita daga gidan ranshi bace ya shiga motarshi ya tayar ya bar gidan. A lokacin ne kuma hjy karima da suke jin hayaniya suka fito ta daiga fitan shi a cikin fushi amma bata samu jin kome ke faruwa ba a lokacin take tambaya meke faruwa ne wai ? Nabila tace a, a hauwace yaya yakewa fada ba komai bane me hauwan tayi mai ta sake tambaya ba wanda ya bata amsa tace to kuma ku daina rashin ji mana kullun aitama fada baka barin abu hardai ta juya ta tafi ta koma part din ta. Koda ya shigo ya samu har tayi barci irin matan nan ne dake barci suyi dadaya da cinyoyin su waje su sake tsirecin su don dadin barci. Duka yakai mata a cinya yana sake tsuki gata yanzu tayi wani irin kiba don dadin data kara samu a yanzu din hankalinta kwace a gidan mijinta. Ke tashi yace da ita a cikin takaici yana kura mata ido ta dan muskusa ta juya tana fadin au ashe barci ya kwasheni ? Yace ke me kika kira mommy kika fada mata dazun yana mai mata wani irin kallon tsana idanunshi a cikin bacin rai sosai yake kallonta din. Kaje an fada ma munafunci da makirci da gulma a kaina yanzu kazo zaka tsureni ko ta fada tana kokarin komawa ta kwanta. Ya wani irin fincikota daga filon data sa kanta dintace kada ka balla min habana don Allah a banza ta fada a fusace tana kokarin kwace jikinta daga rikon da yai mata din. Nace me kika fada wa mommy a waya tace au an fada mane don kazo ka hauni da fada bayan zagin da kanwarka tayi min kuma ? To ni zan iya dako wani munafuki wallahi tunda ba zaman lafiya ake so ganin munayi ba dama ai don haka anzugaka kazo kaci min mutunci don na fadawa mahaifiyarku gaskiya ko ? Tass ya dauketa da wani irin wawan mari saida ta koma kwance yadda ya sameta ya nunata da yatsa yana fadin wallahi ahir din ki da uwata wallahi. Duk iskancin da rashin mutuncinki da zakiyi ki tsaya a kaina nidake auren ki kada ki kuskura ki saka mahaifiyata a ciki don ban raina maki taki ba kema. Kodon kinga ina kyaleku bana kula wallakancin da uncle yake jifanta dashi don kina mara hankali bari kema ki fara jifanta dashi ko ? Mara hankali da tunane kawai ke idan kina da tunane kin taba ganin ina sa,insa da uncle ne duk abinda yake nuna min a fili. Sai kece don kin raina min tawa uwar baki dauketa a matsayin da Allah ya bata ba a gareki na kanwar mahaifinki don baki da tarbiya zaki nunawa duniya kalan tarbiyan da aka baku na rashin girmama babba ? Jin fadan da yake yine yasa yaran nasu falkawa a tsorace suna saka kukan firgita suna kokarin kankame jikin uwar nasu. Nazifa dake dafe da kuncinta tace ni kamara Abubakar kan uwarka da yan uwan ka yace an mareki ke wacece zan gwada maka ko na isa wallahi don sai an rama min marin nan dakai min sai ka raina kanka. Yace wallahi karya kike baki isa ba wallahi kuma banga wanda ya isa ba bayan Allah bata dadaraba ta kara fadin zaka gani wallahi kuwa. Ya daka mata tsawa yace saina tattakaki yanzun nan wallahi mara mutunci ya juya yana jinta taci gaba da yimai suratai tana fadin zaka gani zaka san ka mareni. Uwarta ta kira a cikin daren nan tana dauka ta fara fada mata abinda ya faru tun farko sai data gama fadi uwar tace rufamin baki sakarai kawai an fada maki duk son da yake maki sai ya bari ki zagi uwarshi ko yan shi a gaban shi ? Allah ya aikeki ki fadawa Alh wanan zancen sai kin raina kanki a duniyan nan wallahi don dama neman hanyar da auren ki zai balle ake bida shiko Alh ba ruwan shi rabaku zaiyi kada ki koyi kisa da kisisina irin na kowa zauna kina masa gadara da isa a gida idan shi zai fitar dake ta kashe wayan tana jin haushin wauta irin na yarta. Washe gari yana ganin kiran mommy yaki daukan wayan don yasan zancen ne zatayi masa shiko yanzu ko wanda yasan Nazifa baison jin sunan a gaban shi. Shirin shi ya gama tsab ya dauko dan jakar shi da yake tafiya dashi ya fito a falo ya hangota zaune a saman kujera duk idon ta ya kumbura don kuka. Ya iso inda take bata ko dago kai ta kalleshi ba ya dan tsaya tare da kiran sunan yarshi mai sunan mahaifiyarshi mairo . Saidai ita Nazifan ta juye tace wai sunan kanwarta ce dake bimata mairo ya saka don haka take kiranta da mairo din ba sakayawa don shi. Zanyi tafiya kinji saina dawo ya fadawa yarinyar tare da saka hannun shi cikin aljihun shi ya ciro kudi ya mika mata daga haka ya daga ya fita baiko jiyu inda suke ba yabar gidan ta bishi da kallo. Tun dana dawo nake barci na kashe wayana don kada a sameni kiran ya tayar dani daga barcin gajiyan dana samu din. Barci nayi sosai don ban falka ba sai yamma sosai gap da magariba na tashi gurguje ranan nayi sallolin dake kaina sai kuma yuwan da nake jin na fito umma basu ciki suna shago. Kitchen din muna nufa don samun abinda zanci duk da yunwan da nake ji bai haba in gane cewa akwai sabon abu a cikin kitchen din ba da nabi da kallo ina mamaki akwai miya saidai ba a kaiga dafa abinci ba lokacin. Saina yanke shawaran yi muna sakwara bayan na dafa indomie na aje na dora doyan dana fere na wankeshi na zuba a cikin tukunya. Na fara cin indomie din sai naji baimun ba na aje fara aikin sakwaran da zan daka din miyan na saka bayan doya ya dahu nayi hadin miyan egushi. Kafin a kira sallah na hada komai yadda nake son shi na gyara kitchen din naji ana kiran sallah magariba yayi har falo na gyaro na shige nayi wanka tare alwala . Ban fito ba duk da kafin in idar din naji muryan umma sun shigo cikin gida ma,ana ta rufe shago sun shigo gida. Saida nayi isha,i na fito ina gaida umma take fadin ashe na tashi har nayi girki tana fadin bari su shigo su girka abinci tunda ina barci. Murmushi nayi na zauna ina gaida ita tare da tambayan ta kasuwa take fadin sai hamdala kasuwan ya dan tsaya saboda zuwan dama yanzu ba ciniki sosai. Kasa na zauna na kalli Ammar dake ekujo anty mi na amsa mashi da yaya kake yace lafiya nace ga abincin ka nan na daka maka. Da sauri ya dago yana dariya tare da fadin da gaske sakwara nayi yana kokarin bude kulan abincin yagani. Sai ya kwashe da dariya ya nufi kitchen ya fito da plate biyu a hannun yazo ya zauna a gabana tare da jawo abincin ya bude yana kallona na dan kalloshi ina fadin ehhee mana ma,ana ya zuba muna muci. Har umma shiya zuba mata ina nan zaune hankalina ya dauku a wayata ina karanta sokon da aka tura min. Yace min bissillahi na dan motso muka fara cin abincin falin yayi shiru don yana cikin dabi,an mu hakan idan muna cin abincin. Dazun yayan ku yazo gidan nan saidai bai shigo ba a shago ya samemu muka gaisa ya kawo muna kayan abinci nayi shiru ina ci gaba dacin abincina ban dago kaina ba. Bakiji bane ta fada umma an fada mashi bamu da abincine daya kawo muna wani irin maganane wanan. Shiru na sake yi banyi magana ba yaran nan sune ke kulamu a cikin duka yan uwan mu da muke dasu ina laifin su yanzu don yazo ya kawo muna abinci. Sun san abaya mabukata muke ba zasuyi zaton a yanzu muna da dan dama ba duk da alama ma ya nuna a jikin mu cewa bamu tare da wahala. Amma ko muna dashi ai ba a hana alheri sanan yaushe rabo dayazo gidan nan wurin mu tun lokacin da kikai mai wullakancin nan bai sake zuwa ba sai yau din nan yazo ya kuma zo muna da alherin sa. Wani yayan namune ciki yazo umma ta kyaleni bata ban amsa
Chapter 152 · 0% Book details