← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 337

Sashe 160

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ba take fadin kona shiga na girka yanzu ne yace barshi kawai ban tare da yunwa yanzu ya fada yana mika hannu ya karbi yar dake bayanta goye yana dan mata wasa. Daga inda take tsaye tana kallon su gwanin ban sha,awa bata san lokacin data lumshe idanun ta ba a hankali don sai yau data natsu ta samu kulawan shi take ganin ba macen data fita jin dadin miji ashe duniyan nan. Shiko dan duniyan duk da sun ya kasance da mace dake damun shi bai yarda ya nuna mata damuwan haka a bangaren shi ba ya daiyi kokarin sassauta natsuwan shi da kuma maida hankali wurin nuna kauna ga yaran shi har yaga iya gudunta. Kai ya dago ya kalleta itama dai din kallon su takeyi saita bashi tausayi a yadda tayi din hannu ya mika mata yana fadin zauna mana kin tsaya kina kallon mu kuma. Dole in kalleku kun maidani ta ware kana zance kaida diyan ka kawai kun barni to ayi hakkuri ya fada sai ta kai zaune. Bai samu leka gidan su ba sai washe gari da yamma ya kwashi yaran shi bayan ya zauna ya shiryasu da kanshi don ita madam din sai aukin barci da takeyi wai duk ta gaji shine ya shiryasu da kanshi zuwa gidan su su gaida iyayyan shi. Tunda yai sallama mommy ta ganshi tare da yara wani irin dadine ya kamata lokaci guda saidai tana mika hannu yaran sukaki zuwa wurin ta hakama kannen shi. A nan ya samu labarin mahaifin shima yana gari sai bai dade part din mommy ba ya je tare da yaran su gaisa da daddy din. Sun sameshi yana waya ya mika hannu su zo sukaki suka make a jikin mahaifin su daddy ya gama waya yake fadin ku ke nan baku san kowa bako ? Zasu sani ai dole modibbo din ya fada yana dora karamar saman cinyar shi daddy din ya juyo yana fadin sai kaji ina zancen aure summaya ko ? Wace summay ke nan kuma daddy ya tambaya yana kallon daddy din daddy yayi murmushi yana fadin har ka manta sunan baby Summaya ne kanwar ka na wurin karima dai. Baby dai ta gidan nan daddy kake nufi yace ita fa uwart tace aure zatayiwa yarta ba zata tsaya yin karatu ba sun sama mata miji dan uwurin Alh gyade. Wai Ma,aruf dai ko wa shi kuwa dai wai shine zanbin kanwar taka naso na hana uwar ta ta saka min tashin hankali ka barsu ayi tunda haka suka zaba da kansu ai. Nadai fada masu duk abinda ya taso babu ruwana don kada su kuka dani tace ta amince da sauri modibbo yace amma daddy gaskiya kasan akwai matsala sosai yaron da ko karatun kirki bai tsaya yayi ba za a dauki ya a bashi do kawai yana wani guntun sana,an shi kuma yarinya karama kamar baby ? Ai itama din bata yi ba kaga saisu karata can suji dashi tunda haka uwarta ke so don na nuna rashin yardana shekaran jiya nan taso rikita min gida da hauka. Allah ya sauwaka ya fada yana mikewa tsaye daddy zan kai su wajen anty su gaisa ban shiga can din ba ya amsa da haka nada kyau kafin ka tafi zan fito waje in ganka. Yayi ta sallama a falon hjy karima ba amsa ba ya juya zai tafine yaji muryan Fatima na amsa mashi daga ciki ya tsaya. Tana bude labule ta ganshi tsaye tare da yaran shi take fadin lah yaya kune ashe ta juya tana fadawa uwar dake fitowa ga yayan mu yazo. Ta wani tabe baki tare da fadin wani yayan ku kuma a lokacin ya shigo da sallama a bakin shi ta amsa mai tana fadin yaushe garin yace jina dawo anty. Ya gaida ita cikin mutunci ta amsa mai kadaran kadaham sai fatimane tayi kokarin karban yar bataki ba taje wurin ta kuwa sun dai dan gaisa ya daga zai fita take fadin ka shiga wurin Alh ne ko yace eh daga can nake yanzu ai. Yayi ma bayanin auren kanwarka daya taso ko yayi murmushi kafin yace ya fada min yanzun nan don nasamu yana waya akai yake min bayani. Amma zancen karatu fa anty tace tayi a can ai munyi magana dashi kan hakan yace toh Allah ya sanya alheri yasa wurin zaman tane tace amin amin nagode don jin baiyi wani korafin kar ayi ba bayan haka. Shima din yace hakane don yadda daddy ya fada mai sun kwasa da ita to tunda daddy ma bai iya da abinsa ba shi me zaice yanzu kuma banda fatan alheri. Ya mike yana fadin ina ita baby din take tace tana ciki tana washe baki ya kamata in ganta kafun intafi inji ra,ayin ta anty kada a saya mata abinda ranta baya so. Nan ma taji wani irin dadi sosai koba komai sa yaga a wurin shi dama dai rigimane bata shirya auren yar ba a lokacin zancen ya taso daga sama haka. Baby ta kwalawa yar kira ta amsa daga ciki sai gata ta fito da dan wandon jeans da rigan bubu ja a jikin ta tana ganin shi ta washe baki yace see you . Ta rakube tana dariya ya kara fadin amarya ke nan ashe zamu sha buki shine koki kirani ki sheda min ko ta dan boye fuskan ta ya miko mata hannu yana fadin zo mu saka labule kada anty ma tajimu dagani sai ke ta biyo shi suna rike da hannun juna suka fita daga dakin ganin haka sai kuma uwar ta dan tsargu da hakan tana gudun kada ya zugata Suna fita cikin ikon Allah a daidai kofan su yaja ya tsaya yana fadin kin gane ko duk wani abinda kike so sai kimun list din shi kada kiji komai har in kina so ki rubuto min komai ba matsala insha Allah zan saya maki shi Allah ya baku zaman lafiya tace amin a kunyace. Ya wuce yabarwa Fatima data dauki yaran ta shiga ciki dasu ya koma part din mahaifiyar su ya samu ta shiga dakin ya bita can suka zauna yana fadin ashe aure za aiwa baby ? Mommy tayi wani ajiyan zuciya tana fadin ashe sun fada maka kai yanzu ba wanda ya fada min daga uwar har mahaifin ku. Yin ma abin akeyi a boye kamar ba,ason naji ko idan naji bana bari ayi ko wani abu can dai indai wanan yaron ne ai gasu gashi ko. Suma wa yan nan Allah ya zaba masu na alheri masu addini da sanin ya kamata, yace amin lokaci ne baiyi ba idan lokaci yayi suma ai yi zasuyi insha Allahu. Hakane komai bai wuce lokacin sa ai saukin abindai ai sunyi karatu don haka naje na samu wai ashe Sahiba har ta hada digree dinta wanan shekaran harma tana aiki a wani company nan lagos din. Ka san inda suke yanzu ke nan uwar ta tambayeshi yace na sani mana dama nasan gidan da suke ai bawai ban sani bane barina kasan nan daine . Ita Sahiban har ta hada karatunta tana aiki ga wa yan nan zaune a gida aikin ya buwaya koda yake Alh ne dai bai yarda da wanda aka samu ba ai dama. Bawai aikin bane mommy kinsan zan iya sama masu inda zasu jona su tsaya suyi karatun ne yadda ya dace amma sun tsaya wasa. Ina yaran ta fada tana kawar da zancen kada yai nisa yake fadin suna gun su fatima na barsu suka zauna kuma ta kara tambaya ? Yace sun yarda da ita nan dai sukai ta zancen kan abinda ya shafesu a karshe sai ga yaran an dawo mashi dasu ya daukesu basu jima ba yayi masu sallama suka tafi.
Chapter 160 · 0% Book details