Sashe 41
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
da sauri nakai mai card din ya karbi mtn na dari biyar yace give me five hundred change na bashi sai yake kuma kokarin wucewa da card din da kudin duka nace. Olay give me my money nd my card u de call me thief becouse of ur money ? no be thief u are ? U own my card nd my money u wan run with ur nape sai fada ya barke a tsakanin mu dashi a wurin. Kaya kaya ya sauko ni kuma na fara gyara kayana da kyau ina shirin fada dashi murya mukaji a bayan mu ana fadin waitin de happen ? Na juyo da sauri ina fadin na my money he wan run with bayeraben ya kara fadin oga i go nak dis yeye girl if she call me thief again. No be thief u be na sake fada nima a hasale oya give her d money dan sandan dake da kayan kaki a jikin shi ya fada.. Mutumin ya kara kallona a shasale sai gashi ya miko min dari biyar biyar da sanda na bashi da kuma eani daga cikin aljihun shi yana nace olesi omo buruku, buruku dadani. Ina tura kudin a cikin katon aljihun rigana mai zip na fada cikin dan hasala akai horn daga cikon motan nan na farko duk muka juya muna kallon motan. Naji dan sandan nan yace bring card for my oga na juya da sauri zuwa wurin mitan farko data tsaya kwadayin ciniki ya kaini ga mai keken kuma. Na isa wurin motan ba tare dana tsaya na kalli na ciki ba na fara fadin mtn zain etisalat, an glo five hundred two hundred own de. Jin anyi shiru daga cikin motan yasa na dago kai a dan hasale don dama kaina yana kasa ina gyara katin dake rataye a wuyana. Don haka ban kalli na ciki motan a lokacin saida na gaba na dago ina fadin oga talk naw me i wan go ina dago kai sai mukai arba dashi na dan so in razana don na kadu da ganin shi saboda na sheda fuskan a yanzu . Sai dai gani biyu ne yasa ja she da hakan na farko zuwa kama mai laifi a gidan hayan mu sai na biyun da yazo karban wayan shi da ya fadi a hannuna. Shine dalilin gane fuskan shi a yanzu da nayi har na sheda shi a wanan ganin da nayi mashi a yanzu. A cikin dan rudewa nace oga u na good evening woo how much own u wan na dan fada a sanyaye yana zaune ido kawai ya kura min daga inda yake sin. Sai na dan tsargu da hakan ga kuma irin kallon da yake minnna mamaki nikan ina ganin hakan sai na juya zan bar wurin da sauri. Naji ance wait cak naja na tsaya a wuri daya ban kuma motsa ba ban juyo ba sai bayan yan dakiku naji murya na fadin come back my oga wan see u. Na sheda muryan mai magana a lokacin dan samdam nan ne na tare dassu wanda ya rabani da mai Nape fada. Na nuna kaina ina fadin emi ina tambaya ya kada min kai a hankali na fara dan takowa a hankali ina nufar su. Nace oga na di card mtn eirtel glo which one u want na fada ina dago kai na dan kallesu . Yace yana nunani da yatsa yace you where is your mother na dan kalli bayana da mamaki koda wani yake yi badani ba, a bayana . Sai naga dai dani din yake magana nace she de for house ya sake fadin where ? Nace In surelere side, yace from there you come here nace yes cikin gyada mai kai ya kura min ido na dan wani lokaci. Kafin yace oya inter d car now take me to your mother place i want to see her wani irin mamakine ya baiyana a fuskana lokaci guda. Nace a cikin rudewa da tashin hankali lokaci guda i de come let me pack my tins na fada cikin juyawa da sauri yana magana ai ban tsaya ba da sauri na shige cikin mutane kafin ai haka na shige wani kwarkwada na gudu . Har ya tura dansandan yabini sai kuma ya sa ya dawo ya barni don yaga alaman ba zai sameni ba koda ya bini yadda wurin keda cun koson mutane da yawa haka. Kai tsaye wani titin na bula na dauki shatan mai Nape sai gida duk da kayana da kudin wani dana dauki kayan shi ban sayar ba a lokacin. Sai gani na iso gidan da wuri har umma na mamakin hakan gareni sai dai naki yarda in fadawa kowa wanan zancen nabarwa zuciyana hakan. Sai dai na yanke shawara a raina cewa zan canza wuri ne nisa dasu yanzu sosai don ni sai nake ganin kamar kamamu har umma yake son yi kan wani laifin da bansam dashi ba a lokacin.