← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 337

Sashe 117

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani tsohone zaune a cikin fararen kaya da farin gemen shi mai tsawo sai wano katon casbaha daya rike a hannun shi yana zaune saman wani farin dadduma mao laushi dakin sai kamshin turare yake tashi a cikin sa kokai waye sai kanka ya sara a wanan dakin don kamshi irin turaren da ya game dakin. Muka shigo da sallama yana amsa muna da wa,alaiku mussalam da harshen yarbanci kafin ya juya wurin Abdulhamid yana fadin sune kazo dasu. Yace eh wanan ce diyar tawa dana fadama tana fama da matsalan sai kuma wanan yar uwan nawa itace ta haifeta su biyune kanin ta yana gida mun barshi. Dadtijun yace Allahu Akbar ya dago kai ya tsura min ido kuri kaman yana nazarina lokacin kallon shi nayi sau daya na dukar da kaina kasa don ba dabi,ana bane saka ido cikin na wani na dan lokaci mai tsawo haka. Allahu akabar ya kara fada yana gyara zama tare da jijiga kanshi yace lalai yarinya tana da abubuwa a kanta masu girma saidai ba masu cuta mata bane don su din kamar na gadon gidane suke a jikin ta. Zasu iya kareta a duk inda za,a iya cuta mata ko za a cuci wani sai kuma yai shiru kamar yana nazari a zuciyar shi sai can ya dago kai yana tambayana. Omoge na dago kai don nice dai yan mata kadai a wurin yace ko zaki iya tuna haduwan ki da wani tsoho da kikai mai tallan magani kuma idan kin bayar ana dacewa sosai da maganin naki. Umma na fadin wa Sahiba sam ai bata taba sana,a irin wanan ba yace ta dakata ni yake tambaya. Da sauri na dago kai ina fadin eh na taba a baya na hadu da wani tsoho na fito talla ban samu abin dauka ba muka hadu dashi. Shine ya bani sari kuma ya gwada min yadda zab dinga bayarwa in rudi mutane sai aka dinga saye sosai dana gwada din. Ya dan girgiza kai yana murmushi kafin yace daga baya fa na fada masu kaf abinda ya faru na daina yace ki godewa wanda ya dakatar dake wanan sana,an . Din sun so daukan ki zuwa ruwana kiyi kwanaki a wurun su da zaran kin fito zaki zama babban mamalawo don shi din ba mutum bane. Mutanen ki yan ruwa suna da yawa a jikin ki sune kuma suke aiki da kakan ki a baya shine suka so komawa wurin ki lokacin. Orishirishi Sahiba yaushe duk kikai wanan abin ni ban sani ba umma ta fada cikin damuwa tana kallona ta kuma juya ta kalli dattijun dake bayani. Ba zaki sani ba ai don ba zasu bari haka ya faru ba yar ki nada wani irin tauraro mai haske duk inda take za a sanda ita haka wasu zasu sota wasu kuma da basu da zuciya mai kyau zasuji basa son ta sam. Irin wanan ajannun na gode suna da wuyan sha,ani sosai koda ance za, a fitar dasu a jikin ta sau dai kawai su lafa amma basa tafiya suna tare da ita ko yaushe. Sai ya kalloni yana fadin dai a cikin yarbacin da ake magana yarinya dan fita zan gana da iyayyen ki akan haka zanyi magana da ya shifi jinin ta kin san duk yadda yan uwa suke suna da dadin sha,anin sosai koda kuwa tasan su din masu matsalane a gareta. Jin haka na bike gaba daya na bar dan dakin kafin su dade a ciki suna magana da umma ina waje na zauna ina faman bin mutanen dake zirga zirga a wurin da kallo. Sunzauna sunbi layi suna jiran a akirasu lokacin don wasu ma a nan muka samesu wurin suna jiran iso daga gareshi ga kuma su umma suna ciki basu fito ba don ina jin maganan su daga inda na tsaya din . Sai can suka fito din ran umma kamar a bace kallo daya nayi mata na kawar da kaina gefe daya haka muka shiga mota kowa baiyi magana a motan muka dawo gida. Lokacin har yamma tayi sosai mun samu Amar a shago yana ciniki muka tsaya wurin shi sai da magariba ya kusa na mike na shiga cikin gidan mu. Wanka nayi kafin lokacin sallah na kunna tv ina kallo kamar daga sama naji muryan ya Almustapha a gidan dan wajen gwaggo harin kaduna. Kafun in tashi zuwa dakina har sun shigo shida Amar da umma Allah ya taimakeni a lokacin sallah kawai nake jira a tayar in tada nawa sallah. Har ya zauna ban samu gaida shi ba saida ya zauna ya jawo Amar zuwa jikin shi suna hira da umma nayi mamaki yadda har umma ta sake dashi haka da sauri. Yana tambayan ta yaya jikin tayi amfani da maganin ko ni mamakine ya cikani saida na mike nake gaida shi da zuwa daga haka na juya zuwa dakina. Umma ta kirani tana fadin ban gane shi bane na girgiza kai na wuce ban tsaya ba na tayar da sallah har na idar ina jin muryan shi da umma din. Mamaki nake daga inda nake zaune mutumin daya umurce ni a gidan mahaifan shi cewa kada in fara in nuna cewa nasan shi koda wasa don me yanzu zai dawo ya dinga kokarin son kulla zumunci damu kuma ? Yarinya nake tabasa a gareshi amma zan gwada mashi don bamu da gata yanzu ba shine zaisa har su takamu yadda suke so ba. Ban fito ba saida zai tafi umma ta kwala min kira na ki amsawa Amar ya leko dakin da dokin shi ya samu na tayar da sallah da bansan kan shiba bama lokacin. Ina ji ya koma yana fadi wai ina sallah ne lokacin haka suka kwasa ta dan rakashi ta dawo ta tayar da sallah itama ban yarda na fito ba son nasan kwanan wasa dole sai umma tayi min fada kanshi. Sai karfe tara na fito a cikin shirina na kwanciya barci suna falo zaune inda Allah ya taimakeni kafin takai ga yi min magana saiga Muniya matar Abdulhamid ta shigo tana fadin . Tazone ta fadawa umma bakon da yazo yabawa yaran su dubu goma tafito da kudin tana nunawa umma tare da ajewa a gaban ta. Ban dago kai na kallesu ba na mayar da hannkalina a wurin wakan da akeyi a cikin tv din kafin can na mike jin suna hira tana fadawa umma maigidan ta da yaran sun fita zuwa asalatu wurin daukan karatu ke nan suke nufi da hakan. Abinci na debo na fito ban zauna falo din ba na shige dakina dashisun dan dade tare kafin mijin nata da yaran su dawo tayima umma saida safe ta shiga gidan ta. Haka yasa bamu hadu da umma ba a ranan sai washe gari na gama aiyukana da nakayi kafin in tafi school na dan zauna ina kurba rwan zafi don ga dabian bayerabe baka fita daga gidan ka ba tare daka saka wani abu a bakin ka ba koda kuwa kurbi dayane. A cewan su koda wani mugun abu zai sameka Allah zai kawo saukin abin da kariya bazai sameka yadda akeso ba ba ku koyawa diyan ku sabawa da dan cin koda wani abune kadan kafin su fita makaranta mata Allah ya tsare ya karemu baki daya amin. Umma ta fito daga daki tana gyara daurin zanin dake jikin ta tace dani bayan takai zaune tace sahiba na dago kai da sauri na kalleta. Abinda kikayiwa dan uwan ki jiya kin kyauta ke nan umma dan uwana wake nan ta watso min harara daga inda take na sake dukar da kai kasa. Ki matsa idan nuna kula shi a garemun da yakeyi shima laifine yin hakan kin dai san bamu da kowa a duniyan nan sai wanda ya tausaya muna yazo ya rabemi kafin shima kwana biyu ai masa aiki ya gujemu. Dan murmushin bakin ciki na sake a fuskana kafin ince umma kema kin fada da bakin ki yanzu bazan taba yarda da duk wani daya shafi wanan zuri,an ba kuma a yanzu. Balle wanan din da tun farko ya iya fada min kada in yarda in sake nuna cewa nasan koda a mafalki ni kuma zan nuna mashi cewa ba shegiya aka haifeni ba ai. Ina fadin hakan na mike ban tsaya sauraren ta ba na fita zuwa school ranan ko Amar ban tsaya jira ba na sa kai na fice a gidan ni kadai. A school ma ban sake jiki ba don abinda ya faru dani da umma da safe haka kawai zai zoya haddasa muna fitina a tsakanin mu. Dole akwai abinda abinda yake dashi a zuciyan shi game damu na nasa a raina amma ko me haka ke nufi wata rana zai fito filine ni dai komai umma zatayi min bazan taba yarda in nuna wai nasan shi ko muna da wani alaka dashi ma. Har na koma gida ban yarda na sake ba har lokacin haka itama umma din hakane ya faru da ita don nayi mata abinda take gani saboda na girma nake ganin har zan iya kin bin dokan ta akaina. Shima din dai haka ya koma yana mamaki yadda yarinya karama ta iya masa duk a lokacin bai gano cewa wai saboda wanan maganan bane daya fada min nayi hakan. Me yarinyar nan take nufi ne wai ko ta dauka takai wata mace ce da har zai nuna ra,ayinsa a kanta yaja guntun tsuki tare da daukan cup din glass din dake gaban shi cike da ruwan lemo ya kurba kafin ya aje cup din yana furzo iska daga bakin shi. Me yarinyar nan ta dauki kanta a yanzu yarinyar dake yawo kwararo kwararo a cikin garin nan da kayan talla a kanta. Da badan maman shi data matsa akan ya binciko wani alakane tsakanin daddy damu ba ba abinda zaisa ya sake kula wa yan nan mutanem ya fada a fili shi daya kamar mahaukaci a falonshi. Shi shi ya fada wai bata sanshi ba a lokacin ne kuma warning din da yai min a baya ya fado mashi a zuciya tabbas wanan maganan yar ficiciyar yarinyar nan ta rike. Da badon tafiyan dake gabab shi ba gobe daya koma yaciwa yarinyar nan mutunci ko a gaban uwar natane
Chapter 117 · 0% Book details