← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 337

Sashe 191

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

hakan. Zama umma ta koma tayi tana ajiyan zuciya tare da fadin ban hana ya fada maki ba amma zai bari ai sai kin karasa murmurewa nan gaba sai ya fada maki haka akeyi. Yaushe ne bukin baby umma na tambaya don in kawar da zancen ta dan sake ajiyan zuciya tace inaga wani satine ko shine bukin ko baifi dai kwana goma ba yanzu abinda ya rage. Ok nace na gyara zamana da kyau zamu tafine amar ya tambayeni daga inda yake zaune nace ina ganin hakan zamu tafi insha Allah. Naga ya dan sake murmushi a fuskan shi don jin dadi abinda na fada kafin na juyo ina fadin amma akai sai ranan daurin aure zaka tafi da yaya Abubakar ko ? Wayan dana kirane aka dauka na fara magana kan ina son a turo min da kayan da nake bukata na dauki lokaci muna wayan kafin na kashe wayan . Shiru babu ya Abubakar gidan mu har weekend din ya kare muka koma aiki ummace ma dai naji tayi maganan shi har sau biyu na rashin zuwan shi din saida dare muna cin abinci ranan monday ya kira waya yana shedawa umma rasgin lafiyan shi. A nan muka karbi wayan duk muka jajanta mai tare da fatan Allah ya bashi lafiya ya amsa da amin. A wurin aiki kuma an fadawa mutane tafiya nayi yasa basu ganni ba sai suke zaton na dawone a lokacin suke min sannu da zuwa ina karbawa. Muna tsaka da aiki kwatsam ba zato ba tsamani ranan tuesday saiga Ogan mu gaba daya ya ziyarce mu shidasu oga jimo. Ba wanda keda masaniyar zuwanshi a ranan sai ganin su mukayi sunzo kwatsan mun dan zauna dasu anyi bayanin da korafe korafe kafin su fito don gaba zasu tafi zai tafi kasan Niger republic shine ya tsaya yaga jikina don an masa bayanin komai daya faru dani a takaice. Bayan mun fito ne muka dan kebe dashi ya kalleni yana kara yi min godiya tare da tambayana karfin jiki nace jikin da sauki. Yace yazone ya duba idan aikin zai jawo min matsala mubar aikin a barsu da Allah abinda yasani sakin dan murmushi ke nan wanda ke nisa damu sai yayi zaton wani zancen soyayya mukeyi a lokacin duba ga yadda muka tsaya a jikin motan muna fuskan sauran jama,an da sukaja baya suna jiran mu gama tataunawan dashi. Wanan matsalan bai shafi aikin nan ba na fada ciwone kawai lokacin zuwan shi yazo min i am OK now na fada godiya ya kara min bayan min fatan alheri da zai tafine mun taka zuwa inda suke yake fadin a gaida umma yaso ace ya samu ganin umma sun gaisa da ita. Bakomai zan fada mata na fada da dan guntun murmushi dauke a fuskana yayi sallama da mutane bayan ya bada alheri ga kananan ma,aikatan dake bakin aiki a lokacin Wanan zuwan nasa ne ya jawo tsegumi ga mutane kowa da zancen da yake fada a wurin ranan bamu dade ba don zuwan shi da tafiyan shi yasa muka bar aikin dake gaban mu din a ranan. Hello mommy na kirakine in fada maki baban su maryam baida lafiya kwanan sa biyu bai iya fita ba . Mommy din ne ta kalli wayan a cikin mamaki da karfin hali tace Nazifa kina da hankali kuwa a rayuwan ki wanan wani irin maganane haka kike fada min kai tsaye haka. A gidan ku ba a koua maki sallama bane ko gaisuwa balle girmama na gaba kada ki kawo min diban albarka a gabana dif taji ta kashe wayab tabi wayan da kallo. Daga Nabila har hauwa dake gefen ta suka kalleta da mamaki jin yau yadda mommy ke fada da sarakuwan nata haka hauwace ta kasa hakkuri take fadin mommy meya faru ? Barni da mara hankalin yarinyar nan duk yadda ka iya hakkuri da lamarin Nazifa sai ta kaika karshe watau. Wai yayan kune baida lafiya ashe kwana biyun nan shine takirani haka kai tsaye take fada min ba sallama ba komai. Yayan mu mommy suka hada baki shifa ni wanan kaddarareb auren da bason nayi sabo ba danace da ba, ayi shi ba wallahi. Don yarinuar nan bata da ranan canzawa a rayuwan ta abin nata ma sai gaba yake yi a yanzu kamar mara hankali. Mommy din ta shige dakin ta tana ci gaba da fada da sarakuwan nata dabata masan tanayi ba a lokacin don itama tana can tana mita akan wai mommy din tayi mata cin fuska a kan dan ta. Sam ta manta da cewa a daidai kofan shi take tsaye take wanan maganan saida taji muryan shi yana fadin kedawa ke wanan maganan haka ? Ta wani irin kallo kofan kawai ta wuce yana kwance yake mamakin wanan hali na matar nasa da bata data ido sam kowa ta samu yanzu take wanan sababin haka yaja tsuki yana gyara kwanciyar shi. Don likitan data ganine yazo har gida ya dubsshi yai masa allura yasa ta dan nuna damuwanta akan rashin lafiyan nasa lokacin har taga tayi abin arziki ta kira mommy . Gashi kuma mommy din ta watsa mata kasa a ido har tana kokarin zagin gidan su ita nata gidan daban ne ko yarabta sun fisu tarbiyane ?. Ba,a kai awa daya ba mommy din ta dira gidan ita da yaran ta biyu don lokacin Faiza tana school bata dawo ba yasa basu je da ita ba gidan. Sunyi sallama kusan sau biyu ba a amsa masi ba da alama kuma suna ciki don ga tv na aiki ssidai babu kowa a falon lokacin. Basu ankara ba hauwa ta kirashi a waya sai ji sukayi tana fadin yaya kana cikine gamu a falon ku da mommy duk suka kallo inda hauwan take. Ba a dauki tsawon lokaci ba sai gashi ya fito yana saye da jallabiya a jikin shi kallo daya zakai mai ka gane ya rame sosai a lokacin da alaman yaji jiki sosai ke nan. Gaidashi suka fara a lokaci guda a vikin kulawa da nuna damuwan su a kanshi ya zauna da kyat yana amsawa don alluran da akaimai a lokacin. Bayan sun gama gaisawane mommy ke tambayan shi abinda ke samun shi yace zazzabine kawai mommy ya wuce kawai ai wanan uban raman da layi lokaci guda haka tun yaushe ne ka fara ciwon , ? Ya dan shafo fuskan shi yana fadin tun ranan da naje gaida ku last nadawo da wanan zazzabin kana cin abinci kuwa yadanyi murmushi yana mayar da kanshi a makarin kujera yake fadin bakin nawane ba dadi mommy. Nan dai ta danyi mai fada akan yaci wani abu ya kalli inda Nabila ke zaune yace dan dafa min wani abu naci mai ruwa ruwa . Wanan maganan da yayi sai yaba uwar tausayi take fadin matarka fa tana inane ita yace ban sani ba ko tana gidan nan don banji duriyan ta ba dai. Sallati hjy ta fara ta kalli hauwa tace ke kira min Nazifa a part din ta yanzun nan da sauri hauwa ta mike ta nufi part din Nazifa din.
Chapter 191 · 0% Book details