Sashe 177
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune suke sun kura mai ido sai harkan gaban shi yakeyi kamar baisan dasu a wurin ba zaune ga lokacin da suka bata a waje kafin su samu shigowa wurin shi falon. Saida ya gaji daja masu rai suna zaune shiru don zakace ba wani mahaluki bayan shi a falon. Gyaran murya yayi ya dago yana fadin kai yanzu manaja har akwai wani hallita da zaizo garin nan ya tayar maka da hankali irin haka ? Kuma kace mace ce yar karama ke maku wanan karanbanin barazanan da rayuwan ku yaya akai sake kabari har haka ya faru dakai kamar ba namiji ba ? Zama manaja ya gyara ya dan shafo fuskan shi kafin yace wallahi Alh yarinyar watau shu,umace ta gaske fiye da yadda kake zaton ta. Don ka duba fa wanan file din Bala ya fada muna cewa shida hannun shi ya cire shi kuma ya boye shi amma yarinyar nan sai gata da files din nan a hannun har kuma ta zakaloshi cikin yan uwa tasan dashi. Koda muka shiga muyi yadda kace sai cewa tayi damu me muke nema wanan nan din ta na hannun ta saita miko muna tana fadin gashi ai ta gama dashi ko mu dauka. Ke nan ta kwashe komai na cikin sa ke nan ta dawo muna dashi din muyi abanda zamuyi dashi wallahi Alh yarinyar fa kada kaso ka ganta duk batafi shekarun yata ta biyu ba da haihuwa. Dan shiru yayi kamar yana nazari can ya dago ya gyara babban rigan shi dake saye a jikin shi daga shi sai ita dama kana ganin jikin shi daya fito daga cikin . Yace yanzun dai manaja a takaice ba zaka iya ba ke nan da wanan yarinyar manaja ya gyara yana fadin gaskiya kusan hakane Alh dole sai kun saka hannu a zancen nan. Zamu saka ita sin me ko oduduwa kakan yarbawa ya shigo gonan mu a yanzu ai zamu kawar dashi ne kamar kauda kara ba wani aiki bane kubani yau da gobe ki gani sai ta nemi agaji ta bar garin nan a gagauce nina fada maku. Godiya suka shiga mashi cikin nuna jin dadin su ga hakan nan kuma sai hira ya barke a tsakanin su oga Bala na nuna masu yadda nake turanci wai nasha mai nayi fari kamar baturiya nazo zan masu barazana da fari a nan shiko yace su za a nuna ma farin shago suda sukaga yan matan kano bila,adadin mai zai basu tsoro kafiram banza kawai. Alh na jinsu kafin ya dago yace meye sunan yarinyar ne koba ta fada maku sunan ta bane ta fada ya dago yana kallon manaja shi oga bala dake ta faman zuba lokacin. Gaskiya na manta don sunan dai gashi kamar na yarbawa kamar na hausawa haka ko larabcine oho ? Sa,ba ko me kusan haka dai ta fada koma waye ai zamu sani ya fada ku bani lokacin dana fada daga gobe zaku ban labari da bakin ku yadda za a kwashe da ita. Godiya suka karayi kadin su bar falon nasa ba tare da sunyi wani maganan akan dawo da abinda ke hannun su don har lokacin zancen haka baizo a zukatan su ba. Shi Alh ma shirme da haushin su yake gani yadda suka wani tsorace akan mace macen ma yar cikin su kwaranya da ita. Tsab na shirya a cikin wando da rigan aikin mu na can mai daukan hankali ga duk wanda yaga kayan namu na fito daga daki zuwa da yar jakar tafiyana ina fadin umma zamu tafi ke nan. Tace har zaku tafi baki karya ba dauki ga tea nan nasan dama haka zaki ce zaki bar gidan nan bakici komai ba. Dole na dan kai zaune nayi bissimillah na kafa kai na dan fara kurbawa saboda akwai dan zafi umma ta kura min ido daga inda take zaune . Nagama nace to umma zamu tafi ina mikewa tsaye tace Allah ya tsare ya kare Allah ya haushe ku a saman su ya sa a dace da abinda akaje nema. Na amsa da amin kofa na tsaya hakan kusan dabi,atace ban fita gida ba tare da addua ba bani ba kusan dabian yarbawane hakan da yawan su haka suke wanan dabian nagama na shafa nafita umma tana bayana. A kofan mu ta tsaya tana min sai mun dawo na amsa na tafi bakin motan Adnan nan na shiga muka dauki hanya mu hudu a nasa motar shida felix a gaba zaune nida yemisi abaya. Felix ne ya fara magana yana bada labarin irin wullakancin da akai masu a can din yana mamaki sosai na yadda suka nuna basu san aikinsu subama sam. Yaja hausa hausa are terreble people ya fada dan gyaran murya Adnan yayi yana masa signal da ido gani nan fa yace. Ainikan yarobace don ban san komai ba ga hausa karshema kila bana jin yaren sosai suka kwashe da dariya nidai murmushi nayi masu kawai. Allah da ikon shi mun isa da wuri kai tsaye muka nufi cikin ma,aikatan kamar dai yadda wacan din ya mutu sai ince wanan din ma kamar ya fishi mutuwa ga ma,aikatan a warwatse wani wurima na hango dabbobi suna kiwo a cikin wurin mota ya tsaya a gaban ginan daidai inda Felix yace ya parker da sauri na dago kai nace ya kara gaba gadan ya tsaya a barin dama. Sun rigani fitowa dukkan su a cikin motar har na dayan motan sukazo suka tsaya a daidai inda motar mu yake tsaye suma suka fito daga cikin motan. Hankalin wa yanda ke ma,aikatan ya dawo gare mu ganin mu a cikin bakaken kaya lokacin ganin Felix da yemisi . Kafin na fito ina bin ko ina da kallo na haraban wajen yadda ma suka bamu lavarin dai naga basu fadi daidai don gaba daya wurin ya lalace sosai. Bamu shiga ba sai zaga ko ina da mukayi har idona ya kyallo min an cire injin biyu dake sarrafa alkama a wurin. Mun shiga muna dan gaisawa da wanda muka gani nice baya ina waya da umma da harshen yarbanci muka kai kofan muna tambayan manager wurin. Wai yau bai fito ba suka bamu amsa naja na tsaya daga baya suma din kamar can da muka barone don gulman sukeyi suna ina kwarin nan suka fito hakane wai ? MD da da sauran manyan wurin muka sama sun kira chairman din wurin shima wai baya gari wani ya gama waya dasu ya juyo yana muna bayani cewa wai yace ace yayi tafiya sai next week zai dawo. Har abokan aikina sun fara maganan kan yanzu ya zamuyi ke nan sai sukaji nacewa mutumin excuse me can i have his number please ? Sai naga sun kalli juna sun juya da hausa suna fadin wa zai yarda a koreshi idan oga ya dawo ya gane nina bayar gaskiya bazan basu ba nikan. Ba zasu bayar ba fa yemisi ta fada tana fadin ranan wallahi ba karamin wullakanci sukai muna ba a wurin nan saida kyar muka samu suka fada muna koshi wanine ya nuna muna tabaya lokacin zai fita ya haumu da fada sosai a wancan wurin. Muje kawai nace dasu suka biyoni baya na bi hanyar matakalar benen zan hau da sauri wancan daya buga waya ya biyo mu da waya yana fadin gashi ya kara kiran layin kuma yana mika muna wayan sai Abdul ne yakai hannu ya karbi wayan a wurin shi. Yz miko min na dauka kuma ban tsaya ba har muka hau saman na kara a kunnena ina ji wai bayanan shi don haka sai kubar, , , , No problem koda baka nan ai company na nan zamuyi aikin daya kawomu mu wuce kada ka damu ai na fada ina mikawa wancan mai wayan wayanshi. Tsarin ginan nabi na gane offince din da nake nema din na nufi can murda kofan nayi yana bude sai nadanyi nocking tare da sa kai cikin officen ga baki daya. Saura suma suka biyoni a baya waya yakeyi a lokacin jin yadda aka shigo mai yasa ya dago a fusace yaga ko waye sai mukai arba dashi ya mike da sauri. Sannu da zuwa yayi muna kafin ya tambaya mudin su waye Adnan yayi mai bayanin daga inda muke da abinda mukazo wurin su yi kuma na bincike kan company. Nan ya fara muna inda inda yana fadin ai tun da suka samu labarin muna kaduna suke kokarin shirya files din saidai basu hada ba har yanzu. Baida matsala ai tunda mun sameka zaka iya debo muna wanda ke nan sai mu fara dashi na fada bayan na kare bin office din da kallo. Yace gaskiya ba zai iya bayar da komai ba shugabanin sa basa nan don haka muyi hakkuri har su dawo din. Kana tsamanin bamu san shirin da kukeyi bane a kai yau din nan da muke son su a hannun mu inyaso saiku cinawa wurin wuta kamar yadda kuka shirya yi din da daren nan ko ? Na fada na kallon shi tare da dan sake mai murmushi har dimple dina ya dan lutsa a lokacin bashi ba kowa na office din saida ya kalloni na dan duka kadan ina aje computer na dana fitar tare da fadin files guda dubu biyune ko da dari takwas da muke dasu a nan a cikin shekara goma sha hudu dayin wanan masana,antar . Yanzu kuma kuna kokarin fitar muna da guda dubu da dari takwas sauran fa malam idan kun boyesu koda yake no need ku fitar muna da wanda kuyi niyar fitarwa din ba matsala zamu samu komai a cikin wa yan nan din na hannun mu. Sorry mah ya fada da dan rawan jiki ba laifina bane yin hakan nima umurni akabamu muyi hakan daga saman mu waya kawo wana idea din na tambaye shi ina kallon shi ido a cikin ido. ( Mai karatu zaki iya cewa wanan shirine don labarin yayi dadi haka Allah sarki ranan da Allah ya hada ki da wani dan baiwa mai abin mamaki zaki tuna da ni Sahiba ashe labarina ba karya a cikin sa. Ni kaina haka dai Allah ya haliceni nake gani banda matsalan ciwon kai gaskiya bansan ina da wani matsala a jikina ba .