Sashe 227
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
arziki saboda sun camfa mahaifiyar shi har shi din da wanan mumunan zaton nasu. Shigowan Nazafi dakin ne ya katse mashi tunanen sa bita yayi da kallo har ta karaso tazo ta zauna a gefen gado yana yadda ta sameshi a rigingine bai motsa ba har lokacin. Baban maryam na dawo ban hakkura ba ta fada a daidai lokacin da yaji wani irin zafi a zuciyar shi na yadda take kiran sunan maryam gatsau haka a gaban shi . A cewan ta ta juye sunan mahaifiyar nasa zuwa na kanwarta da kakanta wai ai sunan sune ya saka bana mahaifiyatshi din ba. Nan ma dai shiru yayi mata shi kadai ke jin yadda yake ji a zuciyar shi lokacin a kanta ta sake fadin bb maryam don Allah kayi hakkuri ka saurareni . Kada kayi fushi don Allah dani kace ba zaka ban kudi ba in kaiwa Abba don wallahi duk yan uwana sun kawo masa nasu gudun mawar nice da hafsat muke rage bamu bayar ba a yanzu. Nan kan ya dan muskuta yana fadin me kudin makiyi zai karashi dashi a yanzu tunda a matsayin makiyin shi nake nida kowa na gidan mu a zuciyan shi. Shine kuma zan dauki kudina yau in bashi ai kema kin san ba zai karba tunda ni da diyana jinin makiyin shi muke. Wanan zancen da kakewa Abba yanzu kan ko wanda bai hada komai dashi ba ya kawo mashi kudi ai karba zaiyi yadda yake neman kudin nan ido rufe. A yadda naji har filincan nasa na hayin malali ya saka a kasuwa wai ba a taya filin da kudi me yawa ba yasa bai sake shi ba. What ya fada da karfi yana dagowa daga kwancen da yake ya kara maimaita tambayan da badai filin nan daya fara gina company atamfa a cikin sa ba ? Ta dauka ya damu da jin hakan ne sai tace a cikin marairaice wallahi kasan mutane da son banza suka dinga taya masa shi a wullakance shine ya fasa gashi ance lokacin da aka basu ya kusa cika dole yaje da wani abu mai dan tsoka da zai fara biya. Umm,mm ya fada ya koma ya kwanta yana jin wani irin a zuciyar shi lale wanan mutumin da karfin hali yake sosai watau filin marayu din daya mallakawa kanshi da karfi da yaji shine zai saka kasuwa yanzu da yake ganin filin zai iya fita hannun shi duk da basu yarda da cewa iyalan mai filin suna raye ba . Ba abinda ya kara daga masu hankali kamar jin wai harda da umma tazo masu wai dan dan uwan sune shima din wanan ya fi daga hankalin su sosai don a mota da zasu dawo daga karbo Alh Nuhun can abuja yake jin su baffa hamza na wanan firan. Muryan Nazifa ne ya katse mai dogon tunanen da ya shiga din lokaci guda tana fadin kaji dalilin dayasa akai shawaran tara masa kudin a bashi. Ok naji sai na duba ya iya fada don baison maganan ta kara masu nisa a tsakanin su yana son yin dogon nazari a lokacin. Shine washe gari ya dauki waya ya kira umma yaji yaushe zamu dawo don asan abinda za ayi kafin Alh Nuhu yakai ga kadar da filin ya salwance a dauki mataki. Bayan sun gaisa da umma ya tambayi lafiyan sune yake fadin ya labarin Sahiba umma yaushe zasu dawone daga tafiyan ? Sai umma tace a cikin murmushi ai gata nan a gaba da safen nan suka dawo masha Allahu ya fada tare da fadin an dawo lafiya ko ya aiki kuma ? Na amshi wayan ina fadin yaya mun sameku lafiya ya su mimi da maman su karo na farko tun farun matsala a tsakanin a baya . Duk suna lafiya ya fada OK zan barki ki huta zan shigo zuwa jibi akwai maganan da nake son zamuyi daku na muhinmin idan nazo din. Ok yaya na fada a lalace ina mikawa umma wayan dake hannu din ta karba ban san dogon bayanin da yake mata ba a lokacin na dai ga umma ta bata fuskan ta sosai lokaci guda. Sai bayan sun gama wayan ne umma ta sauke ajiyan zuciya tana kallona take fadin wai filin mahaifin kune da Alh Nuhu ya mallaka har ya fara gina a cikin sa yasa a kasuwa zai saida ya biya basusukan da ake binshi yanzu. Au filin yana nan ashe na fada cikin mamaki ina kallon umma tace haka dai yake fada min yanzu wanan akwaishi da karfin hali da iya cin amana. Ya kai karshe don wanan ko ya sayar saiya dawo hannun mu na fada ina komawa kasan kafet na zauna tare da kallon ammar wanda nasan ni yake jira na bude kaya ni kuma naki bude mai. Murmushi ya sauke a fuskan shi yana fadin anty please na nuna mai kayan da hannnu ya dauko muka fara budewa don ni kaina ban san meye a cikin sayayyan nasaba tunda bani na saya ba. Allah da ikon shi kayan umma ne muka fara budewa kalla bakwai irin dunkunan Dubai din nan na manyan mata tun a jakkar na gane haka don an rubuta a harshen larabci da ~umma~ . Nan muka duba mukaga komai na ciki harda wani handbag mekyau sosai na manyan mata na Ammar na jawo na duba suna na tura mashi gaban shi ya bude. Komawa nayi na jingina kaina saman kujera tare da dan mayar da kan nawa baya ina lumshe idona ba komai nake tunane ba sai zance biyu na farko zancen sayar da filin Alh Nuhu sai kuma zancena da Alaja. Ihun Ammar ne yasani dan dagowa ga yadda nake zaune ina kokarin ganin abinda yakewa ihun wasu suit ne size din shi masu kyau gaske irin da yaran su can ke sakawa ya dago yana fadin Antymi wanan rigan yai min kyau sosai wallahi ya fara min godiya. Bani na sayama ba na fada kai tsaye don ban iya karya ba na kalli na umma da nawa nace ogan mune ya sayo wa yan nan duka a dubai. Wani kallo umma ta jefo min mai alaman tambaya nayi saurin fadin wallahi umma ban san zai saya ba yanzu ma mamakin hakan nakeyi yadda ya iya zabe haka kamar an auna tsayin ku. Wayana ne ya dauki kara na mika hannu saman kujeran na dauka ina dubawa don ba wanda ya kirani tun shigowana gida har washe garin nan. Sabon layi na gani na kasan waje daga kasan Germany da mamaki a fuskana na dauki wayan ina daukan wayan a bangarena. Irin sallaman dana tashi dashi a bakina na dabi,an yarbawa nayi a wayan muryan da aka amsa min sallaman ne a lokacin yasa gabana faduwa lokaci guda duk da na sheda muryan me kiran nawa a lokacin. Kun isa gida lafiya ya kuka samesu duk ya fada a lokaci daya da kyar na samu cikin kyarman murya na hada dace masa Alhamdullahi. Masha Allah ya fada sai kuma yai shiru kamar yadda nayi shiru a nawa bangaren bayan dan second na tsinkayi muryan shi yana fadin. Ina Germany na samu contrac dasu zan shigo masu da wasu kaya daga Labeno sun yarda sun saka min hannu wanda hakan zai jawo min dagawa sosai da yardan Allah. Masha Allah nafada tare da mashi fatan gamawa dasu lafiya na nuna murna a fili kwarai ya dan kara min bayanin yadda abun zai kasance mashi kafin ya dan sake yin shiru na wani lokaci yace. Kiyi hakkuri da abinda mahaifiyarmu tai maku sahiba musanman ma ke kasancewa na bana wurin lokacin da hakan ya faru a tsakanin ku. Murmushin dole nayi ina fadin haba dai wanan ba komai bane don muma ai tana a matsayin mahaifiyace a garemu na tsunci kaina da fadin hakan. Nasan hakan Ganiyat da Jimoh sun fada min komai daya faru don haka kiyi hakkuri tunda mun san dalilin yin hakan a gareki. Na fahinci yaji komai daya faru a dubai din nace kuskure fahinta ne aka samu duk wani mairai idan abu yazo masa a lokacin da bai zata ba zai iya aika kome yake gani a matsayin kariya a gareshi. Nagode ya fada yana sauke ajiyan zuciya a hankali har ina iya jiyoshi ku zauna ku huta na mako daya kada ku fita gun aiki murmushine ya dan subce min nace. Oga ai mun huta zaman yayi yawa hakana gara mu koma bakin aikin mu don nema ya kaimu wurin ka ba hutu ba don haka dole mu koma muci gaba da aiki hutun ya isa hakana. Ke baki kama da wace zatai ta aiki ko wani lokaci ba hakana shigan ku office officialy ne yanzu sai idan bukatan hakan yataso a garemu. Wani nauyi da kunya naji lokaci daya nace nagode yace kada ki damu nike da godiya a wirin ku ki mika min godiya ga mama ya kashe wayan. Na dago muka hada ido da umma data tsura min idanu budan bakin umma tace min kiyi hankali da irin mutanen nan da suke yawan son diyan su maza . Kallonta nayi cikin mamaki tace kwarai saboda data kula da cewa wani abinda batayi tsamani ba yana shirin faruwa a tsakanin ki da danta yasa ta fara bullo maki da haka. Batayi karya ba don ko wani tsuntsu kukan gidan su yakeyi tana ganin ke bakiyi daraja da mutuncin da za a ce danta ya nemeki ba don kedin ba yar kowa bace take gani kuma ga wanan matsalan dake a kanki. Sai lokacin nayi magana jin umma tayi shiru nace umma ki gafarceni ban taba saurayi ba a tarihin rayuwana. Saidai a tunanen ita Alaja din tana ganin kamar muna soyayyane da dan nata wanda ba hakabane a wajen mu nasan dai ya bukaci in taimaka mashi in nuna kamar soyayyan mukeyi a gabanta. Nan dai na labarta mata abinda ya faru a can kaf ban boye mata komai ba saida na gama take fadin wanan gangancin fa Sahiba ?