← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 337

Sashe 2

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana tafe da sauri har tana tuntube don dan yayafin da aka fara tasan ruwane ke shirin saukowa a lokacin.
Amma haka bai hanata sauri ta nufi titi mafi kusa inda tasan zata samu mutane a wurin .
Saidai kafin ma takai titin ruwa mai karfi ya gwauce haka ta dinga tafiya ta hango jerin motoci da ke saman titin sun jera dogon layi don go slow din ya hadu a lokacin .
Haka ta fara bin motocin tana bara tana neman taimako gana Allah da wanda yaji kyanta ya bata don Allah a cikin wanan ruwan.
Glass din motan shi ta gefen shi yaji ana kwankwasawa ya dan dago daga abinda yakeyi da sauri yana kallon wurin.
Mace ya hango a tsaye duk wanan uban ruwan tana cikin shi hankali kwance wanda suke tare ne yace dashi a cikin harshen turanci wa yan nan mutanen ne yan bara .
Bara a cikin wanan ruwan haka yace kana mamaki ne su ai damane ya samu masu ga wanan lokacin yadda aka hafa go slow din nan haka.
Dayan gefen ta koma tana kwankwasawa a hasale ta miko hannu ta inda aka dan bude din tana fadin Wahidu oga .
Give me something oga even small Allah will reward you with , , , , kai innalillahi wanan mutanen suna da kaskantar da kai wallahi ya fada a hasale.
Ta kara mika hannu tana fadin Wahidun Oga give something to eat a hasalw zai rufe glassa din na tare dashi yace a, a yana bude wani wuri yace bari mu bata don in ba bata mukayi ba haka zasu damemu da wanan baran .
A lokacin ya dago kai yana kallon ta tana sharce ruwan daya kwanta mata a fuska da alama karfin ruwan yana damun ta itama a lokacin dubu biyu yayi niyar zarowa sai ya zaro kusan hudu haka takai hannu ta wafta duka a hannun mutumin tana jiyawa da sauri bayan godiyan da tayi mai .
Binta da kallon mamaki yayi kafin yace innalillahi wanan yarinyace karama da wanan halin banza iri sune ma yan iskan gari.
Dan murmushi na gefen shi ya sake yana girgiza kai tare da fadin indai wanan erea din ne zaka sha mamakin su ko wani yare zaka samu a nan tundai hausawan ku yan arewa sun fi yawa ga wanan harkan na bara yaja tsuki yana kawar da kai.
Tare da jin haushin hakan a zuciyar shi ga yarinya har yarinya amma ta tsaya tana wanan kazantar sana,an dayafi tsana ko a arewan su.
Balle lagas da yake ganin hanyoyin sana,a sun fi a kirga ga neman kudi idan mutum ya tashi nema din.
Har suka kai gida a na sheka ruwan sama a lokacin suka fito daga motan a cikin ruwa hakan yasa suka dan jika kayan jikin su din.

Kallon kudin dake hannun ta taji wani irin farin ciki ya kamata da sauri ta juya don barin wurin har tana dan hadawa da gudu gudu don tunawa da tayi tun safe basuci abinci daga ita har kanin ta Amar da duk suka dogara da ita a yanzu.
Tun daren jiya batayi barci da dadi ba idan ta tuna babu abinda zasu ko karya dashi a gidan haka yasa bata kaunan komai nasu ya kare.
Tasan wanan din zasu samu su danyi amfani dashi har zuwa dare in yaso sai ta fito ta nema masu abinda zasu ci.
Da sauri ta karasa wani shago mafi kusa ta sai duk abubuwan da zasu buka mai saukin ci sai a lokacin ne ta kula ashe kudin yafi yadda take zaton ta samu.
Wani irin shu,umin murmushi ta sake lokaci guda nan ta kara sayen komai wadatace da zai ishe su har karshen jibi da safe .
Har ta isa gida ba,a kare ruwan saman da akeyi ba haka tsamo tsamo ta samu ta isa kazamin unguwan nasu da babu abinda ke tashi banda warin kwata da bola a lokacin.
Cikin rashin damuwa da hakan saboda sabo da tayi da hakan a yanzu yasa bata ji kazantar komai ba a lokacin
Kowa na gidan yana dakin shi ya labe ganin yadda yawancin kayan gidan suke iwo a cikin ruwa ganin haka yasa ta tuna da dakin su dake zuban ruwa sosai ga mahaifiyar su ba lafiya duk kwanakin nan wanda tasan ba komai bane ya kawo hakan sai aikin wahalan da takeyi kullun don saman masu dan abinda zasu kaiwa cikin su.
Da sauri ta tura kyauren dakin, dakin ya bude can ta hangosu a takure wuri daya ga yan tsumakaran su duk sun jike da ruwan da ke diga daga saman kamar indararo a dakin.
Da sauri ta karasa inda mahaifiyan nasu take labe tare da dan kanin su karamita dauko wani babban bargo suka kare kansu su ukun gaba daya a ciki.
Duk da halin da sule ciki haka bai hanata dauko masu abinda ta sawo suci ba a takure a wurin suka ta mike ta dauko ledan pure watar daya daya rage masu a dakin ta kawowa mahaifiyar nasu da kanin ta su sha, .
Kai mahaifiyan ta kada tana fadi da kyar kusha keda dan uwan ki ni zan dan samu ruwan saman nan da akayi insha.
Wallahi Umma ba zan sha ba don ban ma jin kishin ruwa a yanzu din ta fada don hankalin uwar nasu ya kwanta tasha ruwan ta sauke wani irin ajiyan zuciya ta juya ta kalli uwar nasu tana mata sannu umma .
Muryan mahaifiyar ne ke fadin kece da sannu da ubangiji ya hore mune ke kike samo muna abinda zamu sakawa cikin mu a cikin karfin ki.
Sahiba ban da kwankwanto a kanki don nasan irin tarbiyan dana taso maki dashi tun farko naki dogara da karfin ki ki tallafi kanki ba sai kin zubarda mutuncin ki da kimarki ba ga maza a karshe ki koma abin kyama a garesu .
Sahiba yadda kike muna Allah ya biyaki da mafificin alherin sa a rayuwan ki Allah ya baki masu rama maki irin abinda kikai muna.
Kin kula dani da kanin ki tun kina mitsitsiyar ki har zuwa yanzun duk wani wahalan mu da dawainiyar mu duk a kanki yake yanzu Sahiba.
Allah kadai zai iya biyan ki don Allah yasan komai daya jefa rayuwan mu a cikin wanan halin da gatan ku a duniya kun koma mabukata karfi da yaji kan wani dalili nasu can na rashin imani.
Da sauri yar ta dago kai ta kalli mahaifiyar nata don wanan ba farau din ta bane wurin fadin da gatan su amma wasu sunyi dalilin komawan su hakan.
Duk da nasan Allah ba zai kyalesu ba suma a kan wanan abin da suka aikata muna a rayuwan mu na shiga kunci da wahala irin haka a yanzu .
Ina alfahari da samun ku a matsayin yaya a gareni Sahiba don da wuya a wanan zamanin a samu ya data fiki tausayin iyayyenta da yiwa mahaifiya biyayya irin haka.
Sahiba a kullun ina maki adduan Allah ya baki kyakyawan sakamo arayuwan ki don a yau in munci munsha duk a dalilin kine Sahibat a duniyan nan.
Hawaye suka silalo a hankali daga idon Sahiban dake sauraren uwarta kan ta na duke a kasa .
A hankali ta lumshe idon ta tana tunanen yadda rayuwan su zai kasance a nan gaba dan sanin yadda suke fuskantar rayuwa a yanzu.
Ga tambayan fam a zuciyar su amma babu mai bata amsan hakan duk mutanen da tasan umnan su na zaman arziki dasu tun farko tabi ta tambaye su ko daga ina suke amsa dayane basu san garin su ba ko yan uwan su suma dai ganin su sukayi kwatsan a lagos.
Abinda suka sani shine daga dai arewa sukazo lagos din da goyon sahiba da cikin kanin ta kuma a jikin umma din amsan da take samu ke nan a gurin wasu da suka san su a baya.
A kullun ta shiga irin wanan tunanen ko wani matsin rayuwa irin kalaman umma gareta ke kara mata karfin gwiwa .
Har ta ji hankalinta ya kwanta da rayuwan su a nan din don ta fahinci inda umman nasu tabaro yan uwan su da mahaifanta yana da zafi da ciwo a garesu ke nan da zama can din.
Don haka takan kwanmacewa rayuwan su a nan lagos duk da irin gwagwalmayan tashin hankali da fitinan da suke gani yanzu a rayuwasu.
Indai hakan da umman nasu tayi na nisanta su da yan uwan su har take ganin shine mafita a garesu.
Idonta ta bude da suka ciko da hawaye ta nisa tana sharewa a hankali tare da tunanen yadda zata bada hinma ga rayuwan su dana mahaifiyarsu din duk da tasan abune mai kamar wuya a gareta a yadda suke nan.
Ganin ruwan saman ya tsaya cak ta mike daga inda suke zaune ta fara gyara dakin don su sami wurin kwana a ranan saboda haka suke a yan shekarun nan idan ana ruwan sama bata da huta a rayuwan ta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANA DARA GA , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI YAN UWA BARKAN MU DA JUMM,A

ZAINAB IDRIS MAKAWA
Chapter 2 · 0% Book details