Sashe 243
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
mata din a cikin gidan shi baffa buhari na fadin akan me zata gudu don ta ganku. Har zuwa kashedin da Alh nuhu yai mata washe gari akan saura ita a gaban mutane yake fakan idon su ya nuna zai yankata itama haka ya sata dauki yarta ta gudu daga garin baki daya ke nan har taje can tayi renon cikin dake jikin ta tare da diyanta duk a can ta karashe a cikin kuka kotun ya dauki salati lokaci guda. Haka masu raunin imani a kotun ma suma kukan suke taya umma na labarin data bayar din a lokacin mai taba zuciya Ina gefe a zaune na hada kai da kujeran kotun dana zauna akai ina faman kuka sosai duk da kamshin da naji na turaren shi hakan baisa na dago kaina ba na daiji mutum ya zauna a kujeran kusa dani ya miko min handcarchef in share fuskana. Bayan na gogene na dago da niyar inwa maishi godiya idona ya sauka ga ogan mu zaune a kusa dani daga bayan mu kuma sauran jama, an mune a zaune. Dan zabura nayi dan mamakin ganin su a wanan lokacin yace be cool kada ki damu, damu a yanzu mu saurari mai wanan alkalin zai yake nan gaba. Kai kawai na iya gyada mai a hankali naci gaba da goge hawayena dake zubo min muryan lauyane ya dawo damu kallon gaban kotun yana fadin. Ya mai sharia wanan shine shedan mu ta biyu dake nuna su alhaji nuhu sune suka kashe dan uwan su saboda wani bukatan da sukaje wajen shi dashi a ranan. Objection my lord wanan ai bai isa sheda ba don za a iya tsara mata fadin hakan tazo nan tana muna kukan karya don tana ganin ba zamu gane hakan ba. Lauyan su ya fada namu zai tare alkali ya daga mashi hamnu ya koma ya zauna wanan ya tunkari umma. Yace hjy mairo munji shirin da kika tsara muna a yanzu saidai abin mamaki ke a lokacin kina ina har haka ya faru baki sani ba . Tace na fada ai jikin yarmu da yayi zafi a lokacin ya turani dakina in bata magani nima nasha maganin daga nan na tsaya na shimfide ta shine barci ya dan daukeni ganin shi yana ta faman rubutu a cikin littafin shi na siri yasa na zauna dakin kada mu dameshi don nasan inya gama zai nememu ai ko don yaji lafiyan yar shi. Shine a cikin dan barcin daya daukeni na fara jin kamar kakarin shi na fito zuwa dakin shi da sauri a nan na samu sun gewayeshi su hudu Alh Nuhu ya dora mai yuka a wuya shi ya ganni sai dai su basu ganni ba da hannu yayi man nuni da in gudu. A daidai lokacin da shi Nuhun ke fadin dama kai kadai ka rage bakin irin a cikin mu yanzu sauran basu dameni ba kawar dakai shine yafi a garemu ya fara yanka mashi yuka yana rokom shi idan kun kasheni ku kula da matana da yata da ciiii daga nan sai salatin shi naji da karfi alokacin na dauko yar muka fice ta kofan kitchen ta baya na nufi dakin maigadi don babu kowa a wajen . Sai bayan na shiga ne na dinga ganin innuwan mutum a cikin duhu yana zirga zirga a wurin yana tsuki tare da fadin wai daga magana sun nemi wuri sun zauna. Kuka ya hana umma karasawa shima lauyan komawa yayi ya zauna yana dan caka biron dake hannun shi saman takardan shi . Alkali kuma sai faman rubuce rubuce yakeyi a nasa takardan lokacin kukana ya tsananta sosai yasa ban iya jin komai. Hannun Ogan mune naji saman nawa yana fadin be strong ba a cin yaki da ragganci ki zama mai karfin zuciya ko yaushe da zafi amma ki daure. Kai kawai na gyada a lokacin don ba zan iya fadan komai ba duk lokacin da ake bada wanan labarin nakaji wani iri a cikin kasan zuciyana nakan kwantanta irin zafi da radadin da mahaifin mu yaji a lokacin. Muryan lauyan mune yake fadin ya alkali mai sharia zanso ganin buharin da ake zance a gaban kotu yanzu ya amsa min wasu tambayoyi kafin nan ga wanan mai sharia ya gani bayanin dashi marigayin yayine a cikin nan din. Aka karba aka mikawa Alkalin ya gyara zaman glass din shi ya fara duba a hankali nan akai cigiyan buhari ya fito a gaban kanta ana neman shi. Kowa ya bishi da kallo har ya karaso ya tsaya gaban su hayaniyane ya fara tashi lokaci guda a tsakanin su Alh nuhu da yan kallo da kyat alkalin ya samu ya saita mutane akai shiru lokaci guda. Sai a lokacin na dago kai na kalli wanda ake kira da buharin nayi mai kallo na tsana da ki shima din yana da zubi hallita irin nasu saidai baikai su shekaru bane kawai shi. Lauya ya fara magana Alh buhari ko ya amsa da eh yace sunan ka ya fito a sharian nan kusan sau biyu ke nan ko zaka fadawa kotu abinda ka sani game da abinda ake tuhuman yan uwan ka da aikatawa ga dayan dan uwan ku da Allah ya karbi rayuwan shi a baya. Fuskan shi ya dan shafo kafin ya soma fadin eh to gaskiyan abinda na sani dai shine shi dan uwan namu ya dawo daga tafiye tafiyen da yakanyi a kasashen ketare . Sai wanan kayon ya bukaci daya ganmu a nan bayan mu hadu a gidan mahaifin mu yake fada muna cewa wanan tafiya ya samu haske da yawa a cikin shi. Nan ya bukaci da mukawo ya shawaran abinda zaiyi har muma mu karu da yaga ba wanda yai magana yake fada muna nasa kudirin a lokacin . To sai abin baiyi tasiri a zukatan sauran yan uwan mu ba bayan mun bar wurin shine suka bukaci damu hadu muyi wani shawara a lokacin. Lauya ya tareshi da fadin ku nawa ke nan fa yace iya mu yan dakin mune a lokacin amma kuma da mukazo taron sai naga Alh bello da Alh tanimu dinne ma suka tsara duk yadda za ayi a tunkar shi sambo din lokacin. Kamar wani irin tunkara ke nan lauya ya tambayeshi yace eh to a gaskiya shawarane kan yaya shi da yake karami a cikin mu don mahaifin mu ya dauki nauyin karatun shi za ace yanzu shine zai juyamu. Ma,ana ya fimi arziki inma arzikin ne aida kudin mahaifin mu yayishi tunda shanun da dukiyan mahaifin mu aka batar har ya samu ilimin nasa. Don haka dole ya kawo dukiyan da yake ikirarin ya samu a kasa aba kowa nasa ko kuma muyi karan shi akwato muna hakkin mu. Na basu shawara kan mu barshi da abinshi shi Allah ya zaba a cikin mu sun nuna min ba hakan ba nace to ba laifi nizan tafi. Sai na manta da dan ledan dana shigo dashi wurin na dawo daukane na samu sun canza maganan shi Alh nuhu na fadin sai in halakashi in halaka banza ba zan sa ido ina kallon takaiciba hakana. Nace kai haba dan uwankane fa ina laifi dai kuyi mai maganan da kukace zakuyi zaifi nabar wurin hankalina bai kwanta ba na samu yayan mu Ali dcp da zancen sai cewa yayi in barsu suyi mai magana ai sambo dukiyan nasane abin tambaya. Nikan lokacin dana bar wuri Ali dcp ina mamaki saina nufi wurin sambo din na fada mai komai dake faruwa akan ya dauke iyalin shi yaje wani wajen. Sai ya nuna min in yan uwan shi na haihuwa sunkishi ina zai tafi ke nan da yamma sai naga yazo wurin nuhu da yake lokacin duk gidan muna gado muke bandashi daya sai gidan kanshi bai zauna a ciki ba. Nan suka dade da nuhu suna magana kafin ya fito ya tafi ranshi a bace daga inda Alh nuhu yake tsaye yace munafuki dama nadade ina zargin ka a raina. Murmushi yayi yaci gaba da ba kotu labarin dashi ya sani Alkali yana rubutawa har aka sallamishi aka dawo kan wanan dan littafin da akai rubutu akai. Inda mahaifinamu ya rubuta idab na mutu a tuhumi nuhu gyade da Ali dcp aminina donshi yasan sirina ya fadawa nuhu komai. Ga inda ya tsara kaddarorin da yake dashi an karanta kowa yaji nan dai Alkali yace aje a rufe su Alh har haduwa na gaba kan zargin da ake masu din na kisan dan uwan su a shekarun daya gabata a baya. Kotu ta tashi na dade zaune ban motsa ba a inda nake ina jin wani iri a zuciyana kafin can in dago kaina.