Sashe 156
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nikan tunda na shige daki ban fito ba barcine ma ya daukeni don akwai gajiya a jikina dama ban gama warwarewa daga gajiyan dana kwaso a gidan ogan mu ba lokacin. Bana son shiga wurin aiki mu sai ranan monday don haka nayi zamana a gida ina hutawa kuma wayana a kashe don wanda ya kira yajishi kashe. Barci na samu nayi sosai natashi nayi sallah na gyara jikina don zan dan fita zuwa lasuwan kusa damu in sai muna kayan miya don yayi low sosai idan na fara fita aiki ba lokaci gareni kuma. Dogowar rigace dai har kasa a mutunce saidai zuwa kafadantace shakallo don idan zan sakata hakan sai dole dantsena sun fito a fili hakama gaban rigan irin mai nuna girman nonon mutum din nan ne a fili. Amma ni da nasaka sai nakawo yar cikin nan da ake yayi mai makuraren wuya da dogon hannu na saka daga ciki sai hakan ya bada kala mai ma,ana . Saidai ranan ban saka hijab ba son wata rana haka nakan fita sai hula a kaina hakan ba komai bane a wurin mu don dankwalin ne na daura kwai kamar daurin tura din ka yafashi kamar gyale a saman kan ki. Shagon umma na nufa na sameta da custermers gaidasu nayi na samu wuri na kai zaune ina kallon abinda zan kira akawo muna a shagon don na kwana biyu ban leka ba. Sallaman Felix mukaji a bakin shagon yana gaida umma da good day mah ta amsa mashi sai ya hangoni a cikin shagon zaune. Why d u swich up your phone today ? We de call u sinces morning we nerver reach u why now ? Oga don base with u today, true true ido kawai na zuba mai ina kallon shi kafin yace u no dey talk today ? Na dan mere baki ina fadin waiting i dey talk now call my phone nd it swich den ? U see na now now ogo live dis country travel to Dubai see d money he give us before he go ya fada yana taba aljihun shi don shi sarkin son barkwanci ne sosai idan ka saba dashi. Nace kun gode ina mikewa tare da fadin na market i de go now to buy some fresh vegetables and other tins . Ina kokarin fita daga cikin shagon umma din take fadin in sawo mata cheas idan na gani nace yes mah muka jera da Felix din zuwa wurin motan shi. Motan dake saukowa saman titin ne yana nufo inda muke muka tsaya muna kallo har ya iso ya tsaya muna ta magana daganin yanayin tsayin mu zaka gane mun san juna sosai da Felix din saidai hankali yana surin motan duk da na ciki bai fito ba a lokacin. Can ya sako kafa daya waje babu abinda nake gani sai bakin takalman maishi da bakin wando shi don sauran jikin shi na cikin mota a lokacin. Felix yai min sallama zai shiga motan shi ya tafi nima a lokacin nabar wurin zuwa motana dake parke a gefe na kwarai ke nan naji an ambaci sunana a bayana saidai kodana waigo naga mai maganan . Yar motana da bai taka kara ya karya ba shima yake kallo a cikin mamaki karara a fuskan shi nasan mamakin shi na dayan biyune bai wuce motar tawa bace ko na wani zan shiga dai ? Ya mustaphane a cikin shiga na suit a jikin shi bakake he look classique sai dai kyakyawan fuska yau a daure yake irin sanin farko da nayi mashi a baya. Na dan yi tsam wuri daya kafin na jingija jikina a motana don ganin yana takowa zuwa inda nake tsaye nakai hannu na zare dan glass din dake idona. Ya karaso a lokacin nima dai na gama daure nawa fuskan a gareshi kamar yadda shima nasa yake daure lokacin. Na dago kaina a hankali na dan kalleshi ina fadin ina wuni ya amsa yabi motan da kallo kafin ya juyo gareni yana fadin ina mama take na nuna mai shagon da hannu ba tare da nayi magana da bakina ba . I would like to see you now ya fada ya juya zuwa inda na nuna mashi umma din a cikin shago nabi bayan shi da kallon mamakin yadda yanayin shi yake yau nasan akwai matsala. Ban shiga ba sai kawao na shiga motana naja nabar wurin bakuma komai yasa nayi haka ba sai dan nasan idan daman ya wuce min ban shiga kasuwa ba zamu dan shiga cikin wani hali na yan kwanaki idan bamu da kayan girki da muke bukata. Hankalina kwance na sayo duk abinda nake da buka ban kuma wani dadeba na dawo gidan saidai ga mamaki har lokacin motar shi na nan a haraban gidan . Saidai wanan karon har umma bata shago suna ciki tare da ita yaran Abdulhamid ne suka tayani kwasan kayan zuwa ciki na shiga da sallamana a bakina. Zaune yake saman kujera kamar yadda itama umma din ke fuskanta shi suna hira akan sana, an ta . Amar ne ya mike da sauri ya karbi farin ledan dana shigo dashi a hannuna yana gaidani da dawo na amsa kitchen ya nufa da komai tare da yaran ciki suka barshi yana saka komai a inda ya dace a aje shi. Na fito ina sauri zan shige daki umma take fadin tun dazun yayan ku yazo yace kun hadu kince zakije ki dawo yana da magana damune. Kallo daya nayiwa inda yake ban iya maimaitawa saboda kwarjin da yai min don idon daya tsura min yaji me zance da umma din kan abinda ta fada. Au bansan ni yake son gani ba ai gani na fada a karshe tare da zagayowa na samu wuri na zauna shirune ya dan biyo falon kafin ya gyara murya yace umma zaso na danyiwa sahiba yan tambayoyine kadan don Allah ya kare magana yana kallon umma. Baida matsala yar uwakace ai zaka iya mata tambayan da kake son yi mata ba damuwa ga hakan don a zaton umma akan wani aiki zai tambayeni. Don Allah ina son ki fada min yadda kukayi da Abubakar modibbo a jiya da na barshi gidan nan wurin ku don ya sameni da wani zancen da yaban mamaki sosai yau din nan. Akan me zanyi zancen ka dashi tunda ban san komai a kanka ba na dai tare shi da fadi su daina zargin ka akan abinda bakai ka aikata ba suke zargin ka dashi. Kamar meke nan Sahiba kike nufi rana wata lokaci duk ban raga mashi komai ba saida na zaiyana mashi komai daya faru dashi bai iya magana ba bayan idon daya tsura min kawai yana kallona da saurarena. Sahiba waya fada maki wanan zancen ina rokon ki daki fada min gaskiya don na dade ina son sanin duk wani abinda kika lissafo min a yanzu. Nasani ne kawai yace hakan kuma bai taba yuyuwa dole wani ya sanar dake hakan na mike kawai nabar falon don yadda nake ji har cikin raina. Umma tace ka yada da hakan don baiwan da ubangiji yai mata ke nan a yanzu har idan kuma baka yarda da wanan ba zaka iya tambayanta wani abin na daban ka gani. Shiru yayi na dan lokaci kafin yace zan gwada don in kawar da zargin hakan a raina Amar umma ta tura ya kirani wani kallo da nayi mashi saida yaron ya firgita ya koma yana fadawa umma din a furgice. Me kake son tambayana a yanzu zancen kayan da kuka boye a cikin conteiner na Alh yayafi don kana ganin shine ke ma sherin haka. What ya fada ya mike tsaye yana fadin lalai umma na yarda don ba wanda yasan da nayi haka sai babban yarona na kasan waje gashi kuma sahiba ta fada yanzu. How come,s wanan ta koma haka yanzu yaushe wanan abin ya sameta haka mama ya sake tambaya yana fadin no warnder halinta keda wuyan sha,ani. Stop it aka daka mai tsawa ranan dai a takaice yaji tonon asiri na yan kungiyar su har da abinda bai taba zato duk na fallasa mai shi jikin shi ya dauki rawa sosai a gaban shi nasha wuya sosai don sai da umma ta shaka min wanan abin na samu kaina da kyat har magariba muna abu guda hankalin umma ya tashi sosai tayi data sanin faruwan hakan saida kyat suka lafa min na shiga wani irin barci mai nauyi. Sai washe gari na falka jikina a dake ko ina yana min ciwo muryan Abdulhamid naji a part din mu yana fadin idan mun shirya yana waje yana jiran mu. Abin duniya ya damu Nazifa gashi majaifiyarta ta hanata fadawa mahaifinta zancen ya daukan mata mataki akanta. Haka ta zauna tayi shiru bayan fitan shi tana tunane ita kaidai a katon falon nasu sai yayanta dake wasan su a gefen ta taji ana kwala sallama tun a waje. Duk da ta sheda muryan mahaifiyar nata saidai hakan bai sa ta yunkura zuwa taron ta ba don irin yanayin da take ciki a lokacin. Sallama ta kara daga murya tanayi da kyat ta iya amsa mata saidai ita hjy salma din muryan yaran da taji yasa ta nufi falon tana shiga ta hango yar nata zaune cikin wani hali na tashin hankali. Me zan gani haka nazifa me kike son mayar da kankine wai ko so kike dani dake mu koma abin dariya idan an kashe auren naki ne ? Hawaye ke zuba daga idanuwan ta tana fadin wallahi mama baki ga irin wullakancin da yayi min bane shiyasa kike ganin laifina. Ban gani ba kuma ba zan gani ba ke da idon ki da girman mu kina dai ganin irun wullakacin da mahaifin ki ke muna a gidan ku ai mun fita kowa muka fadawa hakan da yake muna. Ba hakkuri muke muna zama dashi ba wanda bai sani ba sai ya dauka wani dadin duniya muke kwasa a wurin shi. Gaban ku zai zagemu har iyayyen mu tas a gaban kowa zai dukemu da girman nan namu kuma kin sani ba baki sani bane. Mama baki dai son a fada ne kawai amma idan na zauna wanan dan iskan kasheni zaiyi don yaga ina son