← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 337

Sashe 16

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Zaune take tana lazumi saman sallaya bayan ta idar da sallah magariba wani kanshi ya ziyarci hancin ta ko ba a fada ba tasab kanahin turaren mijin sune wanan.
Shi din ne ya shigo dakin yana gyara agogon hanunun shi ya dan kalleta yana fadin aroka muna da yawa don Allah .
Ta dan dago kai ta sauke a kanshi tana dan murmushi tana fadin Allah dai ya karba muna wanan kamshin haka sai ina kuma haka ?
Ya dan bata rai kafin yace zanje gidan su wanan mara hankalin ne karima don mahaifita ya dameni da kira tun rana hjy Addah bata bata rai ba shima kuma din bai zaci hakan a gareta ba dama.
Shedab da yake mata na bata taba korafi akan karima din ba tun shigowan ta gidan shi ta zauna kuma a cikin su din a yanzu.
Sai cewan da tayi Alh kaima ai ba zaka biyewa mace irin karima kuna sayar da hali ba haka zama da wanda rayuwan shi san ba kwabo sai sannu a hankali zata shiryu ta gane gaskiya.
Amma irin wanan ina dadin sa ga yara a tsakanin ku, ace ka turata gida haka dolene hankalin mahaifanta ya tashi gaskiya.
Hmmm haka kike gani don ita ai bata da alaman nadama kan abinda tayi din ko dazun an fada min an ganta a by pass su biyu a cikin mota .
Da ace ta damu da hakan ne ai da ko idon fita bata gani ba a halin yanzu din tunda tasan akan shi muka samu matsala dani da ita.
To ai kaji na fada maka sai fa hakuri don yanzu wanda duk ya ganta matarka dai za a ce ba matar wani.
Sai na dawo yace da ita don baida amsan da zai iya bata a lokacin ya sakai ya fice daga dakin ya bar gidan zuwa amsa kiran dattijon dake neman shi din.
Yasamu ankai ruwa rana a tsakanin mahaifan ta din da suka samu sabani a gidan akan yar tasu.
Bayan gaisuwa a tsakanin su sai dan shiru ya biyo baya mahaifin hjy kariman ne ya fara magana yana fadin .
Alh mun san kayi hakkuri da halin yarinyar nan kuma kana kanyi har yanzu don ni kaina ba macen da zata kawo min wanan shegantakan in kyaleta ace mijin ki bainan kisa kafa ki fita ba tare da sanin miji ba.
Alh yace ni abinda ya ban haushi fitan karima baida lokaci duk sanda ta bushi iska fita takeyi tana bin abokan banza suna koya mata shedana.
Yanzu meye laifin hjy Addah a cikin wanan zancen da zata nemi ta zageta matar nan har idona ta faka ta kirata ta dawo gida na dawo.
Wai amma ita, ta dawo gidan tana zargi wai itace munafukanta kuma duk wanan abinda tayi mata din bata gani ba.
Daga can kofan daki inda mahaifiyan nata take zaune tace ai dama na fada maka malam karka da da karka kara akan uwargidan yace tazo gida.
Cikin mamaki Alh ya dago kai yana kallon mahaifiyar matar nasa da bata iya boye shigarwa yarta a fili ba haka.
Shikuma ma haifin na fadin saudatu mena fada maki tun kafin mu zauna wurin nan kikace kinji don haka karki kawo muna zancen ku na mata nan.
Yanzu dai hakkuri zamu baka Alh kayi hakkuri yarinyar nan ta koma dakin ta iidan kunne ya ji jiki ya tsira idan halin ta ne ta koma tunda haka taga matarka ta gida tanayi data shigo.
Nan dai mahaifin yai mata fada suka tattaro suka dawo gidan tare da ita inda suka samu mutanen gidan kaf din su a falo suna murnan zuwan yayan su daya dawo .
Amira tana zaune saman jikin shi cikin rashin damuwa da rashin uwar su a gidan sukai mata sannu da dawowa ta shige part din ta kai tsaye.
Alh ne ya shigo karshe bayan ya gama sallaman driver ya samu dan shi zo wanda suka dade basu hadu ba sai wanan karon daya shigo wanan aikin.
Na neman wanda suke zargi da aikata wani abu na daban sabanin wanda ni ya fada min din alokacin a baya daya fada min dalilin zuwan shi.
Da kyat Abubakar ya iya budan bakin yana fadin sannu da dawowa bai tsanmani amsawan ta ba don haka yana fadi ya kawar da kanshi ga kallonta kamar yadda itama ta kawar ranta na kara baci da ganin shi yazo.
Duk da yakan dan samu abinda ya bata idan yazo sai dai hakan bai mata dadi ita don tana rainawa ita tafi son ya bata daidai da na mahaifiyar shi.
Yaranta ne suka nufo ta da murna suna fadin mami ta dawo mami oyo jin muryan maigidan a falo yanawa dan nasa kirari da sarkin aiki ina ka fito office ina zaka aiki sai hakan kuma ya kara batawa hjy karima rai sosai don yadda yake nunawa diyan shi so a fili.
Sai kishi ya rufe mata ido take ganin ai nata yaran basu samun kulawan mahaifin nasu kamar yadda yake kula diyan hjy Addah.
Kishi ke nan duk halarcin hjy Adda da diyanta kishi ya rufewa hjy kariman ido bata ganin wanan halarci karshe ma sai take daukan hakan da kishi wai na munafunci suke nuna mata..
Saidai duk da hjy Addah tasan da hakan kuma abin yana damunta sosai a ranta saidai bata yarda ta biyewa halin ta sun zama daya ba.
Wanda hakan kuma ya kara haska ta ga mijin don hakkurin ta don shi mutum ne da yasan ya kamata.
Sabanin wasu mazajen da zasuga hakan duk da uwargida tana hakkuri sai kuma subi amarya a taru ana musguna mata.
Irin wanan ke uwar gida idan kinga hakan hakkurin ki zai jawo maki raini da koma baya abinda ya kamata kiyi na farko shine addu,a tare da sakawa kanki hakkuri akai.
Saidai kuma dole ki tanka din shiru wani lokaci yankan kawo raini ga uwargida don haka a rika dan magantawa a cikin hikima.
Chapter 16 · 0% Book details