Sashe 150
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
nasani mana ba mommy bane ta fada a lalace tare da fadin kidai ja masa kunne kuma ki kiyayye mommy na fada maki don ni yake aure ba ke ba . Tana fadin haka ta kashe wayan tabar mommy din tsaye da mamaki da al,ajabin yar nata kota manta da bayan uwar mijin ta take ita din kanwar mahaifinta ne ita. A haka yar ta Nabila tazo ta sameta tsaye tana mamakin ta ganin mommy a haka take tambayan ta mommy meya faru halan dawa kike waya ? Ta sake kallo yar nata da mamaki tana fadin barni Nabila yau kan naji abin mamaki a rayuwana duniyan nan waini Nazifa zata kira tana warning dina akan yayan ku. Har da fadin wai idan ni yake aure sai naci gaba da bashi abinci gidan nan yanaci what mommy nazifa din ta fadi haka . Yar abu kazan kazan nan wallahi bata kai yar iska ba tunda bata fadi a gaban yaya ba shigiya mai gadon iskanci kawai. Ta shiga zage zage a dakin hjy din tace da ita tayi shiru kada wani yaji wanan cin mutuncin ko nabila din sai bayan ta fada mata taga yadda take fadan tayi da ta sanin fada mata ko meye. Saiga hauwa ta shigo dakin ganin su hakan itama tambaya take wanaji kina zagine haka tun ina waje ? Bar yar iskan nan Nazifa wai waya ta bugowa mommy na kai nabila kinga halin kike wallahi yanzu kun fara wanan zancen ke nan a gidan nan har hjy karima taji zancen nan. Karshe ta kama yadawa a gari gari ya dauka kunsan halinta kuma sarai kan urin zancen nan. Wai meta fadane haka hauwa ta kara tambaya tana kallon nabila tace wai cewa tayi fa idan mommy na auren yayan mune ta sani jimon yar iska wace bata samu tarbiya a gidan su ba kawai. Kuma uban nan idan banje gidan nan na casa Nazifa shegiya nake don wallahi ban yarda da wanan cin fuskan haka na wullakanci. Kada ki soma wallahi dama nayi take nema ita da iyayyen ta ba wani aiki bane yanzu mahaifinta yace zai sabauta rayuwan mutum kan an taba mashi ya kun sani. Mommy sai a barta ta dinga yiwa mutane irin wanan iskancin nan tanaciwa mutane fuska ko yaushe . Tsawa mommy din ta dakawa hauwa din ta hauta da fada sai hauwa din ta tashi ta fita daga dakin ta mayar da kallonta wurin Nabilan tana fadin kinsan hauwa fa tafiku zafi meyasa kika fada matane wai ? Mommy zagin yayi muni dayawane wallahi amma barta idan ta kara wallahi bazamun kyaleta ba Allah ta mike ta fita hjy na nadaman fadawa yayan nata mata a lokacin. Don tasan diya mace dajin zafi da kishin mahaifiya idan an taba maka uwa yadda kake ji a zuciyar ka. Hauwa,u ko tana shiga dakin waya ta dako ta fara turawa Nazifa zagi ta uwa ta uba ta zage ta tas ta tura mata nabila na shigowa ta ganta da wayan take tambayan ta tace zagi na turawa yar banza taji inda dadi. Idan anyi magana sai mommy tace wai a kyaleta don ubanta ubanta shi Allah ne da za a ji tsoron shi ? Zaune take a cikin fushi da dan jin sanyin yadda tayiwa mommy din yau itama ko banza taji zafin da taji haka kawai zata batamasu shirun su bayan sun kashe kudi mai yawa su tafi a banza. Hauwa aida kin barta sai mun hadu ba zamu hadu da itaba watarana sai mu nuna mata ai mun sani musan kai komai. Wai anty tsoron ta akejine wai da zataci bulus ta zagi mommy a banza a kyaleta koshi yaya yaji bazai kyale wanan cin fuskan ba ai. Ba fa zai kyale ba ni don mommy ne kada tace ta hanemu saida muka tayar da zancen kuma tunda bata son anty taji. Taji mana ke barin fada maki nifa yanzu ban tsoron kowa wallahi duk wanda zaiji yaji ta zagi uwana na zagi uwarta da ubanta ba shike nan ba. Waike har da ubanta kika zaga dama nabila ta tambaya tace me zan tsaya jira da yar banza cewa nayi ita tsafi uwar ta tsafi ubanta tsafi. Kai hauwa baki da kyau wallahi kin mun daidai iyaka dai mommy tayi fushi shike nan ai. Ranan kan sai waya na bugawa ummana kan cewa a gidan zan kwana har hjy ta karba ta roki umma din da kanta don yadda na nuna mata din na damu. Don abinda ya faru ina fita tare da abokan aikina muga tafiyan hjy mansura sai hjy fatima din tace Sha,aban tell me inda ka samo yarinyar nan haka mai abin al,ajabi ? A wurin aikin mu take hjy nan dai ya basu dan labarna daya sani da irin taimakon da nayi mai a rayuwa yake fadin she is tellent in dat way. But a nan suna fadin wai jinnune a kanta eh sudin ne sune aike irin wanan aikin dama mostly ana samun su sosai acikin al,umma amma sai a mayar dasu abin wani tsoro ko mugaye kuma is natural habit din su suna gani sun sai mai zaifaru dakai. Aisha ce take fadin amma dai a nan zata kwana tare damu yayana yace ina fa ita kuma gidan su fa idan ta kwana nan din. Ai gaskiya Aisha ta fada gaskiya takwana damu a gidan nan yau don bazan iya kwana mu kadai a cikin gidan nan ba. But mommy ba gamu ba a gidan ga Felix i beg idan ba zaka iya rokonta ba ni zan roka ya kara bata fuska shi ta yaya zaice ta kwana dasu bayan babu kwana acikin aikin su. And beside mutanen nan suna da kokari sosai dashi kada fa hakan yazo ya jawo mata wani matsla ga yarinyan nan kan hakan. Ita da kanta tasa Felix ya kirani take fada min bukatan su a take na bata raina Allah ya gani ba zan iya kwana ba tare dasu umma ba. Sai naji tana fadin ummaki kike tsoro ko Sha,aban ya fada min komai ki kira mahaifiyar taki in fada mata da bakina please ki taimaka muna gobe da yamma zamu bar garin nan zuwa jos daga can zamu koma insha Allah. Wayan na dauko na fara kiran layin umma din ta dauka tana fadin a sahiba na kira dazun baki dauki wayan ba. Umma ina lafiya zaki dawone yanzu ta tambaya sai na mikawa hjy din waya don irin kallon da takeyi min lokacin har lokacin umma na min addu,a Allah ya dawo dani lafiya. Tace hjy ba yarki bace nice mahaifiyar ogan su da mukazo addua don Allah ina son ki ara maki yarki na yau don gobe zamu koma ta kwana a wurin mu ta taimaka muna da shiri. Kai kai hjy idan bake ba sam ba zan yarda da wanan ba yata marainiyace ban son wani abu yazo ya same ta a waje. Insha Allah ba abinda zai sameki lafiya zata dawo gareki insha Allah ba komai don Allah a rike min ita amma ta fada tana kashe wayan. Sai wayan shi yake dakila bai yarda ya dago kanshi ba kuma yana jin abinda duk akeyi a wayan. Sai yamma muka fita tare dasu sayayya sukayi sosai har ni na samu shiga an samo min kaya kusan duk abinda Aisha ta dauka a wurin zatace nima indauka. Muka dawo gidan bayan anyi sallah ne mukaci abinci dakin su muka kwana duka mu uku a tare ranan. Washegari tun safe ake shiri karfe ukku suka dauki hanyar airport tare damu bamu dawo ba saida jirgin su ya daga muka dawo muna dawowa kayana a hade suke na shirya sai gida ban tsaya bako na minti biyu don dama na kagu in tafi gida. Yana zaune sai kai yake kadawa daga zaunen yana kara nanata sakon Hauwa,u din a cikin wayan matar shi din dake tsaye a kanshi tana girgiza jiki don ranta ya gama baci sosai lokacin. Meya kawo wanan zancen haka ya kara tambaya yana kallon ta tace na fada ma cewa ban sanni ba jin haka yasa ya mike da sauri ya tare da jawo rigan shi ya saka ya fita katfe takwasa na dare.