Sashe 218
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wurin taron ya cika makil da yan kasan dama baki irin mu itako Aishat ganiya sai murna da farin ciki takeyi da zuwan yan uwa duk wanda ya taka a dalilin ta zata har kasa tasa gwiwa bibiyu tayima sanu da zywa irin na al,adan yarbawa don girmamawa. Wanan abin da naganine yasani sake yan kwala watau dai gata wani abune nace a raina wata kila yanzu da ace mahaifin mu yana raye muma zamu iya samun wanan gatan da Ganiyat ta samu. Ranan da na kare karatuna ko kaza bata biyoni ba balle dan mutum ni daya kwallin naje na dawo duk ko da nuna min kauna da wasu abokan karatuna keyi a lokacin gaskiya naga dabam a wurin saboda rashin kowa a tare dani. Ganiyat zata iya girme min da shekara biyu ko ukku gaskiya amma shirun ta ita yai yawa sosai da kuma ba mutum girma. Tunda muka gaisa da farko haba haba da ita mahaifiyar su da bakinta sukaja ta bata kara tako inda muke ba saidai tana daga muna hannu idan ta biyo ta wurun mu. Yemisi da muke zaune a tare kusa da juna naji tayi tsuki tare da fadin Olon magge yasa na juyo ina kallon ta naji tace what a stupid tin be dat as dis gurl come here ke bakiga yadda ta mutatuntamu ba da farko amma ina kallo Alaja ta fada mata wani abu game damu nasan ko a kanki ne tayi magana. Kaina kum na tambaya a cikin mamaki yes bake ke dating din danta ba dawa zatayi kuwa a daidai lokacin ya juyo yake fadin kinga waccan da suka shigo yanzu itace Alaja ke fada dake a kanta. A hankali na dago kaina zuwa duban inda su Alaja suke zaune wata matashiya nagani a tsaye suna gaisawa dasu kallo daya nayi mata na kawar da kaina gefe daya. Kamar sun san da hakan sai ga Aishat ganiyat, ta riko hannun ta a cikin murna zuwa inda muke zaune tana fadin brother meet mansurat . Ya dan dago kamar da mamaki a fuskan shi ya furta who is she a take naga tsarguwan kalamin shi a fuskanta kafin ganiyat tashiga mashi dan bayani da cewa ai ita din diyar kawar ummice dake Manchester. Oh sorry by the meet my Pierce Sahibat from Nigeria ya fada kai tsaye a wurin ba tare da jin komai ba ya dan gyaro wuyan rigan shi kafin ya daga hannu yana duban lokaci a agogon hannun nasa. Dan dukowa yayi kamar yana min rada yake fadin ki mike tsab mu bar wurin nan yanzu yau din nan zamu wuce zuwa Dubai da dare. Kaina gyada ina kakaro murmushin dole a fuska saidai daya san kiris nake a lokacin inyi cikin shi da masifa akan bata min suna da lokana danaga yana kokarin yi yanzu kaina don kawai wani plan nasa zaita nunani a matsayin piance din shi ceni. Wanda ni kadai nasan wanan karyane shirine tsakanin nida shi kawai amma kuma shirin nason ya suce wuri a yanzu na fada don kula da yadda yake son batawa mahaifiyan shi rai a bainan jama, a. Haka yasa na dan kallo Aishat Ganiya tare da bakuwan a cikin fara,a ina fadin kai sannu da zuwa fa kun biyo hanya mai nisa duk saboda Aishat Ganiya sannun ku da kokari Allah ya bar zumunci. Sai lokacin na danga murmushi a fuskokin su naci gaba da fadin ga dan uwan naku nan ina mikewa zamu taka zuwa wancan wurin mu mike kafan mu na dago tare da hannun yemisi da yanzu don dole muke shirin dole da ita sama sama. Wayan ta yai kara a daidai lokacin da take shirin tashi zuwa dakin ta har lokacin tana cike da mijin nata da jin haushin shi sosai kan zantukan daya fada mata daren jiya ta manta da cewa itace ta kawo mai zancen har ya bata amsan daya dace da abinda ta fada sai kuma ta dau zafi dashi. Number mahaifiyar ta tagani take mamaki tana dauka take fadin lafiya mama babu ko sallama mahaifiyat nata tace mijin ki ya fada maki sun dawo da Alh ko ? Abba ya dawo ta tambaya a cikin mamaki tare da fadin nidai yanzu naga ya shigo ya shige part din shi baicewa kowa komai ba. Waiko Nazifa kin san abinda kikeyi kuwa kinsan me ake nufi da aure to mama ya fita bai fada min inda zai tafi ba ya dawo sai nace mai me ? Tsuki uwar taja mai karfi tana fadin zaki shukawa kan ki tsiyane wata rana ji yadda su Alh gyade suke bada labarin yadda aka kai ruwa rana dashi sai da kyat da sanin koshi waye suka ba da bellin Alh yau. Nikan bai fada min ba son haka ban san yayi ba yanzu ina Abba din yake ta tambaya yana nan gida mana tare suka dawo dashi ai. Zan iya kiran shi yanzu ta tambayi uwar cikin nuna ta gaji da wayan lokaci ki kira din ko zai dauko yanzu dai ya shiga wanka don mutane sunyi yawa saida aka rufe gida ya samu ya huta. Barin bari sai gobe na kirashi kada ki soma don nasan halin ki da sakaci ko goben sai lokacin da kikaga daman tashi da barci zaki zo don haka ki gwada kiran shi a yanzu ko zai dauka. Tace zan gwada barin bada minti biyar nan gaba amma fa ina ganin tsiyan da mukayi da baban maryam ne a daren jiya yasa ya tafi yau din. Shirmen banza shirin tafiyan da sukeyi yau kwana hudu ke nan zakice wai kunyi tsiya dashi kan haka yasa kila yaje indai zaki gyara ki gyara don iskacin ki ba inda zai kaiki . Kallon wayan tayi bayan uwar ta kashe taja tsuki tana ajeshi a gefe daya kafin ta dan fada tunane na san lokaci tana nazari can ta kalli me aiki tana fadin haule ki kwashi yaran nan zuwa daki gani tafe yar aikin ta amsa da to hajiya. Dakin ta shigo a dai lokacin data sameshi ya zuba ruwan tea din daya dafo a kicin tana waya bata ji fitan shi ba har ya gama ya dawo dakin shi kuma ya tsunci wani abinda take fadi a lokacin daga inda yake. Yana tsaye daidai saitin window dakin dake bude iska na shigo mashi yana tsiyaya ruwan shayin tashigo da sallaman ciki ciki. Dan juyowa yayi ya kallota kafin ya mayar da kanshi ga abinda yakeyi a lokacin ta karaso tana fadin ashe tafiya kayi yau din baka sanar muna ba. Eh tafiya nayi lokacin dana fita baki tashi daga barci ba a lokacin OK ta fada tana kaiwa zaune can tace dashi kuma ashe anyi nasaran fito da Abba yau din ke nan. Eh anyi don munyi magana da wace ta tsare shi tace a sakoshi ya nemi kudin idan babu su ya biya company abinsu . Wai saima data saka baki ke nan ashe aka sako Abba din ta fada cikin mamaki yace eh dama ba abinsu ya taba ba. Shiru tayi tana binshi da kallo ganin cewa duk maganan da sukeyi bai juyo ya kalli inda take ba yake bata amsa. Mama ce ta bugo min take fada min cewa kaine kayi kokari har aka sakoshi din eh hakan ai rufin asirin kowane banyi don wani ko wata ba ni kaina nayiwa hakan ai. Bata kara tanka mashi ba sai nazarin da takeyi a cikin zuciyar ta kafin can ta nisa tana mikewa tace dashi saida safe Allah bamu alheri ya fada shima. Washe gari sai goma ta isa gidan nasu ta samu har mai aure abuja ta iso a lokacin duk suna falo tare da mahaifin su ta shigo falon kowa ya bita da kallo. Gaban mahaifin nasu taje ta gaidashi ya amsa take gaida shi tare da mai Allah ya kara tsare gaba ya amsa cikin rashin walwalan data sameshi a ciki . Wai Abba ita din waye dahar take da iko haka da zatace zata wullakantaka mu kyaleta haka kawai wata banza can tazo ta batawa mutane suna wani dan shi saurayi ke fadin haka. Shiru mahaifin yayi kamar baiji shiba ya share zancen dan nasa don koda ya dawo jiya duk yana cikin tashin hankali sosai matarshi ta biyune ta shigo tana fadin wai Alh Inusa suna falon ka na baki suna jiran ka. Sun iso ke nan ya fada yana kokarin mikewa da sauri nan ya fice yabar yaran nasa a cikin damuwa suka fara mikewa zuwa cikin gida inda uwayen su suke. Mommy ne tashigo falon daddy din da sallama ya amsa mata tana binshi da kallo don taga yana shirin fita haka da sassafe kuma hakan ba dabian shi bane sai idan wani abu ya faru yake fitan safe haka a cikin garin. Ina kwana tayi mai ya amsa don irin kallon mamakin daya kula tana mai yasa yace gida Nuhu zamu don ya dawo jiya cikin dare akace. Wallahi nima hjy salma takirani tana fada min har na kirashi mun gaisa dashi tun jiya din yace OK yanzu ni zan tafi can din. Ya kafa hula akanshi ya dauki waya yana mata sai ya dawo tayi mai Allah ya tsare a tare suka fito daga falon don bata ko zauna ba ya fita. Tana komawa part din ta yaranta ne a zaune falon ta samu wuri ta zauna kallon su tayi don ta fahinci akwai maganan da sukeyi suka ganta suka shiru. Daddy bai tashi bane Nabila ta fada ya tashi mana ya dai fitane zuwa gaida yaya Nuhu daya dawo jiya. Au yadawo ashe ya dawo jiya ance yayan kune yaje ya fito dashi wai dama jiya yanzo nan da safe yana sallaman mu zasu tafi wurin shi. Mommy wai kinji kuma hauwa ta fada sai sauran suka kalleta da sauri me akayi mommy din ta tambaye ta ? Wai aahe Sufynu yana shaye shayene da gaske yaba baby kashi har ta dawo gida jiya saida wanan yar ta anty tazo ta mayar da ita. Subbahanallahi mommy ta fada da sauri har da duka tace wallahi wai ya farfasa mata jiki ya korata kai Allah ya kyauta har yaushe akai aure da haka ya fara biyowa baya ? A