← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 223 OF 337

Sashe 223

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranan nasan anci gaba sosai a hanyar kasuwanci son komai yanzu a zamanance akeyi shi kamar yadda muke dan kwatantawa dai a Nageria saidai gaskiya a can su kan aun muna fincin kau ma,ana an barmu a baya dai. Mun fito dakin taron na karaw juna ilimi a cikin farin ciki da kwanciyan hankali sai faman binsu a baya nakeyi duk jikina ya mutu da abinda na gani . Sai yaushe mu Nigeria zamuci gaba koda rabin haka abinda nayi ta tunane ke nan har muka fito gashi wurin dai matasa ne masu dan matsakaicin shekaru don tsofi daga ciki basu da yawa sosai. Waya na hngoshi yanayi can dan nisa damu sosai kafin ya tako zuwa inda muke tsaye din suka fara magana da jimoh a cikin yarbancin da idan yanayi zakace wani yaren yakeyi ba yaroba ba. Adanan ne yayi magana daga bayana yasa na juyo ona kallon shi yake fadin ya dai yan mata kingani tun a ciki nake ganin alaman hakan a tare dake. No ba komai tunanen gida kawai nakeyi don ban taba tafiya ba irin haka ba tare da mahaifiyana ba. Suma din basu taba zuwa wani wuri nisa dani ba sai wanan karon nan dai ya dan taba min hira har na sake muna wurin har suka kare tataunawan da sukeyi suka tako a tare inda muke tsaye nidashi. Sun karaso boda jimo ke fadin yawa Adnan sai kazo mu tafi tare dakai ita Sahiba zata wuce tare da Oga daga nan zasu wuce wani waje suyi signing. Sam ban kawo komai a raina ba tunda aiki muka fito a lokacin dukkan mu baya muka shiga don naso shiga gaba tare da driver da zai jamu ya dan daka min tsawa a cikin yarbanci da kada in bashi kunya mana wanan fa driver ne aikin sa yakeyi. Dole na dawo baya tun zaman a motan ban dago kaina na kalli inda yake zaunw din ba shi ga kuma motan a hankali yake tafiya saman lafuyayyen titin dake shimfida a kasa ko ina na garin tsab yake sukan gaskiya sunci gaba ga komai na zamani sosai sun barmu a baya. Eh mun je wani waje muyi signing ashe kayan da za,a shigo mai dasu wa yan nan company din da mukayi aikine a kaduna da kano zai kara farfado da wurin kuma sosai har yafi da can baya dayayi shi. Daga nan zuwa karfe hudu da rabi muka bar wajen duk da agajeye muke hakan baisa mun nufi masauki ba don a kasalance naji yana fadawa driver inda zai kaimu kuma. Kai Dubai kan taci gaba wani irin kantine na sayar da kaya tufafi da sauran abubuwa muka ziyarta tare dashi a zatona na dauka nan ma wani abin yazo yi sai da muka shigane na gane ba komai yazo yi ba a wurin don abinda naji yana fada da muka shiga ciki. Zaki iya yin tsaraban komai da kike so a nan don ba lalai bane ki kara shigowa wanan wuri nasan ba zasu iya shigowa nan dake ba indan kun fito tare. Na rasa me zan fada mai a lokacin don lissafi ya kwance min ba zan iya yin komai ba don kaina lokacin naji ya kara fadin har mama da brother din ki ki saya masu kayan wurin nan zaifi. Tsaye nayi kawai ina kallon shi ban iya cewa dashi komai ba OK idan baki san me zaki dauka ba muje na tayaki kada mu bata lokaci don gobe nake son in bar kasan nan zuwa Cairo. Lokacin ne na iya dago kai na kalleshi ido da ido ina mamakin jin abinda ya fada ke nan har mu zamu bar kasan ke nan yake nufi ko me oho ? Kamar yasan me nake tunane naga ya fara tafiya yana fadin gobe zan koma Cairo zan barku a nan ku karasa hutun ku ranan tuesday zaku koma Nigeria. A daidai lokacin da ya isa wurin kayan maza yake wanan maganan nan ya fara duba saidai hankalina baikai kan irin da naga yana zaba ba a wurin. Yana jefawa cikin wani dan keken da muka sama a gefen wurin sai jidan kayan yakeyi kafin ya tura kekan zuwa wani bangare kuma da alama dai yasan kan shagon sosai nake gani. Ina biye dashi a baya kamar zonbi da wata da muka sama wajen ma,aikaciyar wurin yake magana ta dan juyo ta kalle ni kafin ta fara zabo kaya tana jefawa a cikin basket din muna binta a baya can dai takai ga daga wani tana gwada tsayin shi a jikina saidai bana jin yaren da takeyine. Wani irin mahaukacin sayayya yayi a wurin abin har ya ban tsoro amma kuma sai nasa a zuciyana cewa wanda zamu kara zubawa a shagon mune na lagos lokacin. Don haka naye tsaye duk inda mukaje ina binshi a baya har muka kusan gamawa sai riga daya na iya zaba a wurin saboda tsadan kayan dana gani a rubuce. Muka fito zuwa wurin biya ya basu card dinshi aka cire kudin nan sukai packed xin su aka kai muna a motan da mukazo da ita bamu muka isa masaukin mu ba sai tara na dare a gajiye naga an iso masaukin namu. Tunda moton ya tsaye yake fadin karfe bakawai na safe zan bar garin nan ba lalai bane mu sake haduwa daku nan din don haka ku kula da kanku har lokacin tafiyan ku yazo. Zaku zauna tare da Alaja a nan din don sai kun tafi kun barsu idan na dawo zamu wuce gida tare dasu lokacin sun gama hutun su da zasuyi. Sai kuma ya dan juyo ya kalleni sosai yana fadin nagode da kokarin komai da kikai min Sahiba wani iri naji a raina na dago kai na dan kalleshi ina fadin. Ba sai ka gode min ba ni ya kamata na godema ga irin kokarin da kake muna a rayuwa da badon kai daka tsaya min ba har rayuwana dana mahaifiyana ya inganta a yanzu da bamu san inda rayuwan mu zai kasance a yanzu ba. Wani irin lumshe idanun shi yayi lokaci guda sai kawai naga ya yunkura zai fita daga motan tare da fadin is OK nasan pain din ku a yanzu take care daga haka ya rigani fitowa a motan. Nima na fito tsayawa yayi yana saita kanshi kafin ya daga kai ya kalli saman benen dake gaban mu na dakunan kwanan bakin hotel din. Naga ya juya yana magana da driver daya dauko mu din a cikin larabci lokacin ne kuma muka jera zuwa ciki inda zamu kai dakunan kwanan mu. Alaja da yar ta dake tsaye saman suna kallon dawowam mu suka kalli juna suka tabe baki suna jiran hawowan shi saman na karasa inda masaukina yake na shige ciki. Ban san ya akayi aka shigo da wanan kayan da muka sayo ba dakina nidai na fito wanka danaje don yin alwala na samu an shigo min dasu a dakin. Da mamakin hakan na tayar da sallah ina gamawa a lokacin abincina yana ajiye naci sai barci ranan ban ko tsaya duba sakon wayana ba don gajiya. Har naso makara gayin sallah washe gari don a gurguje na fada ban daki nayo alwala na fito sai da na idar ne na fara tuna ko yanzu ya wuce a lokacin na dubi wayana karfe takwas saura yan mintina. Idona na lumshe ina tunanen abubuwa da dama a raina kafin na girgiza kai a hankali na dan jingina jikina da bangon dake kusa dani na dakin. Zubur na mike ina bude idona daga rufen da suke na daga na nufi wurin kayan da na gani a dakin ko an kwashe na samu kayan suna nan a inda suke ajiye har lokacin. Binsu nayi da kallon mamaki tare da tuna irin makudan kudin da ya kashe wurin sayen kayan don irin kudin da naga an rubuta a jikin kayan. A lokacin idona yakai saman takardan dake makale a gefen kayan na dauko da sauri ina karantawa a hankali na koma baya kadan daga wurin na kai zaune. Ban dago ba ina wurin cikin zurfin tunane yanzu duk ni ya sayawa wanan kayan ashe dama kayane fa da aka kashe kudi masu yawa wurun sayan su don ni na dauka ma a shagon mu nacan zamu saka. Tunane nayi to ni yanzu wani irin godiya ma zanwa wanatn mutumin ne wai na dade a zaune ina tunane gashi bama zan iya cewa ga irin kayan dake cikin packed din ba lokacin. Tun ina dan tunane har na fara gyangyadi a wurin haka yasa na mike na koma na kwanta barci nayi sosai a ranan ga abokan tafiyana suna son ganina gashi ba layin kasan a wurina. Saida nayi barcina na gaji sannan na tashi nayi wanka sai lokacin na nemi abinci na danna masu kan a kawo min abinci a dakina. Bayan naci na koshine na kara watsa ruwa a jikina na zauna a gaban mirrow ina kallon kaina a ciki yadda naga sauyi sosai a jikina. Fatana yayi wani lub lub dashi a yanzu tankar dai dama can a cikin daula na taso ban taba wahala ba a baya. Ashe ko wani jikin dan adam hutu yake son samu dan lokaci kankani zakaga fata ya murje saboda samun hutu da haka harna shirya a cikin wani dogon riga baki mai laushi mara hannu saidai rigan dinkishi har kasa ya sauka min xinkin wani mai shara shara dashi haka ta kasa na dan dira bakin gyale a kaina dake daure ba kitso. Wanda duk da rashin kitso bai hanashi cikowa ba a lokacin don mai masu kyau da nake amfani dashi a kaina din. Dakin yemisi na nufa don mu gaisa don tun shekaran jiya rabon da muga juna nan na samu bata nan don nayi nocking ba bude ba yasa na juya don komawa nawa dakin. Amma kuma sai naji na gaji da zaman dakin ina bukatan in dan zaga cikin wurin in mike kafana na mike don fita haraban wajen. Karaf muka hade da Ganiyat data fito itama daga nasu part din a cikin wani irin shigan da bai dace ba ace tayi shi don kawai tana a wurin da ba garin su ko kasanta ba don na
Chapter 223 · 0% Book details