← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 319 OF 337

Sashe 319

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barci nayi sosai a ranan tun abin safe sai bayan karfe biyun rana dana tashi don saboda yin sallah a lokacin sauka nayi daga kan gadon zuwa bandaki na kewa da niyar na watsa dan ruwa a jikina kawai na fito. Tunda nasan bana sallah don irin jin dana zubar a daren jiya din daga jikina wanda haka na kwana yana zuba min duk da nasan ba lokacin period dina bane a lokacin. Saidai me gani nayi kamar da daids duniya bani bace nayi wanan jinin haka a daren na jiya din don babushi ba alaman shi sam. Sanan kuma babu wanan ciwon mara din daya hanani shakat a daren don ji nake tankar marana zai ballene lokacin don ciwon da yakeyi din. Amma yanzu sam babu shi babu alaman shi a gareni tankar a duniya banice a daren jiyan face face a cikin jini ba. Dole haka na daure cike da mamaki nayi wanka a dadafe zuciyana cike da mamakin ganin hakan a gareni din. Sallah fatima ta shigo ta samu ina yi taja tayi turus a cikin mamaki tana kallona har zuwa idarwana data kasa hakkuri tace yaya akai hakane anty tana kallona. Dan murmushin yake na sake a fuskana kafin nace mata nima dai hakan na gani yanzu nake mamaki don ba alaman wanan matsalan a tare dani kuma yanzu ya dauke kamar banyi ba. Zaune takai a cikin mamaki tana kallona kafinta nisa tana fadin na kawo maki abinci a nan ne kici ? Don uncle tunda ya fita dazun har yanzu bai shigo ba shima abincin dai is ready nasan zaku so don fried rice ne with Chick meat muka hada. Ke dawa na dago na tambaye ta ina kallon fuskanta tace wanan matar ta jiyace ta dawo yau ma tare mukayi aikin da ita yauma. Fuska na bata lokaci guda don jin hakan data fada don ni sam yanzu ban yarda da kowa ba a wanan garin kuma haka zuciyana ya fara nuna min. Wani abune ga hakan anty ta tambayeni tana kallon fuskana cikin sonta san komeye ya bata min rai a lokacin. Nace a dan kasalance no ba komai zan fito na bata amsa ta mike ta fita a take zuciyana ya fara kawo min wani tuhuma nayi saurin kawar da zancen a raina lokaci guda. Na dan jima ban fito daga dakin ba saida nayi sallah la,asar nafito a falo fatimace zaune ita kadai tana kallo lokacin dana fito din. Da sauri ta dan yunkura tare da dagowa daga kwancen tana fadin kin fito anty nace ehh fatika sannu da hutawa dan dariya tayi kafin tace ga abinci can a dinning table an gama zanci amma ba yanzu ba na fada. Hira mukayi sosai lokacin da ita wanda hiran ya shafi hiran gidan sune da yadda suke zama dasu anty Nabila sai banji dadin yadda take ban labarin ba a lokacin. A takaice dai na fahinci cewa akwai wanan akidar ta zama dan uba a tsakanin su wai me wanan halin yake nufi na yan uba ? Shine fa ya jawowa Abban mu rasa rai har saida yan uba sukaga sun rabashi da duniya ga baki daya saboda wani dalilin shirme nasu can akan dan uwa. Shin a ko wani kabila akwai wanan halin yan ubancin ne da ake samu a yawancin gidaje ko dai sai a fulanin mu kawai ? Dole in bincika in gano idan wanan halin a ko wani kabila akwaishi har ko idan hakane kowani kabila har haka suke to lalai kuwa ina da aiki a gaba kan irin mutanen dana shigo cikin su yanzu. Gabana ne ya fadi sosai lokaci guda don tunawa da nayi da wani abu, lokacin daya wanda ya shafi rayuwata dana yan uwana. Mikewa nayi zubur zuwa kitchen yayin da fatima tani da kallo kitchen din naje na samu matar tana aikinta tukuru kamar yadda ko wace mai aiki takeyi a gidan aikinta. Na dan dade tsaye a bayan ta ina nazarin ta alaman motsin mutum taji a bayanta yasa ta juyo da sauri lokaci guda. Dan razana tayi kafin ta kakaro murmushi a fuskanta tana gaidani na amsa saboda kusan itama naji ba hausane sosai a bakinta ba lokacin. Juyawa nayi na koma falon don ban samu abinda nake nema a wurinta ba lokacin fatima ta fara fadin lafiya dai anty ? Lafiya na dai mike kafatane da yai min nauyi a yanzu sai naga tayi murmushi tana fadin aida kina iyawa sai mu fita waje zuwa garden don a kwai garden babba a wajen gidan nan. Ba matsala muje mana na bata amsa ta mike tsaye muka fice tana min jagora ita data san kan gidan a lokacin. Wurin yana da kyau sosai da tsari ga kujerun roba masu kyau gefe gefen na wajen a jiye muka dan fara zagawa muna hiran yanayin wurin dana gane da kuma yanayin weather din garin. Shine muka hango a tsaye daga kofan baya ta inda muka fito din ya tsaya yana kallon mu a cikin mamaki kafin ya fara takowa a cikin mamakin ganin yanayina a lokacin. Muma juyowa mukayi muka nufi inda yake sai muka hade dashi har lokacin ya na a cikin mamakin ganin yanayi na ban mamaki don fuskanshi yanuna hakan kafin ya fara fadin. Sahiba kinji saukine har kin samu fitowa waje ina can ina tunanen irin halin yanayin dana barki a ciki kafin in fita. Anty kan taji sauki ai uncle don har sallah tayi dazun don nima abin mamaki ya bani wallahi ni har tsoro ta bani wanan abin haka da ban mamaki yake kamar ba ita bace jiya gwanin ban tausayi muka kwana da ita ba. Sallah ya fada a cikin mamaki tare da kallona yana fadin how about the blood ya daina zuwane kuma ko a yanzu ko me ya kara dan kura min ido a cikin mamaki. Ya daina ne ai tunda har tayi sallah fatima na magana kamar wata babban mace da tasan ta kan duniya din nan kamar zaiyi magana sai kuma ya koma fadin. Muna can munje wani waje amma hankalina yana nan tun dazun ashe Alhamdullahi sauki ya samu masha Allah. Dan sunkuyawa nayi irin yadda yarbawan zamani keba na gaba dasu girma a yanzu cikin stly ina fadin you're welcome . Thank you ya fada a sanyayye yana mai dan sake fuska da nuna wani yanayi har lokacin a fuskanshi dana kasa ganewa. Uncle Bataci abinci ba tana jiran ka tun dazun nayi mata tayin abinci tace ba yanzu ba nasan kai take jira ka dawo kuci tare fatima ta fada a cikin zolaya ya kallo inda nakw da wani mamaki a fuskanshi ya kalloni a inda nake tsaye yana fadin. Ba kici abinci ba kina jirana madam ya fada cikin mamaki tare da kara karasowa gab da inda ni nake tsaye cikin mutuwan jiki? Har lokacin idon shi na kaina ya sake fadin keda kika kwana baki da lafiya haka don kawai naga kin samu barcine sosai da safe yasa bamu tafi asibiti dake ba a yau. Yanzun ma na dawone naga yanayin ki idan zamu tafi mu samu wani likita a nan ya duba min ke da wanan niyar na dawo yanzu don naji tsoron yanayin dana ganki ciki jiya din. Na samu lafiya na bashi amsa ina dukar da kaina kasa don haka basai mun tafi asibiti ba nagode daga haka na juya na nufi cikin gidan na barsu tsaye suna min kallon mamaki a wurin. Nima naji tsoro kwarai amma kuma sai naga ita bata damu ba wata kila dai mutanen tane sukazo mata da wanan yanayin haka. Don gashi kamar ba abinda ya faru da ita yanayinta ya nuna fatima ta fadi hakan tana kallon shi bai furta komai ba sai kai daya girgiza kawai yabi bayana itama ta shigo zuwa falon gidan. Bai fita ba saida akai magariba ya tafi samujn jam,i a cikin jama,a muma sallah mukayi normal kuma nake har lokacin bayan ya dawone daga sallah muka zauna mukaci abincin dare tare. A wanan lokacin ne mai aikin nan tace zata tafi gida alheri nayi mata tare da umartan ta tafi da sauran abinci abawa mubukata kada ya kwana ya lalace a nan din. Tayi godiya ta tafi sai bayan fitan ta yake fadin a ina muka samo wanan matarne nace hjy ce ta turo muna ita ai. Dan shiru yayi kamar me nazari kafin yace well tunda hjyce a barta amma ni nafi son a samu namiji da zaifi koda a bangarekune . No banda ra,ayin me aiki sam a rayuwana don wanan din ma banga matsala a wurinta bane kuma tana da tsabata da kula yadda ya kamata. Don bakin mu da baifi na mutum goma zan iya girka muna abinci ai a kullun na fada sai ya kalloni da sauri yace No ba zakiyi girki ba sam wanan din ma da kikayi a yanzu na barkine don in dandana hannun ki naji kalar girki a yanzu ai . Meye amfanin dukiyana iyalina basu huta ba koda yaushe nafi son naga iyalina suna hutu suna jin dadi nima na zo garesu na sauke gajiyana a wurin su ya karasa yana min murmushi a fuskanshi. Sam ban fahinci me maganan shi ke nufi ba don haka ban dauketa da wani muhinmanci ba shima din kuma ya gane hakan gareni sai ya share zancen bai fita mun dan taba hira. Daya shafi mahaifina yadda suka hadu dashi har ya zama yaron shi saidai hiran bai kai ko ina ba don dan kukan dana fara a cikin kunan rai da jin daci a zuciya. Haka yasa shima jikin shi yai sanyi bai iya karasa min labarin ba ya barni sai kuma ya dauki waya daga wata kasa yana amsawa shine ya tayar damu a wurin na mike zuwa dakina. Lafiya kalau na kwana a ranan shima ganin banda lafiya yasa bai nemini ba ya share yadai leko dakin ina barci haka yasa ya gane ni kadai ke kwana a dakin ba tare da fatima ba. Washe gari bayan mun karya yake fadin karfe hudu in shirya zamu tafi gidan hjyn shi tare da hjy falmata dukkan mu ukun zamu hadu a can. Sam banji komai ba a raina sai cewa kawai nayi
Chapter 319 · 0% Book details