← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 337

Sashe 87

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan yanzu da watani da faruwan haka . Shima dai din yaso kaduwa saidai a can kasan zuciyar shi saboda iya duniya da yayi wajen mu,amula da mutane ya nuna bai taba ganin fuskan ba ko sanina. Duk abinda ke faruwa ba wanda ya nuna yasan da haka a wurin in ka debe mutum biyu da suka gwane da aikin su na jami,an tsaro a lokacin. Yadda ya nuna min din yasa na gane ko bai ganeni ba ko kuma kuma wani abu dai amma yana da wuya yace bai shedani ba a yanzu gaskiya. Da sauri na bar wirin gabana yana faduwa don nayi bala,in kaduwa da ganin dan hayan gidan hanyan mu daya zauna na yan kwanaki a ikko s gidan daya damu yanzu a gaban daddy din. Muka bar wurin sai gasu kuma har yaya Abubakar din sunzo wurin event din matar shi sai wani jiji dashi matar shikeyi a wurin har akayi taron aka watse haka kawai na tsunci kaina da boyewa ina Allah Allah in dawo gida in fadawa umma gamon da nayi a ranan. Daga can nisa kadan damu suke zaune don a cakude ake a wurin maza da mata ana ciye ciye saman table din kowa da irin zancen da sukeyi a wurin su. Ya hango ni zaune na rungume hannayena saman kirjina kamar ina tunane kafin in juya ina magana da Fa,iza dake gefena. Har lokacin mamaki da tamtama yakeyi na ganina kuma a gidan su tare da yan uwan shi na kusa kuma alama ya nuna cewa sun saba dani a gidan. To udan nice yaya akayi nazo gidan su ga guma mun saje da yan uwan su mata don zubin mu daya dasu wurin kama saidai ni ina da haske da tsayi fiye dasu. Kai anya ba kama bane yake gani a hakan to ga wanan din ma da turanci ai yaji uncle yayi mata magana a yanzu a fili ya furta how comes haka ya faru ya dan kira yaron shi yana masa rada ya duba ya ganni a zaune yadda nake ina faman tunanen da nakeyi a lokacin. Duk da taron yayi kyau amarya da angon ta sun sha kyau sunji kayan alfarma a jikin su kowa ya yaba da hakan sai fadi ake an nuna hali a wurin sha,anin bukin gaskiya ba bangaren amarya ba bana angon ba kowa ba a barshi a baya ba . Amma ni duk wanan bai burgeni ba kwatsam naji wai ana kiran sahiban lagos da mansurat ibadan, da idayat da kubura illorin su fito su nuna farin cikin su a wajen nan MC yana ta faman nanata hakan . Atake ya furta impossible a fili how comes wanan yarinyar tazo nan kuma ? Kidan yarbawane ya fara tashi a wajen a daidai lokacin da nake fadin emmi ina karkada hanayena sai Nabila ta taso a fusace ta rada min idan ni yar gida banyi ba ai sauran ba zasu yi har bukin ya kawatu. Tana wucewa na fara takowa daga inda nake lokacin da kowa ya baza ido yaga su waye ake kira a filin yan kudu da suka. Nasan yadda rawan su yake tafiya da kidan don haka nake bin wakan ina juyawa a hankali suma sauran ukun suka fito da irin rawan dukan muna da ankon a jikin mu da suke kira da dinkin kabilu na zaba akai min sai gashi, duk dinkin dana sa sai ya zarta na sauran manyan yan matan masu ji da kai a wurin taron sai bina suke da kallo yadda dinkin ya dane jikina. Holl din ya dauki ihu don rawan da mukeyi din fuskana a daure nake rawa, dama rawa kan ai ya kare a wurin yarbawa don haka mukayi yadda suke rawa suna dukawa har kasa . Nan aka shiga muna mannin kudi daga abokan ango yan uwa da abokan arziki wasu suka fito suka tayamu rawan har da iyayyen su kubura din suna manni suna rawa don su a ganin su an karrama masu yaran sune a wurin. Kidan ya kare muka fito mc nayi muna godiya na nufi wurin da nabar su fa,iza a zaune na same su na zauna suka shiga min dariya wai ashe na iya rawa haka shine basu sani ba . Na danyi murmushi da shine halina sai dimple dina ya dan lutsa ina dariya dago kan da zanyi sai a table din su yaya Abubakar da yake min wani kallo mai kama da harara nayi saurin kawar da kaina gefen da suke din . Sai idona kuma ya sauka kan wanan bakon da ban san matsayin shi ba a gun su daddy tunda tare na gansu. Ni da kaina na tsawala da zama a wajen taron, na mike tsaye kamar zan tafi wani wuri na faki idon mutane na nufi kofan fita daga hall din taron ko zan samu idon sani ya kaini gida duk da dare ne a lokaci don indan ta nice zan iya bin duhun dare in kai kaina gida a wanan lokacin ba don fadan mommy da zatayi min ba. Don Allah kadai yasan iya inda na taka da kafa a cikin garin lagos kan talla dan neman abinda zamuci wa cikin mu nida dan uwana da mahaifiyamu. Zama nayi saman wani dankalin dake kofan shiga wurin taron ina bin mutanen dake shige da fice a wurin ko zanga idon sani da zai kaini gida . Duk da naji mutum ya zauna a kusa dani hakan baisa na dago kaina ba tunda nasan wurin taro ne muke dole akwai mutane da yawa a wurin dake cikin irin yanayina. Saida muka kwashi kamar second goma a hakan naji ance dani how comes you come to kaduna ? Na dago kaina da sauri na dan kalli gefena koda wani maishi ke magana banga kowa da yake magana dashi ba dama kuma ba sake murya yake kamar sauran mutane bashi. Nan ma din kanshi a duke yake kafin ya dago ya kalleni ido da ido gabana ya fadi rass tabas shi din daine a zaune a kusa da inda nake zaune daga gefena na kara juyawa naga wa yan nan yaran nasa dana san shi dasu a baya dan nisa dashi kadan suna tsaye kamar suna gadin shi. Bakiji tambayan da nayi maki bane ya fada a tsawace na dan kadu da tsawan da yayi min din sai na mike tsaye yace don't try that, or my guys take u out, of dis place now. Tsoro ya kara kamani don nasan zasu iya min abinda ya fada din saidai a irin karfin halina ban nuna hakan ba a fili nace dashi shabi u no me before ? Sai ranan nasan shi mutum ne don karfin halina daya bashi dariya a lokacin yasa shi dan murmushi mai sauti har ina jin sa mikewa yayi kafin yace. Well if u continue to pretend like u don no me before is good for u, and if you tell any body in this town about me. That i am d guy living in ur compound for some days, i will cut that ur yeye tongue, ya watso min wani kallo ya fara tafiya sauran suka bi bayan shi da sauri kamar walkiya suka shige motar su na bisu da kallo. Sahiba what are u doing outside muryan yaya Abubakar ne a bayana ya fadi hakan a cikin tsawa na juyo da sauri cikin dan kaduwa don na firgita tunda a tsorace nake lokacin. Duban hanyar da suka bi nayi kafin na kara juyowa gareshi ina fadi a cikin i,iniya da cewa i just come out to have some fresh air. If u are tiered, call some one to take u home, why are you staying here u alone ? Sai kuma naga ya fara dan dube dube kamar yana neman wani ashe tare da matarshi suke tafe ta tsaya magana da wasu yan uwan su a baya sai gata tana fadin honey na barka kana jiran, , , , Sai ta kasa karasa abinda zata fada din don maganan ya makale mata a daidai lokacin da ta gani tsaye dashi muna magana . Idan gida zaki sai mu sauke ki don gida zamu koma yanzu ya fada da sauri nace zan tafi nabi bayan su ina baya zaune shida ita suna gaba. Ya ciro waya a cikin aljihun shi yana neman layi kafin ya gyara zaman ear pods din shi yana fadin hello Nabila idan zaku gida kada ku nemi sahiba gata nan a tare damu zamu koma gida. Sai lokacin na gyara zama da dan kyau ya kashe wayan ya kada gaban motan yana fadin kada suje suna neman ki idan angama event din basu ganki ba hankalin su ya tashi. Dan tsuki Nazifa tayi tana kawar da kai gefe ya kallota ta sai ta dan wayance da fadawa saman kafadan shi tana fadin wallahi duk na gaji yace idan mun isa sai ki kwanta mana. Bai kaimu gida direct ba saida ya tsaya a wani wajen ya shiga ya barmu a motan waya Nazifa ta fara yi aka dauka take fadin mufa mun tafi gida meshi ta tambaya tace wallahi mun tafi me zamu tsaya jira mukan da auren mu bamu gama amarcin mu ba. Tace Allah gamu wata yar iskan kalan dagi nasu nason ai ta kwabsa muna wallahi sai nayi maganin yar iskan yarinyar nan idan bata fita min a ido ba kan mijina. Wallahi fa itace ta sake fada ko meshi ta tambaya a ina suka hadu dani take fadin ba yar bariki bane ki duba fa yar nan dufa bata fi sakina ba a shekaru har ta iya son maza haka. Bari zan kiraki idan mun isa ta fada da ta hangoshi daidai zai karaso inda ya aje motar shi din, damu a cikin ta muna jiran shi. Ledoji ne guda biyu ya shigo dashi motan yana zama ya juyo ya miko min guda a baya inda nake zaune take dis ya fada ita kuma ya mika mata daya. Naji tace dashi ka aje nan mana ya dan kalleta kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru baice komai ba ya tayar da motan muka tafi. Har suka kawoni kofan gidan daddy ba wanda yayi min magana a cikin su na sauka
Chapter 87 · 0% Book details