Sashe 78
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
diba kamar yadda ta saba a kullanta ta mika mata takai mata part dinta ta dawo tana fita ta dan labe ta ganta tana zuba abu ga sauran miyan ta motse don dama tunda taga anyi haka take zargin akwai wani abu kuma gashi hjy taja mata kunne kan ta saka ido sosai taga abinda hjy karima din take masu a girkin su sai gashi kuma ta gani. Da farko bata so yarda da hakan ba saida mommy din tace kin san dai nice na daukoki gidan nan da kuma a guna kike in ba yanzu da kuka hade ba idan har cutan mu take yi to harke ake cuta don duk abinda akayi tare dake muka ci shi a gidan nan. Wanan yasa jikin ta yai sanyi ta dawo hankalinta da ta kwadaitu da dan abin da hjy karima din kan mata ihisani dashi don kama bakin ta a kanta mata ku kula da yawan mutane badon son ransu suka juya ma baya ba. Sai don kwadayin abin duniya da akan basu a jaye su dashi hankalinsu ya raja,a ga amarya har su bar wanda suke tare dashi su hade kai da bakuwa sabon zuwa don zuciya bata da kashi. Saboda shi alheri bai bar komai don kyautatawa yana saka kaunan ka a zuciyan mutane har suji suna kaunan ka da zuciya daya komai munin halin ka kuwa. Gabanta ke faduwa sosai koda ta dawo hjy din ke fadin ki karasa zuba abincin akawa kowa nasa har wa yan nan bakin ki zuba masu miya mai yawa akai masu. Tace baki hjy jiya da mukai girki tace a daina saka masu abincin yanzu don nasu sukeyi a aurin su basai an saka masu ba su. Wani irin juyowa tayi da mamaki tana fadin a daina saka masu suna girkin su daban akan wani dalili ta tsareta da idanu. Tace nima ban sani ba gurkin nan daina hjy kaf ba,ayi dasu ba jin haka ta fita fuuuu zuwa part din mommy din ta fado masu ciki a fusace tana fadin. Duk ta samesu a zaune falon su ta soma fadin bako sallama yanzu Asabe ke fada min wai an daina saka abinci da bakin nan . Hjy tace eh saboda basa iyacin abincin mu kada abin ya zamo barna yasa aka sayo masu wanda zasu iyaci a wurin su. Din sufi mutane ko me don ni ban gane wanan fitinan ba haka wasukafi a gidan nan da za ace wai abincin su daban ne da namu yanzu. Ba haka bane kinsan bawai sun iya cin namu cimakar bane na nan yasa yaran basa iya cin abinci wanan ai masifane aka daukowa mutane. Wasukafi ko wa suka kai ta juya ta fita tana fada tare da fadin idan ba munafunci ba don me ba za a fadawa mutum ba ko banda hakkin sanin hakane a gidan. Ya fita suka hade da Asabe a hanya take gaida ita da dan girmamawa har lokacin jikin asabe ya rawa don abinda ta ganewa idon ta din game da ita a kitchen din. Nan ta shigo ta aje abincin suna gaida ita da aiki take fadin ga abinci an gama hjy saidai yau din na ganewa idona gaskiyan abinda kika fada min don ta zuba ta motsa miyan bayan ta gargadani zuwa kai mata nata da batayi hadi a cikin sa ba. Shine na dan tsaya na labe na kamata tana zubawa a cikin wanan din daya saura shi kuma tace na dibarwa bakin nan daku nan na kai maku. Ke nan wanan din tayiwa hadi ke nan bada nata ba ta tambaya tace hakane hjy ki gafarceni kusukurena ne da ban tsaya a inda kika ajeni na kula da komai yadda ya dace inyi ba. Koma me tayi muna Allah zai isar muna a kanta don da nufin cutan mu tayi wanan abin da takeyi har Allah yasa yarinyar nan ta gane hakan da badon haka ba haka zamuyi tacin mugun abu tana cutan mu a kullun. Ban faye shiga ko ina ba na gidan don ma umma ce data matsa na dinga shiga part din mommy ina gaida ita a can ba sai tazo nan ba ta samemu bamu je mun gaidasu ba. Yasa har nakan dan shiga kuma bana iya sake jiki dasu kona shiga din don kowama tsoron sa nake a nan arewa tunda akwai hassada a zukatan su. Zamu dafa abinda ramu ke so muci mu sha mai kyau amma hakan bai hana umman shiga cikin tunane ba don ita ko yaushe zaki ga ta zauna tayi shiru abin duniya yana damunta. Ba komai umma ke tunane ba sai yadda makomar mu zata kasance a karshe in lokacin haduwan mu da yan uwan mahaifin mu yayi. Sam ban da zuwan baki gidan ba ina kwance ne umma tace najie wurin mommy in samo mata paracetamol tasha kanta na ciwo. Na shiga falon da sallama sai naja na tsaya suma din dakatar da dariyan da sukeyi sukayi a lokacin suka zubo min idanu a kaina. U are wellcome ma nace dasu ina dan rusun nawa tare da fadin good afternoon ma suka amsa min kamar yadda na gaidasu din. Nace mommy do u have paracetamol tablet, my mother want to use it, har lokacin ido suka zubo min suna kallo na da mamaki. Tace go and check dat rober nd see na nufi wurin data nuna min din don nasan inda take ajewa sai naji dayan su tace . Ina kuma kuka samu wa yan nan haka kamar kabila sai mommy din tace dasu diyar aminn Alh ne suka zo . Daga ina dayan ta kara tambaya mommy din tace daga lagos suke aukuwa dai ga kama nan a fili wata ta fada a cikin su. Tubarkallah ma sha Allah wanan yar kamar ba diyar kabila ba idan ka ganta sai dai idan ka kalli shigan nata ko batayi magana ba zaka gane kabilace ita. Suma fa a cikin su dama ana samun kyawawa haka sosai wallahi kamar su sukayi kansu wurin kyau saidai kuyi mata magana mana wanan shiga haka ga yarinya haka da dirin daukan hankali. Dariya mommy din tayi na dauko maganin tare da dan rusunawa ina fadin thank u ma na juya na fita duk suka bini da kallo. Dayan mai kama da hamshakiya ta maya da bayan ta saman kujera tana fadin yarinyar nada shawa,a ga kuma irin ladabin su. A kwai ladabi kan saidai ni bazan iya aje irin wa yan nan a cikin gidana ba azo ayi barna wanan kyau tafa bana wasa bane don duk dirin da ake son ya mace tana dashi. Dadin abindai baku da yawan samari a gidan shine amma gaskiya tana da kyau sosai suka katse hiran da dauko wani hira kuma. Nakaiwa umma magani tashe ba, a dade ba sai ga mommy ta shigo part din mu tana tambayan umma din ashe bata jin dadine jikin ta ne Umma ta dan dago daga kwancen tana fadin kaina ne kamar ya fashe nake ji dazun shine na tura ta ta nemo min magani. Dazun su hjy Asiya sun zo gidan nan ai saidai babu halin inzo dasu nan ku gaisa don ina gudun Alh yai fadan hakan. Allah sarki aiko da mun gana dasu wallahi umma ta fada kafin tace yaushe rabona dasune wai Allah dai ya kyauta wanan al,amarin. Ai zan tura yaran nan gobe gidan su sai suje tare da sahiba suga wuri gobe idan Allah ya kaimu ta fada tana mikewa. Umma ta kalleta tana fadin fitan dasu bai kawo matsala kada daddysu ya dawo yai fada suja maki laifi. Tace daga fita kawai da suke zuwa school fa ai ba zasu san ita ko wacece bane tukun na sai ya gama shirin shi ta fada har gidan modibbo zasu tafi idan sun fita din gobe weekend