← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 216 OF 337

Sashe 216

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

magidanci ace bai samun kulawa yadda ya dace haka ga iyalin shi waima mai aikin meye ranan ta a gidan ne ita ? Kai kuma ya haka ta fada a fili wai wama ya baka abuncine gidan nan yanzu kai tsaye yana daukan kofin ruwa yace faizace kuma ta fita. Zaune ta karasa kaiwa tana fadin kai yaran nan basa ji saida fa na gargadesu da hakan su daina baka abinci bana son fitinan matarka wallahi don bata da kunya. Mommy don Nazifa kikace su daina bani abinci ai kasan halinta dai wuri rashin kunya ta fada tare da daure fuska lokaci daya. Ni zanje Abujane yanzu ya fada ko daddy ya tashi yanzu da wuya idan sun tashi tunda yara ba makaranta suke zuwa ba saidai ka duba in ya fito. No indai ya tashi ki fada mai nazo bai tashi ba zance kan case din uncle Nuhu mu gani idan zasu ban belin shi. Allah yasa su baka wanan abu dai baiyi dadi ba wallahi yanzu ita sahiban tasa dai aka rufeshi ke nan . Mommy ko itace ai bata da yadda zatayi tunda baida niyar biyan su kudin da company ke bin shi kinga ai yanzu yasan da gaske sukeyi tunda shi komai yace aikin suhiri zaiwa mutum. Sahiba ko ba ai mata wanan idan ya sani munyi magana da ita da safen nan tace ya fadi lokacin da zai bada kudin sai a bada belim shi shine zan tafi in ganshi yau din ko hankali zai kwanta. Ni dai bana son kana saka kanka cikin wanan zancen gaskiya da zakaji ta tawa kabarsu can su karata a tsakanin su zaifi. Bani kadai zan tafi ba tare dasu uncle hamza ne zamu tafi so ni zuwa kawai zanyi inga manya a can final. Alh yasan da zuwan ku daddy bai sani ba ina ji amma ai yasan da zancen neman bellin don shima ya gwada ba a bashi ba. Wayan shi ya dau kara ya dauka yana fadin gashi tafe yana tare da mommy ne daga haka ya kashe wayan yana mata sallama ya fita tana mashi addua. A ranan kan basu dawo gida ba saida Alh nuhu din wanda ya fada sosai da dare suka shigo kaduna suka wuce dashi gidan shi kai tsaye nan iyali suka shiga murna kowa da abinda yake fada. Bayan sun sauke shi gida ya nufa ya samu basuyi barci ba yaran ne da suka ganshi suka tare shi a cikin murna itako tana zaune a hakince tunda ta juyo ta kalle shi sau daya yana shigowa bata kara juyowa gareshi ba. Dakin shi ya shiga ya watsa ruwa kafin ya fito yana tambayan abincin shi sai lokacin tayi magana tana fadin nasan ina kaje tunda safe ni banyi abincin dare ba yau naka na rana mukaci. Kallonta yayi kafin ya juya ya koma zuwa dakin shi cikin takaici shirin kwanciya yayi kafin kira waya ya shigo mashi sun dade suna waya da wanda ya kirashi daga Abujan kafin suyi sallama yana kashe wayan a lokacin. Iska ya furzo daga bakin shi tare da shafo kanshi yana gyara kwanciyar shi don abinda sukai magana a kai din yanzu. Bai saba mata haka ba yanzu ma din daya share ta yana jin bai kyauta ba hakan yasa ya mike zuwa dakin da mahaifiyar nasa ta sauka. Yako samu Alajan ta hau dashi iyakar hau don yana shiga tunda taga shine taci gaba da wayan ta da ya sama tanayi a lokacin. Daga tsayen kaiwa yayi zaune saman gadon yana kishingidewa tare da zaro wayan shi daga aljihun shi yana latsawa. Har ta gaji ta kashe wayan taci gaba da tsabgogin gabanta lokaci guda ya fara gaida ita bata juyo ba balle ta kalleshi. Ummi wani abu ya farune ya tambaye ta a lokacin ta dago tana fadin sha,aban ban san me kake nufi dani ba a yanzu watau ban isa in ma magana ba kaji. Magana ummi wace magana ke nan ya tambaya cikin mamaki kamar bai san abinda take nufi ba a lokacin. Kada ka maidani mahaukaciya mana shaaban kana nufin gayatan yarinyar nan da iyayyen ta da nayi haka zasu zo ka nuna masu ban isa da kai ba ? Har a gabana kake rike hannun yarinyar nan kana laluba wai ka nuna min ban isa da kai ba kome da har gaban kowa ka nuna min kai ga zabin ka. Haba ummi kiyi min adalci wan can karon nayi maku biyayya ga abinda kuke so ya kamata wanan karin kuma ku bani dama nima in gwada sa,ata mana na fada maki bana son wanan hadin da kuke son yi yanzu . Ya kamata this time ki bani chans nima in nemo abinda zuciyana ke so da sauri ta kallo shi tana fadin badai wanan zabin naka ba mara amfani a garemu . Ko don jujun ta kake sonta ne sai ko kuwa don kyau da take dashi bayan nan fa ka fada man wani abu da yarinyar nan zata gwada wa wace na zabo ma yanzu. Kai ya girgiza yana fadin ko daya ummi saboda halinta na gaskiya da sanin ya kamatane kawai nake son ta. Gaskiyan ta na banza da wofi dama don ta kamaka haka yasa ta nuna maka ita mai gaskiyace ai . Dama nasan abinda zai faru a karshe ke nan tai maka jujun da zaka mutu da sonta umiportant love zakayi don abinka take so ba kai ba. Lalala haram Alaja ita ba yadda kike zato take ba asalima ni din ke son ta ba itace ke sona ba don haka ita na yanke a zuciyana zan aura final. Yana fadin haka ya mike daga inda yake zaune ya gyara kayan shi da sukai dan squzing yana kokarin fita daga dakin ta kira sunan shi ya tsaya cak ba tare da juyowa ba. Tace udan tace hakane zan nuna mata ita bata isa ba ko juju din gaba da gabanta wani jujun yafi karfin nata.
Chapter 216 · 0% Book details