Sashe 84
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
muna dai irin yayan ashawo din nan da turawa ko larabawa kewa ciki akazo maku da ita gida. Wanan kinyi gangancin barin ta cikin ku wallahi fuska anty ta tabe tana fadin ke dai bari nayi magana da uban da matar gidan har dansu sunce ina nafito . Wai yar aminin ogace daya rasu don haka suba zasu yarda in wullakanta suba lokacun fa Alh nunawa yayi kona bar gidan idan ban iya zama dasu. Kinga ko ya zanyi ga yaran nan kaf din su sun dauki son duniya sun dora a kanta kona hana suna part din su lake a wurun su . Idan kinga hakan sakin fuska suka samu aishi yaro haka yake kaman kare in yaga sakin fuska saidai gaskiya kiyi taka tsantsan da irin wa yan nan tsintattun mage din idan idon ta ya bude nan gaba ba zaku iyata gidan nan. Sai ta ukun su tace kai haba menene ba gashi yanzu tana more mata ba albarkacin zama tare meye wani abin tayi hankali a nan don Allah ku bar wanan zancen haka tunda yarinyar na taimaka mata jifa yau yadda muka samu part din nan tsab. Wani iri naji na wanan maganan da sykeyi naji kamar in saka masu magana saidai yin hakan zaisa a gane ina jin hausa. Tunda a zaton su har daddy din gidan mu bamu jin ko zo in kasheki idan an fada balle shi amar da har yanzu bako yake a gidan ga kowa. Sai dana hada komai cikin dauriya na na dan rage yawan gas din na fito don tunda daddy ya dawo wanan can karon akai rikicin girki kowa ya dauki girkin shi a gidan shi da yaran shi . Don anty ce ta tayarda fitinan don me za a bamu girkin mu daban a gidan su kuma a hade masu suci na yawa a gidan da yaran su. Allah ya kawo saukin kai daddy din yace ai sai kowa din ya dauki nasa ba komai bane idan sunga hakan yafi garesu dama shi don yaran sa su hada kansu yace hakan . Kuma abinci da suke gani bashi ke saya muna ba modibbone yace a bar masa wanan nauyin don yana kwadayin ladan da zai samu ga ciyar da marayu ya dauki hakan. Daga wanan ranan aka kaiwa kowa kayan girkinshi a part din shi har muka samu arzikin saka muna freeze a dakin mu muma da aka sawo wa kowa don aje abin amfani karya baci. Na fito ban ko kalli inda suke ba son suna yan dararakun su a lokacin nasa kai na fice a part din cikin kunan rai. Ina shiga wurin mu na zauna na fara cire safan kafana na nufi cikin dakin kai tsaye wanka na fada yi saida na fito ne nake ba umma labari abinda ya faru . Murmushi umna din tayi tana fadin wanan haka hakin matan mu yake ga kishi su a zaton su kada daddy ku ya dawo ya aure ki. Idan ma harta dauka haka din ne daga baya zatayi kunyar hakan don zata gane shidin ubane na kwarai a gareki kudin ba kalan dangi bane gunsa yadda suka dauka din. Fatima ce tayi sallama ta shigo dauke da abincin da suka dafa tana fadin ga abunci inji mami nakawo maki ina fadi da sauri koma dashi ga wanda umma ta girka nan banci ba ma . Zoki aje umma ta fadawa yarinyar ta aje abincin a gaban umma ko kallon abincin banyi ba karshe ma tashi nayi na koma daki na kwanta. Barci nayi sosai ban tashi ba sai karfe biyu saura na tashi don Allah koda na fito har lokacin kwanon abincin yana nan dakin mu ba alaman an tabashi. Fita nayi zuwa part din mommy nan samesu ga turamen zani masu yawa a gefen ta a zube bai shafeni ban kuma tsaya kallo ba nake gaida mami kafin in wuce zuwa dakin kwanan su don nasan mutumiyana fa,iza tana can dakin tunda ban ganta a falon cikin su ba. Tana zaune tana waya na shigo ta kalleni da murmushi taci gaba da waya har ta gama ina dan duke ina karanta wani takardan da nagani. Tace ina jiran ki tun dazun kinga kaya a falon mu anko ne aka kawo muna na yar kanwar daddy da zata aure. Ke ai kin santa wace sukazo ranan har take fadin ki bata kanki kuyi musaya da ita nace na gane ta. Itace zatayi aure kin san yayan modibbo taso kamar ta mutu amma yanzu zata auri wani dan uwan baban sune a jos shine . Jos na tambaya tace min eh ko kin san jos din ne ta tambayeni tana kallo na nace ban san ko ina a arewa, ba banda wanan garin. Zaki sani har idan mun dace za a tafi damu ai zakiga gari na danyi dariya ina fadin wa zai tafi dani bansan kowa ba ? Tace aukin san mu ko kuma tare damu zaki tafi don su anty Nabilace manyan kawayen bukin kinga kuwa ai damu za ayi komai taso muje falon mu duba ankon. Ta daga na bita a baya muka zauna ni dai ina a takure ta jefo min zanin daya a jikina tana fadin wanan nakine. Na nuna kaina da mamaki ina dagowa nace ni tace eh zaki koyi daura a tamfa ko, kome kuke kiran shi a can nace ankara. Tace akwai wasu da za,a kawo muna wani irn dinki zakiyi da naki duk a cikin turanci buga buga muke maganan mu din dasu. Kafin nayi magana mommy tace a cikin hausa ina tasan inda ake dinki ko tasan inda za a dinka din balle takai ayi mata ku kai mata ayi mata. Nabila ta dago tana fadin ni kin san aiba irin dinkin su zanyi ba don haka karma a dora min wanan nauyi ban iyawa . Tellana zamu kaiwa yayi muna dinki ta fa,iza ta bada sai hauwa tace dama kun fi kusa da ita sai kukai ai maku tare din. Mommy tace na rabaki da wanan halin Nabila yarinyar nan idan bata biku ba wata sani a garin nan yanzu zaki wani fara fadin maganan banza a kanta tun yanzu. Shiru sukayi ga baki dayan su a falon har mommy din ta kare ni ke tambaya me ake dinkawa ga ango zanine ko buje ko dogon riga ? Wanda ranki ya zaba idan muje gun maidinkin zai baki hotone ki zabi wanda yai maki kyau sai a dinka maki nace buje nake so ba zani ba ko dogon riga. Mun dan dade muna hira a dakin dasu har zuwa yamma na koma part din mu ina bawa umma labarin zance zanin da yadda akayi. Washe gari ko sai ga Fa,iza har dakin mu tace in shirya zamu kai dinkin ankon namu saida ta jira na shirya duk da ni ba wani kwaliya nakeyi ba mun fito ne sai muka hadu da ya Abubakar zai shigo gidan mukayi mashi sannu da zuwa. Ya amsa yake tambayan mu inda zamu tafi Fa,iza ta fada mai yace kada mu dade mu daina fita wuri mai nisa haka. Bada motan gida muka fita ba taxi muka shiga zuwa wurin akwai mutane a shagon dinki tayiwa tellan bayani ya kawo min photuna na zaba sai suka saka min dariya wai ai din kin iyamurai ne wanan dana zaba nace shi din dai nake so ni akai jinga ya fadi kudin shi. Mun dawo gida take basu labarin irin dinkin dana zaba sukai ta min dariya wai ni zan dawo ince ban shi wata rana aka shigowa masu da nama kallon naman nayi sai gabana ya fadi. Da sauri na fita zuwa part din mu har na zauna zuciyana yana tashi hankalina kuma bai kwanta ba da ganin wanan naman . Hardai hakan ya jawo min yin amai bayan na fitone na kasa daurewa na fadawa umma abunda nake ji game da naman . Sai hankalin umma bai kwanta ba da zancen dole ta kira mommy ta fada mata abinda ke faruwa game da naman da nagani a part din ta dazun . Sun ki ci zuwa safe naman yayi wani irin baki ba dadin ganin hakan ya kara tsora mommy hae umma ga lamarina ga buki kan sun fara a gidan sosai kullun cikin fita auke yanzu.