Sashe 114
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun tambayeni umma tace dasu ina barci tun ranan da abin ya faru bana ciki hayacina don lafiya bai isheni ba tun lokacin. Sun nuna tausayawan su ga hakan daya faru yayin da suke dan dube dube a gidan kafin su aje key din motan suna fadin ga wanan shugaban wurin aikin mune ya aiko mu muyi ma Sahiba godiya mukuma bata wanan a matsayin tukwaicin abinda tayi mai har kudaden shi suka fito gareshi. Yana fadin hakan ya aje dan makulin mota saman kujera tare da envelope yana fadin wanan kuma kudin mai ne ya bayar tasha mai muyi duba da zata shigo aiki sai dai bamu ganta ba tun wanan ranan a zaton mu abinda ya farune ya hanata fitowa aiki a wurin mu din. Bashi bane lafiyane bata dashi bayan haka kuma tun kan faruwan wanan abin dama tana da niyar barin aiki a tare daku nan gaba kadan. No no mama don do that please, we want to work with dis gurl now don Allah ayi hakkuri abi, ya kalli sauran yana tambaya idan ya fadi daidai a lokacin. Suma dai dariya suka kwashe dashi a lokaci daya don sunji irin hausan da yayi lokacin sai dayan yace ba karamin ci gaba muka samuba a sanadin wanan yarinya a yanzu. Don ayi muna barna mai yawa da bai dace ba wanda gaba dayan mu wurin nan da duk ya shafe mu saidai Allah zai cece mu kawai. Sai ga Allah ya jefo muna sahiba a ciki rayuwan mu ta warware muna wanan rikicin wanda hakan yai muna dadi ga Abdulhamid nan shi yayi muna bayanin komai muka fahinci baiwane Allah yayi mata a kan hakan mun gode mun gode kwarai da abinda tayi muna din. Makulin dake samandan table gaban umma ta dauka tana fadin muma mun gode da kuka fahinci hakan sai dai ku mayar masa da makulin motar shi a yanzu sahiba bata kai bukatan mota ba a rayuwan ta. Sahiba yarinya ce kara dake shirin rufe shekara ashirin a wanan shrkaran mai zuwa yayana marayune basu da mahaifi don mahaifin su tun sahiba nada shekara uku ya rasu ya barni da cikin dan uwanta ta sanadiyan kasheshi da yan uwan haihuwan shi sukayi don kawai kan abin duniya. A haka nake kula da diyana bayan na gudo zuwa nan dasu har zuwa yau din nan da kuka zo min da wanan maganan don haka ba zan karbi komai nasa ba . Sahiba nada wanan laluran tun tana yarinya haka yasa bana son tana shiga mutane sosai don abin zuwa yake mata a lokacin da ba,a zata ba idan wani yayi abin da bai dace ba ga dan uwan shi ma,ana dai ba,a cuta a gaban ta idan tana wuri zata fadi haka kai tsaye ba tare da anyi tsamanin hakan ba. Kallon juna sukayi lokaci guda kafin su juya ga umma suna fadin shi wanan kyautan ba komai bane daga cikin abinda yake da dan haka kada ki hanawa yar ki jin dadin daman da Allah ya bata a yanzu. Abdulhamid ne ya tare da fadin mama nasan me kike nufi da zancen ki insha Allahu hakan ba zai faru da yarki ba a rayuwan ta saboda adduan ki a gareta da kuma maraicin dake saman kansu a yanzu na rashin mahaifin su tare dasu. Wanan ba komai bane hakan wani budine daga Allah daya fara aiko mata a rayuwan ta a yanzu, adduan ki gareta shine abin bukata don haka kiyi hakkuri ki karbi kyautan nan a matsayin tukwicin abinda tayi muna ga baki dayan mu. Shiru umma tayi tana tunane a daidai lokacin suka mike suna fadin su zasu tafi sun gode kuma da taron da akai masu. Ban san wainar da ake toyaba a gidan ina dakina rufe ina barci ga don haka bana sanin abinda ke faruwa a cikin gidan lokacin. Ban fito ba sai karfe uku na rana na tashi nayi sallah bayan na kara watsawa jikina ruwan sanyi don na danji daman yadda nake ji a lokacin. Fitowa nayi falon bayan na idar da sallah umma na sama zaune a falon tayi shiru ta mike kafafun ta saman center carpet din falon mai jikin damisa . Sannu da gida nayi mata ta bini da kallo har na zauna take fadin me zanci akwai abincin data dafa a kitchen ta debo min naci. Nace ba yanzu ba umma ina kaiwa kwance ta kalloni tana fadin Sahiba zaki halaka kanki da yunwa na fada maki ki dinga daurewa kina dan cin abinci don ki samu sauki da sauri amma bakaci komai ba ya zaka gane kaji saukin jikin ka. Zan sha tea umma na fada ina bata fuska tace madara ya kare nace da lipton kawai nake so nasha don dama sai naga dama nake shan tea din da madara wani lokaci. Mikewa nayi zuwa kitchen din umma ta bini da kallo na hado ruwan zafi tare da litop da dab suga kadan don ban faye son suga ba ni haka dai nake na zauna ina dan tsoma ganyen shayin a ruwan zafi umma ta kura min ido daga inda take zaune. Kafin na dago na fara dan kurbawa ina hutawa zuwa can na dauka na kara kai cup din a bakina ina kurbawa naji umma tana cewa yan wajen aikin ku sunzo kina barci. Da sauri na cired cup din abakina har ina sarkewa wurin fadin gidan umma yaushe suka zo ? Yau din nan suka zo kina barci ga key nan da wanan takardan suka kawo a matsayin tukwicin aikin da kikai masu wai sunce a baki. Aiki kuma umma kuma sai kika karba kuma hakan na nufin ai na zama mai bada magani ke nan kuma umma. Nima abinda nakewa gudu ke nan naki karban wanan abinda suka kawo amma sai yaron nan na cikin su musulmi din nan yai min magana kan na karba wanan ba komai bane daga cikin dukiyan wanda ya baki koda bamu karba ba wani zai ba shi gara dai din mu karba yafi. Kinji dalilin da yasa na karba na kuma fada masu cewa zaki bar aiki dasu nan bada dadewa ba suka nuna bacin ransu ga hakan suna roko a barki ki koma aiki dasu don Allah. Nace dama kina da niyar barin aiki ko ba wanan matsalan ya faru yanzu ba dama akwai niyat yin hakan gareki zaki aje aikin ki dasu. Bazan kara zuwa aiki dasu ba umma wurin ga baki daya ya fice min a raina don ranan dana je karshe suka nuna min ba sabo ga aikin su idan ka saba masu zan dawo nan kofan gida ko snack na dinga ajewa da dare tunda wanan titin namu babban hanyane na kowa. Ko bakiyi wanan ba yanzu wanan kayan drinks din da mukeyi akwai kasuwa sosai a gareshi ana samu sosai a cikin sa matsala dai shine rashin jarin mai tsoka da bamu dashi a hannu da sai mu kara ya zamanto muna egent na company yadda za a iya sari a wurin mu. Shiru nayi ina tunane don umma ta kawo babban shawara a nan saidai inda zamu samu kudin yin hakan ne a yanzu shine matsalan. Dan shirune ya biyo baya kafin nace yanzu umma yaya zamuyi da wanan kayan tace dani wanan dai zamu jira yazo tunda yace zai shigo ya kaimu wurin wani da zai baki maganin matsalan ki. Umma ni banda wani matsala banda ciwon kan nan dake yawan damuna wani lokaci shine dai din matsalana a yanzu. Shidin dai ai ake magana do mutanen kanki suke haddasa maki wanan matsalan ciwon kan ai idan su taso maki gara tun wuri a nema maki magani a kanshi zaifi. Amma umma kin san matsalan masu maganin nan a yanzu shine irin kudin da suke tsulawa mutum tunda ba ko yaushe ne hakan ke taso min da a barshi kawai zaifi. Sahiba kin san matsalan nan naki ba karamar matsala bace fa yau da ace mutanen basu da fahinta kinsan abinda hakan da suka sakaki zai jawo muna kuwa ? Ban dauki key din ba bankumayi magana a kan komai ba karshe ma na mike na shige daki ina tunane na bar komai a wurin. Don ni almara naji zancen motan kamar a mafalki na dauki zancen waini sahiba ce da kyautan mota gun mutumin da ban san shiba ban kuma da wata alaka dashi. Da yamma Abdulhamid dinne ya dawo gidan mu sun tsaya a falo suna magana na fito maka gaisa dashi yake tambayana yaya jiki nace da sauki . Suka cigaba da magana da umma akan alkawarin gobe da yamma zai zo ya kaimu wurin mai maganin dayace din. Umma tace ab gode saidai da fatan ba wanda za a kaucewa Allah bane wurin ya danyi murmushi yana fadin. Shima baya shirin da irin wa yan nan mutanen sam inda za ai muna rukiya ne asan abinda suke so su rabu dani har abada idan hakan mai yuyuwane. Sai kuma ya dauko zancen inda za,a aje min motana don sabuwace dallailiya ashe don ma komai nata a leda yake tukun ba a bude shi ba. Umma tace akwai gareji a gidan nan sai dai ba a gyara shi ba yace ba matsala zai mayar da motar company ya kwana a can don akwai tsaro a wurin gobe zaizo dame gyara a gyara wurin da zan dinga aje motan a gidan. Ya dan dago yana tambayana ko na iya mota da sauri na dan girgiza kai ina bata fuskana da kawar da kai yace ba matsala matarshi ta iya mota sosai za a samu lokaci ta koya min. Hakan daya fada yasa na danji sanyi a raina ya mike tare da yi muna sallama umma na masa godiya yace tabar gode mai yana kwadayin ladan kula da marayu ne a garemu. Odaro na fada daga inda make zaune ban tashi ba don ni jin komai nake har lokacin kamar a mafalki don har lokacin zuciyana bata gaskanta min gaskiya bace motar tawa ce wai. Umma ta dan dade a waje saida ya nuna mata ko ina na motan kafin ya shiga yaja zuwa inda yace zaikai ta din ya tafi. Sai bayan ya tafine umma ta shigo sai kuma hankalin