← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 337

Sashe 106

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

baida nisa da gidan mu sosai. Idan na dawo daga school zan saka uniform din aikin wajen in tafi aiki sai dare nake dawowa sai dai aikin ya fara fita min rai saboda wani lokaci koda zan dawo hanya ba mutane da yawa sosai. Shiyasa tun wanan abinda ya faru dani yanzu sai nake jin tsoron hawan Nape idan dare yayi yasa nake sin barin aiki a shagon. Manyan mutane yan kwalisa masu ji da kansu maza da mata ke zuwa sayayya wanan shagon da nake aiki din wasu suyi muna alheri wasu kuma musha disgawa a wajen su duk da muma dai neman kudine ya kawomu shagon ba wani abu ba. Gashi duk wanda ke shagon sai sun maka interview sun ga idan ka cancanci aiki dasu zasu daukeka aiki a wurin don tasare tsareb su saidai akwai kudi sosai yasa mutane ke neman aiki a wurin suyi. Nima wata kawata yar school din muce ta kaini wurin da wasa sai ko suka daukeni gashi suna jin dadin aiki dani don ina jin yaruka kala kala a bakina don yawon gidan haya da mukayi a baya tun ina karama. Yau ma duk da nagaji don mun dan wahala a makaranta hakan baisa na zauna na hutawa rayuwana ba a gida . A gurguje na shirya zuwa aurin aikin duk da nasan na makara a lokacin zasu iya korana inyi hasaran kudin ranan ke nan. Don sai sun cire a karshen wata a cikin abinda suke bamu din yasa ban son missing din ranan zuwa aikin don kada dan abinda suke bamu ya ragu. Tun a kofa ganin ogan gaba daya a waje yasa na sha jinin jikina duk da yana magana da wani hakan bai hana in tsaya in gaida shi ba a wurin. Ina fadin good day sir har ya amsa cikin daga hannu na dan wuce sai kuma naji yace dani wait wani lokaci kika zo aiki ke nan ? Sorry sir na samu dealy ne daga school ban dawo da wuri ba sai yanzu na dawo na kara fadan sorry sir ina dukar da kai. Sai ki koma yau baki da aiki ke nan ya fada yana kawar da kanshi gefe daya ka barta ta shiga tunda ta bada uzurin ta . Kai na dago na kalli wanda ke maganan farine sosai mai zubin iyamurai ga dan saje a fuskan shi yana saye a cikin suit baka data karbi jikin shi. Saidai kana kallon shi kasan boko ya ratsa jikin shi da yawa haka wayewa sai yake min zubi da yanayin wani wanda na sani. Ga shekaru kuma baikai ya Abubakar ba ko ya mustapha saidai do jin dadi da samun wuri zai iya kaisu ga gani idan mutum yayi mashi kallon tsoro. Thank u sir na fada ba tare dana tsaya jiran komai ba nashige daga ciki na barsu a wurin a gurguje na fara aikina don na samu har an kawo wata ta a madadina ta tsare bangaren da nake aikin ko. Tare suka shigo da ogan mu suna zagayawa na kara gaidasu ban kula ba ko sun karba min don dai naci gaba da zagaya wurin da nake din ina duban masu shige da fice a gefen wurin. Sun danyi tako baikai biyu ba wayan shine yayi kara yaja ya tsaya yana daukan wayan tare da fadin hello Didi, Tun suna magana da turanci har suka koma kamar larabci daga inda nake zaune na saka earpieces a kunne na ina bitan karatuna don ban yarda na yarda karatun dana samu a zaman mu na kaduna ba. Na hango wasu sun zo part dina suna duba kayan zasu tafi basu mayar da kyau ba nake fadin zaku jawa mutane hasara ga banza kuma ba saye zakuyi ba ku kuja min matsala ga mutanen nan da basu san kaddara ba. Ya juyo ya tsaya yana kallona a cikin mamaki na gyara kayan ina dan kara kakabesu na koma inda muke zama na zauna kafin custurmers su shigo wurin ga hasken a ko ina ya haske wurin ga baki daya ba zakace darene ba a lokacin do haka kalan wurin ya bada ma,ana sosai. Mun saba ganin irin su yan kwalisa suna shigowa shagon don haka ban damu da isan koshi waye ba na dai ganshi da oga suna zagayawa haka yasa na fahinci yana da muhinmanci a wurin ogan namu.q Har kusan lokacin tashi mun daga aikin suna tare da oga da sauran manyan shagon a lokacin ne na fito da abayana daga cikin jakkata na dora saman jan rigan dake da tabarin shagon da bakin bujen dake jikina. Nayi rolling din kaina da gyalen kayan ina irin wanan shigarne don kare mutuncina don ban yarda in fita hakana idan zan koma gida saboda bata garin dake akwai a garin. Duk dadewan shagon shine goma da rabi zuwa sha dayan dare mu mata goman ne namu sai dai wa yanda ke kusa da shago din ke zama har a rufe shagon su tafi. Jakkana na dauka inda muke ajewa ina fadin good night oga da cewa manyan mu dake wurin suka amsa min da cewa night miss Sahiba na fito ina gyara dan kwalin abayan da yake dan sabulowa a jikin nawa. Sai lokacin naga hadarin daya game gari yayi bakikirin yana shirin tasowa da iska ban damu da wa yanda ke haraban ba nake fadin ya subbahanallah Allah ka ceceni na samu abin hawa ya karasa dani gida kafin ruwan nan ya fado. Na dan tsaya na minti biyu lokacin har an fara iska a garin kadan kadan yasa na fara dan takawa da kafa don kada ruwan ya tsayar dani a wurin. Motocin dake fitowa nake dan waige kafin wata motar ubansu taja ta tsaya a gabana jan danjan bayanta yana dan haskawa kadan kadan har na tako ina kokarin wuce ta . Glass din motan aka zuge lokaci guda naji wani murya na fadin can i help you don akwai hadari ruwa zai iya fadowa ko wani lokaci a yanzu. Na duba da kyau na gane wanan guy din ne dana gani da shugaban shagon mu yake min magana no zan iya takawa ba nisa sosai na fada ina ci gaba da tafiya. Kada kiji tsorona niba mugu bane ya fada a cikin hausan shi pure saidai hausan akwai dan bambamci dana yan kaduna dana kara gwanewa yanzu dashi. Mamakine ya kamani jin hausa radau a bakin shi yasa naja na tsaya ina bashi hakkuri tare da fadin. Ba haka nake nufi ba don kada in bata ma lokaci na fadi hakan banda nisa sosai da nan shiyasa nace hakan . Kizo ki shiga na saukeki kada ruwa ya tsare mu banyi mussu ba ya bude gaban motan na shiga ya subbahanallah na fada a raina. Kamshi da sanyi ne sukai min maraba a motan sai kuma karatun malamina dan india ne ko balarabe dake kira,a a cikin motan. Saidana zauna nace nagode na gyara zama na takure a wuri daya kamar a tsorace idan ka ganni a lokacin don nasan ranan na shiga motan maya kan. Bai juyo ko sau daya ya kalli inda nake zaune ba sai tukin shi yakeyi a hankali don ina shiga na fada mai layin da zan tafi yace nayi mai kwatance idan mukai wurin. Layin nace ga wurin ko a nan ma ka saukeni ba nisa damu zan iya karasawa yace gidan nakune bakyason a gani nayi shiru har kofan gida ya saukeni ina faman yi mashi godiya yaja motarshi ba tare da amsa min ba ya tafi. Umma suna waje suna hada kaya don sai na dawo nakan hada mu rufe shagon mu shiga gida zuwa sha daya don masu zuwa sayen kayan sanyi a lokacin. Tun fitowa na daga motan umma ke bina da kallo har na karaso inda suke nagaidasu sukai min sannu da zuwa na karbi kayan dake hannun umma din don sun gama hada komai muka fara tafiya zamu shiga ciki. Naji umma tace dani ina kika samu mai motar nan daya saukeki yanzu na juyo da sauri ina fadin wallahi umma ban san shi ba taimaka min yayi kada ruwan nan ya dukeni . Sahiba kardai ince kin fara kula maza ne a rayuwan ki wani irin juyowa nayi na dakatar da tafiyan ina kallon umma din kafin incw maza kuma umma ? Wallahi nafada maki nansan shiba ban kuma taba ganin sa ba sai yau din nan kuma banda gaisuwa da godiya ba abinda ya hadani dashi.
Chapter 106 · 0% Book details