Sashe 121
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
nan nan gaba kadan idan na gama aiwatar da shirina a kan su. Wayan tane dake hannun ta ya shiga ruri shine kuma ya dakatar da mahaifin nata ga fadin abinda yake fadi a lokacin. Mijin tane yake kiranta a lokacin yaji saukan su don bai samu layin nasu ba sai wanan lokacin amma har wayan ya katse bata iya dagawa ba. Jin mahaifin nasu yayi shiru yasa ta mike zuwa don barin falon ranta a bace dakin mahaifiyar ta ta koma dake zaune ta hakince tana waya tana ba kawarta labarin dawowan yar nata. Kawar na fadin ai gara da kika nace aikai wanan hadin irin matasan da ko wace uwa ke burin taga yarta ta aura ke nan a duniyan nan ai yanzu. Saiga Nazifan ta shigo mata da kuka abinda ya dakatar da ita ke nan daga wayan da takeyi din lokacin tana tambayan yar nata hankali tashe abinda ke faruwa. Dakin ta shiga bata iya ba uwar nata amsa ba don kukan da yaci karfinta a lokacin ba zata iya furta komai a lokacin. Tashi tayi tabi bayan yar nata tana fadin ke lafiya ko mijin nakine wani abu ya sameshi baki fadi zaki dagawa mutane hankali haka ? Mama bashi bane fa ta fada a cikin kuka Abba ne yace baya son diyan nan don baya kaunan zuri,an uban su kuma in rubuta in aje zai rabani da mahaifin su nan bada dadewa ba. Zaune uwar takai tana salati tare da fadin abin na Alh har yakai can don wani bukata nasa ya mayar dake bazawara ko ya mayar maki da diya marayu don shi daukan ran wani a wajen shi ba a bakin komai yake ba. Nazifa din ta dago tana fadin mama zan tafi tunda har Abba ya iya fadin haka kada ya zo halaka min yaran nan don Abba zai iya ga yadda na fahinta yanzu. Dako na tona masa asiri a garin nan idan har ya taba min jikokina da Allah ya fara ban idan ma zasuyi abinsu shida mahaifin Abubakar ya tsaya iya su amma karya kawo gareku gaskiya ta mike da sauri yar tace mama dawo. Zuwan ki yanzu zai iya haifan wani matsala da zai kawo fitina don shima Abba din ya hau yanzu don Allah mamakiyi hakkuri kada ki masa magana yanzu kan hakan. Naji amma yasa duk abinda yake takama dashi nima din nasani don tafiyan duk gudane dani dashi idan yace zai taba min yaran nan yanzu sai inda karfina ya kare dashi wallahi. Abubakar kuma yayi kita bai shiga ba yasa ya bugowa hjy Addah waya yaji ko lafiya matar nasa bata daga waya ba. Don bai taba zaton wai gidan su zata tafi direct ba haka tunda yasa a gyara gidan su kuma tasani komai an saka masu sabo a gidan an kara gyara ko ina na gidan. Wani dalili ya hanashi zuwa tare da iyalin nasa shi sai karshen wata zai shigo ya don aikin daya taso mashi bayan sun gama shirin tafiyan su tare dole ya bari su fara zuwa kafin shi ya biyosu daga baya. Dauka tayi da sallama suka gaisa take tambayan shi aiki da iyalin shi sai mamakin jin hakan ya kamashi har yake fadin. Mommy ai suna Nageria kwana biyu ke nan basu zo bane nan ko baku da labatin zuwan sune ya tambaya cikin mamaki . Suna Nigeria fa kace yace kwarai kuwa mommy tun shekaran jiya suka taso kuma na tabbatar da tana kaduna yanzu haka. Lafiya har ta shigo garin bamu da labarin hakan yace shine abinda ke ban mamaki yanzu ke nan ai mummy don tasan na gyara gida don zuwan ta din ai. Kashe waya yanzu in kira mahaifiyarta muji idan tana gurin su yace tana can ma tunda bata zo nan gurin ku ba ai ya kashe wayan itama ta kalli nata wayan. Ta kira layin baije ba not reachable ake fadi lokacin ne kuma Faiza ta fito daga dakin kwanan su ta zauna tayi shiru tana jin abinda suke magana a kai. Ba wanan ne ke damun ta ba sai mafalkin da tayi shine ya tsaya mata a rai tayi shiru tana nazarin mafalkin a ranta . Hauwace ta kira sunanta ta dago tana fadin na,am Sahiba me kike fadi duk suka zubo mata ido suna kallon ta kafin suce wata Sahiba kuma kike kira yau ? Yau kuma kin tuno Sahibace a zuciyar ki ko me Sahiba kan ai sun manta damu yanzu sunci moriya sun manta kowa yanzu suna can suna bariki Nabila ta fada. Bariki kuma Fa,iza ta tambaya a cikin mamaki idan ba bariki ba me sukeyi a can lagos din dama ? Hjy dake jin su tana kokarin sake kiran mahaifiyar Nazifa ta katsesu da fadin uban wa yace daku haka wai ? Tayi sa,a a lokacin kiran nata ya shiga ta kara a kunnen su har aka dauka da hello ta amsa sai dan gaisuwa sama sama tace na bugo in tambayene idan su Nazifa sun iso gida ? Tace sun iso jiya da yammn nan gata kwance tana barci sai Addah djn tace Alhamdullahi dama mijin tane ya bugo yana tambayan isowar su din . Ashe ta taso ita bamu da labari Allah ya hutar da gajiya yaushe zata iso gida ke nan ta tambaya a karshe. Tace sai ta huta a nan an kwana biyu ko idan mijin ta yazo saita dawo hjy Addah tace amma ko in kunyi hakan bakuyi muna adalci ba gaskiya amma ba matsala zan turo yara su daukan min yaran nan ingansu ta kashe wayan ta. Zage zage hjy ta fara da fadin zancen banza zancdinnmmwofo ni Addah zata kira ta raina min wayau kan danta idan zatayi mulki ta tsaya iya danta kawai don ko yaran nan ba zan yarda su shige mata ba cewa da diyan Nazifa din. Me tace mama Nazifa dake kwance tana waye da kawayen ta ta tambaya ta dan dago tana kallon mahaifiyan nata sai ta fada mata yadda sukayi da Addah. No ba inda zasu tafi ta bari idan ubansu ya dawo mun koma zata gansu kowa ban yarda dashi ba ai yanzu ta fada tana komawa kwancen da take din da farko. Itama din dai Addah fada ta kamayi a nata bangaren tana fadin laiai ma yarinyar nan me take nufi da hakan wai da yin haka ? Amma zata dawo ai zata fada muna dalilinta na komawa gida ta zauna ga dakinta ta bari a nan sai kuma taja tsuki tana fadin shima dai daya turota zuwa gida ita daya haka don su basu raina dalili ai. Mommy yaran ba zamu gansu ba ashe yanzu don nasa ko anje daukan su ba zasu bayar dasu azo gidan nan dasu ba saidai idan yaya ya dawo kasan nan ke nan kuma. Zanje zanje duk abinda zamuyi muyi ta akan yaran nan kafin Alh ya dawo gidan na kuma ya aza min nasa jidalin ina zaune kalau. Wani irun nisawa Nabila tayi kafin tace solution dayane mommy kawai yaya ya kara aure zasu shiga hankalin su idan yayi hakan. Amma wallahu nasan idan kin dogara da wa yan nan jikokin ba zaki taba nunasu a matsayin jikokin na fanin yaya ba tunda kinga sun fara haka. Sun fasan yaran nan gidan nan ba wanda yasan su da ido saidai a photo kawai amma ta iya shigowa kasan nan dasu ta share kowa idan ba don shi din da ya kira yana fadin zuwan ta ba. Kinji ki da wani zancen shirme Abubakar din ne zai kara aure ko wanan din da yaya na samu yayi har aka kai haka din. Iskancin ta yayi yawa mommy haka ya dace ayi masu kawai don idan sun gashi da wata matar ai dole su kama kansu su daina kawowa mutane rainin wayau haka.