← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 337

Sashe 66

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kuka kwana ta amsa da lafiya. Mairo ina kika shege haka tsawon wanan shekarun da kuka kwasa baku gida wanab dan kuma gashi da ganin shi shima dan gidane shi don ya debo kamar mazan gidan mu sosai. Banji me umma tace ba don ina mikewa na mike zaune ina fadin good morning ma ta juyo tana amsawa a cikin sakin fuska a garemu. Dole ne ya kasance ba zamu iya sakewa dasu ba koda kuwa mun tashi a cikin su balle al,adun su yanzun da muke gani bakon lamari a idon mu zama da hausawan. Naji tana tana tambayan umma din da cewa meyasa bamuci abincin da aka kawo muna ba da daren jiya din ko tabawa bamuyi ba. Umma din ne ke fada mata cewa munce bama cin manshanu ta dan kallo inda nake da mamaki tana fadin a ikon Allah dan filo ne zaice baya cin man shanu kuma ? Har saida ta fita nake tambayan umma da ita din wacece a wurin mu take fada min itace mahaifiyar Abubakar daya kawomu gida. Akan hjy Addah din ta fara min bayanin yan uwa take fada min yadda muke da ita maimakon inji dadin hakan sai naji wani iri a raina na ba dadi. Don su gasu a cikin wadata amma sun barmu ba tare da damuwa da muba a cikin duniya cikin wahala duk da nasan hakan akwai laifin umma a cikin hakan don itace ta tafi damu ai. Na koma tambayan kaina me zaisa umma ta bar yan uwanta irun haka har ta shiga duniya damu ta kyalesu na tsawo shekaru haka. Wanan zancen kan gaskiya abin dubawane ga duk mai tunane dole fa akwai wata a kasa da ya jawo barin umma din gida damu. Abincin da ladi ta shigo muna dashi nake bi da kallo tare da gaida ita da gurbatacen hausa na da sannu kawai ba tare da karawa ba. Son umma ta fada min kada in nunawa kowa cewa ina dan jin hausa dagani har Amar din mu boye dan hausan da muke ji a gaban dangin namu. Sai gashi ko farawa da iyawa Asaben ta fita tana fadin ikon Allah yara sun koma kamar wasu kabila haka dasu nikan idan kin kwana yi mun shegeb yaren ku ainba zan gane me kike fada na yarinya. Kallon umma din nayi tayi murmushi kawai mai nuna kin fara gane me nake nufi yanzu ke nan dai daukan abincin naga umma din tayi ta duba. Ta dade tana kallon cikin kulan abincin kamar tana nazarin wani abu kafin ta juyo wurina tana fadin in taso munci abincin da aka kawo muna din na dan bi abincin da kallo kafin in tashi zuwa inda abincin yake. Wanan kan munci sosai don shayi ne da bread sai dankalin turawa da kwai da kosai da koko aka kawo muna abin kari din. Mun gama misalin karfe gomana safe daddy ya shigo har dakin da muke din suka kara gaisawa da umma muma muka gaida shi ya amsa yake tambayan sunan mu muka fada mai sunayen mu. Hjy Addah ce ta shigo falon ganin haka a cikin yaren yarbancin umma tace damu mushiga daga ciki muka mu barsu a falon. Koda muka shiga din hankalina bai kwanta ba don haka na dawo kofa na make ina sauraron su duk abinda ake fada a kunnuwa ina jinsu naji daddy na fadin. Daddy sai a lokacin yake tambayan ta ya bayan rabo mairo ashe kina lagos duk wanan neman da ake maku ?. Kin shige cikin duniya da yara haka kinyi shiru kamar baki da gata haka mairo ai mutum bai yanke irin wanan hukuncin ya tafi shiru haka har wanan dan ma da kika haifa a can gasu yaran gaba daya basu san mu. Gara dai ka tambayeta tun kan zance yakai wirin yan uwa idan wanan yaron dan Sambo nd duk dai ya kwaso zubin gidan mu gaba daya shima don har ince kaf din jikokin baba babu wanda ya kwaso shi da komai kamar yaran nan wallahi. Gara dai da kika ba kanki amsa karshe don ko makaho ya laluba yasan yaran nan jinin gidan mine su don babu ida suka rage gida wirin kama. Da kuma kike zancen wani yace wani abu yanzu wa kike tunanen zan dagawa kafa cikin su a sake wullakanci ga zuri,an sambo kuma ? Wanda dai da akayi mai dashi da iyalan nasa ya isa haka sai dai yanzu a nemin hanyan tuba da gyara gaba kuma amma a yanzu ba mai kara hada kai dani ayi irin shirmen da aka tafka a baya. Ko wancan karon bani nan ne har haka ya faru suka bar kasan bada sani ba aida ina nan duk abinda za ayi saidai ayita amma ba inda zasu tafi a lokacin. Amma Alh ka san yaya Nuhu fa ka kuma san halin sa da kudirin shi akan duk wani wanda ma yai magana game dasu tunda ya dauki abinda zafi sosai haka. Da wani irin kallo ya juyo yana kallon ta a cikin takaci kafin yace shi din Allah ne waliyin Allah da zai saka wani dokan shi na banza yana amfani da mutane kamar wasu jahilai yana kaiku ga halaka. Yanzu din abar min su din a nan gidan zasu zauna tare damu babu inda zasu har sai mai rabuwa ta rabamu ina dai dukiyan daya rike a hannin shi ya zama nasa a yanzu duk yake wa wanan fadan haka ? Yaje yaci ko ince suje suci shida masu binshi a yanzu din Allah ya basu wani wanda yafi wanan din daya rike ina shike nan dai duk dai wanan abu akan abu daya akeyiwa fadan nan kuma sun karba basai a barsu su zauna lafiya ba. Ni dama ai ba wai ina cikin zancen nasu bane kasani amma su yaya din nakejiwa a yanzu don yadda suka dauki zancen nasu na gani. Kuma hakan zai iya jawo su kulla da kai kan hakan don ba kyau kega halinsu ba ka sani don, , , , ke dakata don Allah ya isa haka ya fada a kausashe. Alokacin kuma Abubakar dake tsaye a kofa ya karasa shigowa falon namu fuska a daure jikin shi yayi la,asar don jin abinda mahaifanshi ke fadi. Daddy bai dakata da abinda yake fadi ba a lokacin don ganin Abubakar din yaci gaba da fadin shi Nuhun Allah ne ? Ko yayi kaman Allah a garemu da Allah zai fadi abu saboda wani akidan banza nasa ya sauyawa mutane zancen su don jahilci ko a da can ke kifi kowa sanin bana cikin wanan shirmen ni. Abinda kikewa tsoro dai shine Nuhu ba Allah ba shi Nuhun kanshi ai ya sanni yasan koni waye don haka ne ma zasu zauna anan gidan tare damu babu ida zasu tafi koda ita mairo tace zata bar nan din ba zata zauna da muba yaran nan babu inda zasu tafi sun dawo gida ke nan har abada koda bana raye kai Abubakar karike min su ammana kamar yadda mahaifin su ya bar muna amanan su a baya. Allah ne ya karbi addu,ana har yai sanadin ta tsatsona zasu dawo a garemu da zancen nake kwana dashi nake tashi don nasan Allah zai tambayen mu kan sakacin da mukayi akan yaran nan. Nasan kuma zasu so ja da hakan don su a nan Allah ya ajesu akanyin hassada nima kaina aiba barina sukayi ba na sani duk da kuwa bana shiga zancen kowan su a yanzu. Wanda yace yasan ni inyi dashi wanda baisan ni ba kuma ya zauna lafiya nima in zauna sai zancen dukiyan yaran nan ya zama dole duk wanda yaci dukiyan su a yanzu ya fito masu dashi abasu abinsu. Wanan wani zance kakeson daukowa yaya don kasan yadda ko wurin raba dukiyan man aka samu matsala balle yanzu ace za a bawa masu hakki hakkin su. Allah ya fisu akan hakan mommy hakki kan dole su dawowa yara da hakkin su don sule da alhakin abinsu ba wani ba. Don Allah ku barsu da shi yaya matukar zasu ban min yarana a raye don sun fada sun kara fada a gabana ina jinsu sun fadawa mahaifin yaran cewa zasu kashe shi ko su batar dashi kuma suci arzikin shi.
Chapter 66 · 0% Book details