← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 337

Sashe 5

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

LITTAFIN NAN NA KUDINE YAR UWA KI BIYA DON ALLAH KADA MU RIKE JUNA DANI DAKE AKWAI GOBE YAR UWA, , , ,

Kanta yana duke tana faman kirgan katin dake hannun ta idan bayi missing din wani ba a cikin su biya ya hau kanta ke nan don mai shago baida hasara shi.
Card seller aka fada a cikin wata bakar moto da baka ganin wanda ke cikin ta sai idan ya bude zaka ganshi.
Irin wanda mu hausawa muke kira da motar muggan mutane don ba,a faye yarda da masu irin wanan bakin glass din ba.
Da sauri ta dago zuwa wurin da taji kiran ta tsaya saidai window motar kuma a rufe yake bata kaza ba tana tsaye kafin a kara bude glass din a daidai lokacin da take fadin.
Hurry, up Oga i wan, go nd pray is time for pray now ba tare da ta dago kai ta kalli wanda ke cikin motan ba da gani kuma tana a cikin sauri ne a lokacin.
Don yadda take dan girgiza jiki alaman sauri dai takeyi da gaske taji daga cikin motar ance.
Give me ten thousand mtn card da sauri ta dago tana fadin sir pardon you means mtn card only for ten thousand naira.
Sai kuma ta dan ruga da gudu kafin ta juyo tace i dey come oga i wan go nd bringam now zata ruga da gudu aka kara fadin and eirtel for ten , , , ,
Ai bata tsaya ba ta ruga a guje don tasan duk dadewan ta ba zasu wuce go slow din nan daya jeru a layi ba zata samesu ko gaba ne.
Tana zuwa bata tsaya magana ba ta figo roll din katin don tasan a yadda yake zuwa ta hado dana glo dana etisalat ta juyo da gudu mai shago na ihun fadin you you .
You abi you de crazy today play with my money like that ai bata tsaya sauraron shi ba ta tafi da gudu kai katin wurin motan.
Kamar yadda ta tsamata haka dinne ko sunyi nisa a lokacin haka ta bisu a guje tana kwala ihu har ta samesu ta dan kwankwasa glass din tana fadin here is d card oga all is for ten ten thousand making Fourty thousand Naira.
Ta saka a cikin motan saman jikin mai shi da sauri yace you be mad who ask you to bring all dis daga gefen shi aka miko kudi yana fadin ya bari ta wuce kawai ga kudin ta.
Godiya ta fara sake mai tana fadin oga tank you may god bless all your family and protect dem tana daga masu hannu .
Yau itace farar rana a gareta cinikin dubu arba,in da dan kai haka tasan tana da kudi da yawa ke nan a yau sai lokacin tasan ta gaji sosai ta fara dan jan kafa a hankali zuwa wurin mai shagon data dauko katin ta iske shi ya cika fam yana zaran ido yaga ko zata dawo gareshi.
Sai gata ta bullo gaban shi tana washe baki tare da fadin oga don bese with me na market matter isee that is why a run to catch d money now now i sell fourty thausand own.
Beautyful girl you good wor ya fada yana washe baki a take ta hade rai tunda ya fara fadin hakan ta katse shi da fadin .
Oya give me my share, i wan go home now my mama are wetin for me at home to come with something.
Haba beauty u no go livan till tommorow to get more money than dis one wen i go give u now.
No give me my money today ta fada cikin kara tsuke fuskanta gareshi don ta gane wayau zai mata ga hakan don yana iya fadin ba haka bane idan har ta bari goben yayi.
Don dole ya bata kada ta tara mashi mutane a shago don haka ya debo kudin ta ya bata bayan sunyi lissafi ta tafi.
A hanya sallah ya risketa don haka ta tsaya a wani masalaci nan bakin layi tayi sallah maimakon ta nufi gida wurin da ake sayar da masara sari ta nufa don taga kamat za a caba a wanan sana,an zata gwada ta gani ta dan hada da sayayan dan abinda zasuci ta nufi gida.
Koda ta isa ta samu ana hayani a gidan fada ya hada mijin wata matar gidan tare da iya mulika suna cacan baki kamar zasuyi danbe ga wasu hausawa suna girke a part din su tayi masu sannu ta shige zuwa nasu dakin dake can kurya da gidan.
Ta samu umma da Amar hankalin su a tashe don karo na biyu ke nan umma tana tura Amar zuwa kofa ya duba idan zai hangota dawowa gidan.
A gurguje ta shigo ta gaida mahaifiyar nata kafin ta juya ta fita da sauri alwala tayi a wajen ta gabatar da sallah isha,i dake kanta .
Sannan ta zauna a gefen su tana bude kayan data dawo dashi din ta zaro abincin da tasan mahaifiyar su tafi so tuwo shimkafa da miyan taushe saidai ita da Amar basu damu da tuwo din ba sosai.
Nan umma tashiga tambayanta take bata labarin komai suna cin shikafa dafa duka a cikin take away tare da Amar.
Umma gobe idan Allah ya kaimu masara zan gasa da safe ba zan shiga schoool ba ta fada tana kai shikafan dake shakesu a bakin ta.
Masara Sahiba ina kuma kika kwaso masara tace da kudin dana fada maki na samu a yau di naga an fara wanan sana,an ko ina yasa zan gwada in gani ko akwai samu a cikin sa.
Karatun ki fa Sahiba uwar ta tambaye ta fuska ta bata a lokaci guda kafin can tace umma na dan lokacine wanan tallan ai.

Kaga wanan unguwar mazauna cikin ta yan kazo nazo ne shine mafi hatsarin unguwa a cikin garin nan kaf don in kana neman yan iska a ko wani irin yare kazo nan zaka samesu .
Ya juyo yana kallon mai maganan daga gefenshi sai alokacin ya dan nisa ya juyo yana fadin naga alaman hakan tun shigowan mu ai.
Meye sunan unguwar kai tsaye yace dashi AJAGULE sunan unguwar ai kaga baida wani nisa damu amma yanayin su yasha bambam sosai
Don shi gaba daya erea din yayi kama dana yan duniya tun daga yanayin shigan su zaka gane hakan ai .
Shi yasa ka gani ban faye shigo wanan erea din ba idan ba aiki ya kawoni nan ba sam bana yarda in shigo don sai su nakasa mutum a nan ga banza ba wani aiki bane garesu .
Ai kuwa dai da alama ga zancen ka don yanzu na fara nazarin yan unguwar a hankali simo ya juyo da sauri yana fadin dama kasan wani ne a wanan unguwar ?
Kai ya girgiza yace ai na fadama wanan ne karo na na biyu danazo aiki a lagos yace i see.
Saidai ka shirya gobe iwar haka zamu saje a cikin su don dole mu aje wanan kayan da komai namu mu zama daya da yan unguwar.
Hakan na da kyau ya fada yana lumshe idanu har suka kai inda zai sauka sukai sallama ya fita ya shige masaukin shi dake cikin APAPA.
A gagauce ya samu wuri yayi sallah cikin sane dake kugi ya tuna masa da abinci don tun karin safe yana office suna tsara yadda zasu kamo mai laifin dayazo kamawa din.
Yana zaune a wurin yayi odan abinda zaici wanda ba wani abu bane illa dan ruwan zafi da kayan shayi har aka shigo da abincin yana zaune yana nazari.
Babu abinda yake a zaunen sai nazarin da tunanen ta yadda zai fito wa wanda yazo kamu tun daga wani kasa kuma suke tuhumar yana nan Lagos ya boye.
Gwaunati ta saka hannu ga aikin nasu don a yanzu ne idan yai nasara ga kamun wanan mutum din sunan shi zai yi fice a cikin aikin sa sosai.
Sanin inane lagos yasa ya zauna yake nazarin komai yadda ya dace yasan kowaye zai kama da irin alakarshi da wasu manyan kasan shi yasa akai komai a asirce ba tare da kowa yasan da hakan ba.
Don hakane yake son shiri na musanman akan wanan aiki don ko simo abokin aikin nasa na nan bai san wani shiri da yakeyi ba.
Don simo din ma dan adam ne zai iya juyawa a barshi a ciki tako wani lokaci kuma gashi dan kabalan yarbawa kuma dan kabilan zasu kama ke nan dolene yayi taka tsantsan da hakan.
Mace mace ce ta fado mai a ranshi don haka ya zama dole ya hada da macen to ina zai samota agarin nan ya tambayi kansa ?
Da wanan tunanen ya kwana a ransa yana faman nazarin ta ina zai fara gashi baison Simo yasan komai akan shirin shi din a yanzu.
Chapter 5 · 0% Book details