← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 337

Sashe 12

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bafa wani wuri naje ba Alh na leka gidane in dubusu don an kwana biyu ban lekasu ba. Babu wayane da ba bazaki kirani ki tambayeni ba sai kiyi yadda kika ga dama ko to ki koma gidan naku har ki jini. Alh a kan wanan maganan kake fadin wai in koma gida to kayi hakkuri idan ranka ya baci ta fada tana zama a kusa dashi. A hasale ya juyo yana fadin watau fitan bada izinina ba shine dan magana ko lalai ya kara tabbatar da baki da hankali karima. Shiru tayi kafin ta mike ta fita daga dakin ganin baida niyar yi mata magana a lokacin yasa ta fice ta bashi wuri. Tana fitowa sukai kicibis da hjy Addah wace ta fito daga kitchen da sauri ganin hjy kariman ta ce a, a karima kin dawo ashe ina nan hankalina a tashe tun dazun. Eh na dawo ta fada a gadarance tunda bukata ya biya ai a ce yanzu wai an damu don bana nan to sai me iyaka dai yace inje gidan mu din. Kamar Alh ya sani tana fita daga dakin ya mike shima ya fito yana bayan ta tsaye yana jin abinda take fadawa hjy Addah din. Karima kanki daya kuwa meye laifina a cikin maganan nan ko da zaki fita kin fada min ne amma haka na daure na kiraki ki dawo Alh ya dawo kada hakan ya zama matsala a tsakanin ku. Ummhumm hjy ke nan sai ki samu yara gasu can ki masu wanan dadin bakin amma ai daya fada maki zai dawo baki fada min a lokaci ba sai daya dawo ya samu hakan. Yau wani iskamci kike jine a gidan nan karima Alh ya fada daga bayan ta ta juyo munafucine banso Alh . Ni baka kirani ba amma ita ka kirata ka fada mata dawan ka harta bari na fita bata fada min komai ba don munafuci sai a dinga nunawa mutum ana sin sa a fili. Alhalin zuciya tab da bakin ciki da hassada yakewa mutum a hankali ya tako yana fadin fice daga gidan nan kafin ranki ya kai ga baci yanzu cikin dakewa da nuna shi din tsohon dan kakine shi yayi maganan. Ya juya wurin hjy yana fadin ki hado min abin sha yanzu ya juya zuwa dakin shi din sai yaji tabe a bayan shi tana fadin aikin banza ta wuce. Kamar yadda ya dace a ranan karima din ce da girki wanan matsalan dai ne daya faru ya kawo hakan a yanzu. Ji abinda ya fada sai ta fada kicin a fusace tana hada mai abinda yake sha din daya umurci Addah ta hadomai din ta shiga hadawa da abinci ha baki daya nasa. Hjy Addah tana ganin hakan ta juya abinta zuwa dakinta cike da tunane da takaicin irin wullakancin yarinyar data tsiro ranan. Shima maigidan daki ya koma ya zauna yana bakin cikin abinda ya faru din bayan kamar rabin awa sai gata ta shigo dakin dauke da kayan abinci zata aje yace. Ke dakata waya umurce ki kikawo wanan ko dake nayi dana bukaci hakan ki kwashe kayan nan ki bace min da gani kuma dole yau sai kinje gida ba zaki kwana min a gida ba. To sai me ta fada a hasale tana mikewa tare da ci gabada fadin nasan makircin maza dama ka tayar muna da hankaline don a cuceni. Tunda kasan yau nice da girki ai amma da yake ba ita bace zaka kawo wani fitina kuma . Naji girkine idan ga da,a da biyayya amma tunda yanzu kin isa da kanki ba umurni na kike bi ba don haka yanzu ina da daman sauka a inda naga dama . Ai don ka fadi haka a yanzu banyi mamaki ba don nasan duk abinda kakewa a yanzu kakw hakan don kawai musguna min. Don ka dawo ta baka tsohon abu kayi yadda kake so a ciki zaka zalunceni yanzu ko don an mayar dani ban san abinda ke faruwa ba. Dan murmushin takaici ya sake ba tare daya dago a yadda yake ba yace ke kike ganin shi tsoho don ni a wurina sabone . Don ni tsohon nan yafi min na yar yarinya sharaf don ya wadatar dani komai karima sai ayau nake nadaman auren ki a ruyuwana walh. Tun sunayi suyi kadan kadan har yakai ta fara daga murya hankalin wanda ke gidan a lokacin ya dawo garesu muyi hattara mata fadan mu ya tsaya iya daki da mazajen mu.
Chapter 12 · 0% Book details