← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 337

Sashe 137

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fada yana lumshe idanun shi kafin yace wai dama kece dai din na gani a kaduna tare da sha,aban muyideeen ? Sam ban yarda ke din bace saidai mai kama dake a wurin don hakane ban yarda ke bace da zuciyana ke fada min ke din ce. Excuse me na fada na fara tafiya na bar wurin yana tsaye ya bini da kallon mamaki kafin yace wa na tare dashi su tafi suka bar wajen . Aiki na sama sosai don kwana biyun da nayi ban fito ba saidai haka nayi shi ina jin wani iri a raina ba dadi nasan haduwan mu da Al mustapha din ne ya jamin bacin rai din. Don haka nake duk ranan dana hadu da wani daga cikin su zan yini ne raina na baci saboda mun tashi a rayuwan kadaici da badan Allah ya bamu uwa ta gariba Allah kadai yasan yadda rayuwan mu zai kasance a ciki. Na taso daga a gajiye zuwa gida inda na dan tsaya lagos market nayi cefanen fresh vegetables da nama danya na koma gida dasu don zanyi girki dare ranan. Tun dana doso naga mota a kofan gidan na dafe kaina don nasan mafalikina na jiya ke son zama gaskiya haka dai na daure na karasa na parker motan ina dauko kayan dana sayo ne suka fito daga cikin gidan. Hankalina ya kwanta lokacin da naga Felix ya fito daga cikin gidan namu na dan sake murmushi yana fadin see you from where are you now ? Na share ina fadin Amebo olofofo inda ka aikeni na fito na kara da fadin na dauka baka kasan nan ai har kun tafi ko ? Yace ina oga na kasan nan ba zai koma ba sai munyi bukin zagayowan mutuwan mahaifin shi na shekara da yan dangin su suke yi a zuciyana nace wa iyazu billahi har dake kasan musulunci suna wanan dabi,an ashe ? Yanzun ma naje can office din ku ban sameki ba shine nazo nan don na kira layin ki bai shiga sai lokacin ma na tuna da tun kashe wayan da nayi a daren jiya ban kunnata ba ashe. Akan me kake nemana na tambaye shi yace aikine ya taso muna kan wanan shagalin da za ayi din don haka kinga muna da zama a gobe ke nan daku. Fuskana bata kafin na wayence da fadin Allah ya kaimu goben na dan taka mai zuwa wurin motan shi ya tafi na juya na shiga cikin gidan namu. Nazifa kan abubuwa nason su kwabe mata lokaci guda don in tabi ta mahaifin su shike nan ta rasa uban diyan ta tana ji tana gani don ya hana ta koma dakin ta. Ga abinda kuma mijin nata ya fada cewa ai basuyi fada dashi ba balle ace sai yazo zata dawo asalima da zata zo din yai mata goma na arzki don kada su shigo su wahala a lokacin shi bai kasan tare dasu kuma. Yanzu kuma abin ya koma mata ciki yadda mahaifin ta ya kafe kan wani dalili nasa da su suka kasa fahintar manufan shi akan haka. Yau dai ta rufe ido ta samu mahaifiyar su da zancen komawa ta tace ita zata koma dakin tane tunda tasan halin Abubakar tunda ya fadi hakan bazai taba zuwa ba kome za,ayi ko bazai zo ba tunda ya fadi ta fadi hakan. Kina ganin cewa komawan naki baizo ba shine mafita kinfa san halin mahaifin ku Nazifa haka zai iya jawo muna matsala dani dake a wurin shi. Mama idan na zauna kuma shima matsalan aurena zai samu don haka gara ki bari in koma kawai tunda dama ra,ayinane nazo nan na zauna a gida bayan ya kara gyara min gida kafin inzo. Yanzu ai kinga illan hakan don auren ki ya mutu ba komai bane ga Alh shi don bai daukeshi wani abin kunya ba haka. Ta kasa ba mahaifiyarta amsa sai hawayen da take sakewa kawai a lokacin don yadda take jin kanta kiris ya rage takai ga aikata abinda take ganin zai dace da ita a lokacin. Itama mahaifiyar nata a cikin wani hali take a lokacin don tasan mutuwan auren yar nata ba karamin hasara zai jawowa rayuwan au ba idan auren ta ya mutu a yanzu ta wanan dalilin. Don duk ilahirin diyan gida dake aure babu wace tayi dacen gidan miji irin yar nata shi kanshi majaifin nasu yasan da hakan bakin haline kawai dai irin nasa ya taso. Aikuwa da yamma mahaifiyar nata ta samu mijin nata a falon shi yana waya yana kumfan baki yana mazurai da idanu sai billahillazi bai isa ba shi waye har yaushe yazo kasuwa shi da zai kawo zancen sauke farashi. Wuri ta samu ta zauna a gefen shi har ya gama wayan yana huci tayi shiru bata tanka mashi ha har lokacin daya kare hucin nasa tace dashi sai hakkuri mutane. Yace aisun sanni sun san halina sun san kuma koni waye da abinda zan iya yiwa mutum idan yace zai ketare abindana sharadawa mutum. Jikin tane yai sanyi don jin abinda ya fada a lokacin don ba zata iya fito da zancen daya kawota wurin shiba na yarsu a lokacin. Jin tayi shiru yasa shi kallota yana fadin shi wanan karamin dan iskan baizo ba har yanzu ke nan ta gyara zama tana fadin wallahi baizo ba Alh shinema dalilin zuwana yanzu ai kan zancen. Don Nazifa tace tunda ya fadi hakan ba zaizo gidan nan ba kan maganan nan nasu tunda ba fada sukayi dashi ba tazo nan don haka kayi hakk, , , , Ke salma ki kama kanki da wanan maganan da kike kokarin fada min a yanzu idan baizo ba shike nan a kashe auren mana bashi ke nan ba. Alh har da bakin ka kake fadin auren yarka ya mutu bayan kasan akwai haihuwa a tsakanin su yaran ina za a kaisu idan ka kashe mata aure ? Yayi wani irin juyowa yana fadin yara yarafa kika ce salma yaran dasu taje gidan sa dama ta mayar mashi da tsiyar sa mana kowa ya rike nasa. Gaskiya hakan ba zai faru ba insha Allahu kadaiyi hakkuri kai mai diya mace ta koma dakin ta tunda dama duka daya ake matsalan ka da mahaifin shi ba zai shafi auren yarka ba. Wani tsawa ya jefa mata kafin yace kin ko san abinda kike fadi idan kin mata dako ni waye ya kamata kishiga hankalin ki kinatsu keda yar taki zaifi maku. Mikewa tayi rai bace ta fice falon nasa tana magana ciki ciki ya bita da kallon tsana har ta bace mashi da gani yaja tsuki yana kallon ruwan dake gaban shi. Dakin ta ta koma a cikin bacin rai ta rasa meke mata dadi a lokacin zama tayi tana kallon yar nata dake kwance dunkule a cikin damuwa. Mikewa tayi tafita daga dakin tare da wayan ta falon ta ta koma ta fara neman layin da take son kira har ta samu ta danna kira ba, a jima ba aka dauka. Sun dan dade suna magana da wace ta kira din a wayan kafin ta mike tsaye tana kashe waya tare da sauke ajiyan zuciya. Dakin metting din namu yayi tsit ana jiran aji me zaice damu a wurin game da kiran da yai muna na gagawa kan shirin da yake son ayi din. Shi ya fara gabatar da tsarin shi kafin sauran su kawo nasu shawara duk su dora akan nasa din sai da naji sunyi shiru na dago kai na dan saci kallin su lokaci guda kafin na mayar da kaina kasa ina rubutu. Sam ban yarda nayi wani magana a aurin ba don abinda nake son fadi bai yuyuwa a lokacin don a gauraye muke ga addini sannan kuma su ko musulmai sun dauki wanan da muhinmanci sosai. Har aka gama na tura mashi sakon a nasa sytem din ina jiran su mike nima na tashi Ausa girl you no say anything now ?. Felix ya fada yana mikewa na danyi murmushi ina tashi tsaye tare da kallon su ina fadin Allah ya sadamu da alherin sa na saba jakata na fita daga office din. Tun a mota na fara fada a zuciyana ina faman jin zafin irin dukiyan da suka ware na wanan shagalin kai ina na fadin shirmen banza shirmen wofi mutane ku dinga hauka haka wai al,ada tir da wanan bakin al,adan nasu gaskiya naja tsuki ina kada kai tare da fadin kai ina sam hakama bazai yuyu ba haka kawai ku karawa mamaci nauyi don jahilci. Shiyasa bahaushe ko yauahe yake rena addinin yare don duk yadda kayi dashi sai ya surka hakan da al,adanshi. Bayan na isa gida nayi wanka nafiti banci abinci ba kwantawa nayi don in huta saidai barci ya gagareni a lokacin. Gashisai juyi nake ina tsuki can nayi wani tunane take na mike zaune na jawo wayana don aikata abinda zuciyana ya bani a lokacin. Wayana dauka na zauna na tsara komai yadda nake so na tura sakon kai tsaye zuwa gareshi nayi saurin kashe wayan nawa don kada ma a kira a sameni a lokacin kan wanan karanbanin dayi a lokacin . Sai lokacin naji dan sanyi a zuciyana duk da nasan al,adan sune hakan shawarana ko magana ba shi zaisa su fasa abinda sukayi niyar yi na barnan dukiya ba ga wanda ya mutu din. Na fadakar dashi yin hakan da zasuyi katin wani nauyi ne gun mamacin su kamata yayi su bada sadaka gun mabukata da gidan marayu a cikin unguwa. Ko asai shimfida akai masallataiya da butoci da laspeakee gadai abubuwa nan da dama na rubuta mai na fadarwa garesu da wanan tunanen na koma na kwanta barci. Washe gari da safe ina barci ummace ke tayar dani na dauka zancen zuwa wurin aiki zatayi min har na fara fadin umma yau ba company zani ba. Sai naji tace kina da bako a waje yana jiran ki wai umma waye da safen nan kuma na tambaye ta banga maishi ba dan wajen Abdulhamid ne ya shigo yake fadi. Lokaci na duba a wayana tara saura na safe ashe lokaci har ya ja haka ina kwance na dan shiga bayi na fito na dauki rigan da nayi amfani dashi jiya
Chapter 137 · 0% Book details