← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 229 OF 337

Sashe 229

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari tunda safe na fara shirin don samako nake sonyi zuwa inda na kwana ina kullawa a raina. Koda na fito su umma basu tashi ba a lokacin ko Ammar dake fita school bai tashi ba na bar gidan Allah ya taimakeni na samu mai taxi irin masu sammakon nan na safe nace ya kaini airport. Already Felix yayi min bucking din jirgi tun karfe bakwai na yammacin jiyan na godewa Allah don yan mintuka kadan suka rage jirgi ya tashi na iso. Karfe sha biyu na shigarda kara da taimakon Bello ma,aikacin mu da yazo ya daukeni a airport mukai duk wani abinda zanyi ya juya dani ya kaini airport jirgin karfe biyu muka shiga lagos karfe hudu da rabi ina cikin gidan mu a zaune ba zakace na tafi kaduna a ranan na dawo ba. Gaida umma nayi da gida don a shago na sameta na hausama zuwa part din mu wanka nayi na fito na tayar da sallah ban tsaya neman abinci ba nabi lafiyan gado na kwanta sai barci. Baifi awa daya ba na falka don wayana dake gefena daketa ringing na mika hannu na dauka a jagule a cikin muryan barcin dake idona a lokacin. Harshen yarbanci ya zaunu a bakina na dauka ina tambayan wake magana a cikin yarbanci saida gabana ya fadi lokacinn da naji muryan Daddy a kunne na. Hausa yake min na nuna mai banji me yake fadi ba na kashe layina kai tsaye har wayan a lokaci guda ina jifa da wayan gefe daya. Ido na mayar na lumshe da niyar barci sai kuma barcin ya gagareni don tunane ya rinjayi zuciyana a lokacin don babu abinda yazo min sai mamakin kiran da daddy yake min a wanan lokacin. Shigowan umma dakin ne ya hanani ci gaba tana fadin Ngwa Sahiba yau ki tafi kadunane ko me ta miko min wayan tana mamaki tare da fadin yayan mune ke magana dani. Na karbi wayan a hannun ta na kara a kunnena ina jin dan hayaniya a wurin koda yake min sallama don haka na gane cewa bashi kadai bane a wurin lokacin. Mikewa nayi zaune da kyau ina karba mai sallaman sai gaisuwa daya biyo baya a lokacin kafin yace wani abin mamakine yaji don gasu nan the all family sun hadu ana neman iyayyen su a kotu ranan Monday . Wai nice nake kalubalantar su akan dukiyan mahaifin mu shine daddy ya kira layina ban ganeshi ba an nema daga baya wayana akashe. Sai Umma suka samu yanzu wai ya wanan zancen yake ne ko ina da masaniya nace idan munje kotu zamu hadu a can suji komai amsan dana bashi ke nan kawai a lokacin. Kace ubanta dake kwance a cikin kasa koshi ya taso yayi kadan yace zai wullakantani naji muryan baffah Nuhu na fadin hakana sai dan hayaniya daya biyo baya a lokacin. Recording din wayan na dana tun karbana haka yasa na sauke wani irin murmushi tare da fadin if he insult my father again i know how to handle him i swear will turne dat his folish mouth to his toes. Alh wallahi ka daina don yarinyar nan da ji bata data ido kaji abinda take fada yanzu a cikin waya naji wani murya na fadin hakan ashe baffah hamza ne lokacin rike da wayan daya karba a hannun ya Abubakar din. Ko uwarki mairo tazo nan bata isa ta tunkaremu haka ba hujja ba, , , , , subbahanallahi na fara ji a cikin wayan sama sama iya abinda zan iya karasawa ke nan a lokacin. Ku kamashi mana kada yakai kasa subbahanallahi innalillahi kagani ba kunga abinda nake fadi wallahi yarinyar nan bata tun karo mu ba saida data shirya muna . Duk sun manta wayan yana kunne ake ta wanan hayaniyar wasu na fadin ku kamashi a kaishi asibiti zaifi kada a barshi gida haka don Allah. Dif umma dake sauraren su taji wayan ya mutu lokaci guda gidan baffa Amadu kanin mahaifin iyayyen mu kuma sai ya dauki salati da tashin hankali. Hanklin kowa a tashe yake a lokacin dole asibiti aka nufa da Alh din fitowa magariba labarin komai ya isa kunnen yan uwa don a gaban kowa lamarin ya faru. Bakin shi bude ya shiga common nan iyalin shi sukaji meke faru aka fara fada masu abinda ya faru baffa gyade yana fadi a cikin hasala Saida baffa buhari yace kai gyade ka kama bakin ka wurin nan kada naka ya sameka yanzu kana fama da kafafun ka. Shiru yaran sukayi suna sauraron abinda iyayywn nasu maza suke fadin wai wace yarinya wanan wanda ya kawo min hari ya juya masu a kaduna ya sake tambaya. Baffa gyade yayi mai bayani yace kut wanan yarinyar shu,umace ta gaske yoooo ai shegiyace ta gaske don a shirye take da kowan ku nan ya nuna su da yatsa har yan uwanshi naji haushin shi. Yace ni tsoho ya tura aiki kwanaki wurin ta yasin nayi wata daya ina ganin suranta a mafalkina duk na kwanta barci itace fa wanan, , , Kai ya isa haka don Allah bari muji da abinda ya damemu a yanzu yace alkur,an idan itace tsoho ya kara tabowa yanzu kuma sai kun lalubeta na rantse maku. Idan kuma kun dauka wasane toh ku gwada ku gani aishi tsoho yasan ko ita waye don ya gwada duk sa,anshi a kanta karshe saida ta laishi makargama. Aiko take wurin hayani ya fara tashi wasu na masa kallon mashayi wasu kuma kallon tababe ake mashi baffa hamzane ya ratso tsakiyan dakin yana fadin. Yanzu kun daiji abinda yaron nan kalla,mu ya fada saboda haka a gwada don kallamu yafi mu sanin Alh da komai nasa kun sani. Aiko a gwada din zaifi ya kara fada daga kofa shi kallamu din yana fadin wanan shegiyat kila a indiya take zuwa tsafin ta tunda bata tsoron kuna. Mata gungun su daban mazan ma haka ga matasan diyan su a gefe daya suma suna nasu a daidai wanan lokacin da ake wanan maganan daddy da mommy suka shigo cikin dakin dake shake da yayan fulanin asali na kurnan kaya a can cikin jahar yola wanda suke surkukin daji daba kowa yasan dasu ba sai yan asali. Daddy sun sama baffah hamza na fadin tsiyan abin yanzu ko an kira wayan bata dagawa idan ba wayan modibbo bane. Meke faruwa daddy dake kallon yanayin Alh nuhu din dake kwance shirim saman gado baki bude ya juye ya koma gefe daya sai ya baka tausayi a lokacin don bai san wanda duk ke wurin ba sai numfashi da yakeyi sama sama a lokacin. Yace kun dauka wanan ne dalilin ne yasa hakan faduwane kawai don damuwa da yai mashi yawa amma ai ita yarintane kawai ke cin ta harta furta hakan. Wanan zancen da daddy yayi yasa suka dan lafa amma zagi kan ranan na shashi a wurin wa yanda suke dauka kazafi nayiwa iyayyen nasu a lokacin. Duk yadda daddy ya kira layina kona umma a ranan muki dagawa har na dan nasu Abubakar din ba a daga ko daya kwatsam sai ga kiran dan hjy halira a wayan umma lokaci guda. Nice na daga wayan a lokacin kwana biyu da faruwan hakan tsakanina da Alh nuhu da har lokacin yana kwance a yadda yake. Ina sheda muryan shi na mikawa umma wayan tare da fada mata mai kiran ta din ta dauka suka gaisa da umma lafiya yake tambayana tace gani kusa. Yacewa umma din mahaifiyar shice take magana da umma tace a cikin mamaki hjy hari yace ita gata zasuyi magana. Muryan hjy hari din ne da sallama suka gaisa da umma akayi yaushe rabo don inaga har kuka saida tayi a lokacin kafin ta fara magana akan karan dana saka yan uwan ubana kan gadon mu. Dan murmushi umma ta sake kafin tace wanan zancen sune da yarsu kinsan ita ta gado komai na kakanin ta itakeda karfin halin iya tunkaran su kan wanan a yanzu. Hjy hari tace bazance kada ta nemi dukiyan su ba a yanzu amma komai nason sulhun gida kafin a kai ga hakan. Naso nazo lagos din wurin ku kodan in ganku in saka ahalin yaya marigayi a idona wallahi Allah da ace nasan kuna raye da ba haka ba wallahi. Don haka ku shirya ku zo nan kaduna duk ayita ta kare a zauna a sulhunta wanan zancen don magana ya gama karade garin nan kowa da irin abinda yake fadi akan zancen. Zamu zo ai a cikin satin nan da za,a shiga kotu insha Allahu muna kaduna zanso idan kunzo na ganku kafin kowa don da abinda nake son mu tatauna daku. In son samune zaku iya sauka a gidana idan babu takura kada ku zauna hotel ko wani wuri a,a ki barshi yarki nada gida a nan kaduna da muke zama a cikin sa bamu da matsalan wanan ko kadan. Sunyi sallama an barta da mamaki ashe wai har kaduna din muna zama da sunan aiki amma duk basu da labarin hakan ? A cikin satin sau daya nafita aiki ido yayi min yawa na canzawan da nayi sai kuma ga tafiyan kaduna ya riske mu haka muka shirya tafiyan yamma mukayi muka isa goma na dare don juye mun da akayi a abuja sai muka kara bin wani jirgi zuwa kadunan Belli ne yazo ya dauke mu zuwa gida a lokacin. Ya Abubakar ne ya gano duk kwana biyun nan ina cikin kaduna don haka ya tunkaro gidan namu daya sani kai tsaye tundaga nisa ya hango wuta gidan a kunne alaman akwai mutum.a gidan lokacin . Bai shiga ba ya juya zuwa yayi ya fadawa su baffah hamza da uncle Abdullahi sai gasu tare sunyi sallama muna zaune mun idar da sallah suka shigo. Sau daya na daga kai na kallesu ban sake kallin inda suke suna gaisawa da umma ba sai kokarin shiga daki danayi a lokacin. Ummace ta hanani take min yarbanci idanuwan su tar a kaina suna min kallon mamaki ina saye da dan t-shirt fari mai rubutun da manyan haruffa i wander why na kamfanin Nike sai dan bakin wandon jeans daya tsaya min iya idon kafa ya matseni kaina daure kawai da ribon da
Chapter 229 · 0% Book details