Sashe 17
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Nayi mamakin yadda umma ta yarda ana kashe wanan kudin duk data soki wanda ya bamu shi din a lokacin.
Sai gashi naga tana zara ana sayo duk abinda Amar yace yana sonci don iya sayen abin kaiwa baki kawai muke saye a asibitin.
Magani da allurai saidai muga an shigo dasu dakin ana masa amfani dashi ba tare da mun fitar da kwandalan mu ba anyi amfani dashi.
Yamma yayi karfe hudu umma ta turani gida in dauko muna dan abin bukatan da zamu zauna dashi asibitin don irin fitowan da mukayi koma bamu samu dauka ba dakin muma a bude muka barshi.
Inda Allah ya taimaka ga irin wayau na duk da rudewan da nayi a lokacin bayan naga umma ta fita da Amar a rude sai dana koma na kwashe dan kudin mu dake dakin a lokacin.
Don nasan yadda akeyi a gidan da zaran dan tafiya ya kamaka kayi kwanaki masu dan tsawo baka dawo ba sai abi dare a fasa dakin a kwashe ma abin kwarai a dakin masu amfani .
Wanda sanin hakan yasa farga na kwashe kudin na tafi dasu a cikin aljihun rigan dake jikina wanda sai wanan lokacin nake tuna hakan.
Abinda na zata shine ya faru don na samu har dan raggan katifan da umma da Amar ke kwana a sama andaga a dakin kai ba katifan bama har ledan kasa an daga wanda nasan kudi ake nema a dakin don mu bamu da wani abin jin dadi na zamani a dakin na kudi.
Fada na fito waje ina yi a cikin yarbanci ina zage zage ina hadawa da turancin brokin a bakina wanda su suka amshe bakina wajen gwanewa.
Ba wanda ya tanka min don hakan ne wasu ma basu gidan basu dasowa a lokacin daga kasuwa da sauran wajajen balaguron su.
Gidan babban gidane zai mutane saba,in zuwa tamanin ke rayuwa a cikin wanan gifan da baifi mutum goma su zauna suyi rayuwa a cikin saba a arewa.
Na karaci fadana na tsunci yan raggadun mu da yan plate na jawo kofan don bamu da kwado na rufo na nufi titi.
A hanya muka hadu da iya mulika take tambayana abinda ke faruwa na fada mata tace in gaiyar mata da umma da Amar din.
Har take ban shawara tunda muje asibiti muyi kokari umma taga likita asan abinda ke yawan damun ta datake faman ciwo haka.
Naji dadin wanan shawaran na iya mulika din don duk fadin gidan ita kade ta nuna muna damuwanta a kan mu.
Na koma nake ba umma labarin halin dana samu dakin mu a ciki ta bugi kirji tana fadin aiko mun shiga uku dama tayi tunanen hakan tun dazun.
Shike nan an kwashe dan kudin da mutumin can yabaki shekaran jiya kudin bai amfane mu ba na tsaya dogon guri dashi.
Umma ban bar dakin mu ba saida na kwaso duk dan kudin dake garemu na hado da wanan din don nasan akwai matasa a gidan masu shiga dakuna idan mutum bai gida.
Sahiba kin kyauta muna da baki bari an sace wanan kudin ba yau umma ina zan bari tunda shi nake son muyi amfani dashi wuri ganin likitan ki kadin mu bar asibitin nan.
Sahiba yadda nake jin jikin nan yanzu ina mukaga kuflfldin da har zanga likita ko na yaron nan ai Allahne ya kawo muna mafita a kanshi.
Gobe dai sai muje mu yanki kati umma kema a dubaki tunda gamu a cikin asibitin ko iya mulika yanzu saida ta kara ban shawaran hakan kuma tace na gaida ke.
Mun bar wanan zancen a kan gobe zamu ga likita ashe likitan yakan zagayo duba marasa lafiya da dare da rigimana nan na jefo mai zancen umma din.
Saida ya dan kalli umma inda take zaune din yake fadin sai mu yanki kati a goben mubi layi Allah ya kaimu umma ta fada da hausa.
Nan ya barmu ya fita bayan ya gama dan dube dube da tambaya akan jikin Amar din dake kwance yana barci.
Abincin dana sayo muna da zan dawo shi umma tace na diba naci kan na kwanta tunda tasan a gajiye nake dai umma ta mance irin jigilan da nakayi a duk wunin Allah.
Ban kaiga tashi a wurin ba don na tsaya ba umma labarin yadda na samu an burkuce muna daki har ledan kasa.
Wata yar nurse tayi sallama dauke da ledan abinci da abin sha ta shigo dakin duk muka bita da kalkon mamaki.
Tace a cikin yarbanci iya Amar ko ?
Umma tace ahmi tace ga wanan ance na kawo maku inji wanda ya kawo ku ta aje tana fadin manbo, wa ta fita sai gata dauke wani katon kwali mu dai muna binta da kallo kawai har ta aje.
Tace duk shi yace na shigo dashi yana zuwa zaiga likita eh, kwale data juya umma ta fada don nikan nagama shan jinin jikina a lokacin don nasan wani fadan zansha kuma a hakan.
Kodan ance wai yana zuwane bata furta komai ba sai bin kayan take da ido tana ajiyan zuciya ga tagumi data hada tana umm,, , ,
Shiru har dare ya soma yi alokacin nakai kasa na soma barci don yau gamu ga fanka a dakin zamu kwana dashi kamar kowa a dakin nan da nan jikina ya mutu na fara gyangyadi har nakai kwance.
Umma ce ta tayar dani naci abincin duk da taji tsoron cin namu amma saidai kuma zuciya naso don lafiyeyen abincine koda ba a bude ba duk kamshi ya bure dakin ko a lokacin.
Saida ta dan kira sunana kamar sau uku na amsa tace a cikin yarbanci na tashi naci abinci kada inyi barci banci abinci ba.
Na tashi na shiga ban dakin na kurkure baki ba na fito na zauna na dan kali umma nake fadin umma ba zakici abincin bane ke ?
Tace sai zuwa anjima kafin mun kwanta zanci na jawo kedan na fara fito da take away din nan mai tsada na dan kali umma tayi kamar ba kallona takeyi ba.
Saida na debo abincin naji umma na fadin indaici da bisimillah don bzmu san manufar su akan mu ba.
Hakan nayi da murna a zuciyana da yau banji umma tayi wani fada ko maganan da zai ban tsoro naji abincin ya fita min rai ba.
Naji dadin sakwaran da miyan egushi da naman shi kamar yanka duk da yajin da miyan kedashi haka nayi taci don yaji kan mun saba dashi mun tashi a cikin cin sa tunda muna garin yarbawa.
Aka turo kofan da sauri muka dago don ganin waya shigo wata nurse ce dauke da file tace umma ta bata cikakken sunan ta likita yace da safe akwai awon da za ai mata kada taci komai har zuwa safen.
Har zata fita umma take tambayan ta kudi nawa za, a bayar tace maganan likita ne wanan ba nata ta fice ta barmu da mamakin hakan don sanin halin asibiti da mukayi muna jin rashin nasihan da akewa marasa lafiya idan basu da kudin ganin likita.
Mu sai gashi anzo kawai wai umma ta fara shirin za ai mata aune aune zuwa safe din.
Abincin ne yafita min a rai duk da son da nakeyiwa abincin don dadin shi amma haka naji komai ya tsaya min cak lokaci guda.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , , , ,
8️⃣
BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM SIRA,ATAL LAZINA AL,AMTA ALAIHIM, , , ,
BARKA DA JUMMA,A YAN UWA
PAID NOVEL BY MAKAWA, , ,