← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 337

Sashe 141

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fadin shi zai tafi sai ya sake dawowa insha Allahu zai shigo ya kara ganin mu. Wanda har lokacin ban kara masa magana ba ko kallon inda yake ya daga daga zaunen da yake umma ta kalloni tana min signal da ido nayi saurin fadin mungode ya Abubakar. Yace No kada ku damu wanan duty nane in kula da ku don ku din yan uwane sosai a gareni don haka ba zan kara barin ku ba kuma insha Allahu ya fada yana taba kafadan Ammar Hannu umma ta daga tana fadin amin wooo amin mun gode nikan hankalina na mayar kan wayana na nuna ban ma san yana falon ba a lokacin. Wanda sam bashi ba ko umma hakan da nayi sam bai mata dadi ba don ita a nata taso muyi haba haba da shine mu nuna ina aka saka dashi don zuwan dayayi wurin mu din. Niko a yanzu kaf din su a matsayin makiyan mu nake daukan su dan yadda suka barmu cikin diniya a watse babu kulawa lokacin da muke da bukatan hakan garemu. Bayan sun fita umma ta dawone aiko ta hauni da fada wai ban kyauta ba da ban rakashi ko nuna kulawana da zuwan shi ba . Shiru nayi ban dago kaina ba balle in bata amsa don nasan abinda zan fada ba zai mata dadi ba shine kawai nayi shiru a lokacin. Suna zaune a gaban tsofin suna mayar da magana bayan sun gama saurare dayan tsohon yace su barshi dasu kada masu nuna cewa sunzo wurin su don tasan halin mijin nasu karyazo ya zama matsala a tsakanin su kuma. Ta dawo gida Allah ya taimaketa ba wanda yasan fitanta har ta dawo don kowa na part din shi a lokacin don haka babu mai tseguntawa mijin nasu fitan ta. Duk da Allah ya dorata a kanshi yana dan daga mata kafa ita don yana son ta ita ba auren su na filani yayi da ita ba. Wurin barikancin su can ya hadu da ita ya auro ta don yaso kawai suyi zaman banza a watsene sai gashi har abin ya kaisu ga aure tsakanin su. Akayi kuma sa,a yana ji da ita sosai cikin iyalan nasa don tayi iya harka dashi yadda yake so saidai duk da hakan idan halin shi ya motsa yakan mata rashin mutunci sosai. Basu zo ba sai bayan kwana biyu da zuwan salma din gidan su saiga tsofin sunzo su sameshi a kan zancen yar shi din da dan wajen dan uwan nasa Alj Ali dcp. Da farko fada ya soma yi yana fadin shi za a kawo iskanci yaro yayi ba daidai ba zaice yana son ganin shi zaice aiba fada sukayi da matar shi ba balle yazo ya ganmu. Kai jam jam jam Nuhu wala hankali o da ace yau Namadine ke raye zai shiga zancen zurian ku har zaka iya musa mashi. Dayan kuma yace amma Nuhu ka ban kunya da mamaki ni da nayi bugun gaba ina fadin acikin kaf babu mai jin maganan mu da girmamu sai kai don haka ba zamu samu matsala wurin ka ba na bada wanan shedan a gaban yan uwanka. Son girma da yabo gareshi don haka tsohon na fadin haka kanshi yayi girma ya fara fadin ba hakana bane baffah yaron ne yake da girman kai da izza irin na uban shi yasa nake son nuna masa shi ba kowa bane wallahi. Shi kowane kuwa, dayan tsohon ya fadi yayi saurin kallo shi yace kwarai kana matsayin mahaifin shi kuma surukin shi zakace baida kowa shiko keda kowa a garin nan tunda har gaku iyayayyen shi da rayuwanku. Sai yayi shiru kamar yana nazari kafin can yace dasu naji baffah na kuma gode da zuwan ku gareni in Allah yaso zata koma idan na kimtsa. Haba Nuhu haba dai ai kamata yayi tunda har kaji maganan kuma ka yaba da zuwan mu a matsayin mu na yan uwan mahaifin ku ya kamata ne ka bamu dama yanzu mu mayar da yarinya dakinta tunda ba fada sukayi ba sukace. Ya kara yin shiru na dan lokaci kafi yace kada fa hakan ya jawo mata gori a wurin shi nan gaba yan tsofi har suna hada baki wurin fadin haba haba sam bazaiyi haka ga yar uwan shi ba ai. Nan dai sukai mai dadin baki da bashi girma har dai yaji ya zugu yace a shiga ciki ai mashi magana da hjy salma karshe ma dai shiya mike sai ganin shi kwatsam sukayi yana fadin Nazifa ta fito ta koma gidan ta gasu baffah a waje suna jiran ta yanzu. Komai dama ita Nazifa din ta gama shiryawa tana batun sulalaewa ta mayar da kanta gidan tane koda iyayyen nata basu yarda ba sai gashi Allah ya kawo saukin abin manya sun gyara zancen. Sun isa gida saida suka buga maigadi ya fito a bakin shi suke jin cewa maigaidan yayi tafiya a safiyan ranan ya tafi. Allah ya taimaka makulin daya bata da zatazo yana hannun ta shi tayi amfani dashi wurin bude kofan suka shiga tare da dan mata nasiha kan zaman aure ta daina daukan zance tana kaiwa mahaifan ta. Badon Allah ya gyara uwarta tayi dubaran tun karansu ba auren nan babu abinda zaisa ba, a rabashi a wanan lokacin tunda kowan su yahau haka. Ba gida suka nufa ba gidan hjy Addah suka nufa don sun san ba lalai bane su samu daddy a gida lokacin tundashi ba mazauni garin bane shi sosai. Sun sameta sun mata bayanin duk abinda ya faru sun kuma ce idan moddibo din ya dawo a yasamesu sukai mata sallama ta kawo masu abin arziki tayi masu sallama suka tafi a cikin dadin rai. Washe gari koda na tashi nayi sallah kamar kullun na dauko waya na samu sako daga Oga Sha,aban cewa na sameshi goma na safe. Nayi mamakin ganin wanan sakon duk da nasan hakan nada nasaba da sakon dana zauna na tsara mashi ranan . Saidai ina tamtama a zuciya ko hakan ya zama laifi a gareni ke nan a yanzu don haka korana ko warning dina zaiyi don da dukan mu yake nema dole Felix ne zai nemeni. Don haka sai tsoro da fargaba ya kamani lokaci guda a cikin raina daidai ba yadda na iya haka na tashi na shirya bayan na fadawa umma zan fita ana neman mu nayi mata bayanin kan bukin mutuwan da za ayi din asabar mai zuwa. Itama dai bata goyi bayan wanan dabi,an ba nasu saidai tace nayi taka tsantsan da aikina a gama lafiya kowa da nasa irin al,adan tunda na saba ganin yadda sukeyi lokacin da nake talla har pure water na leda dana gora muna kaiwa a wurin mu saida masu a ranan muna ciniki sosai idan ana taron. Nagama shiri cikin atamfa dana dinka buje da riga na dora hijab a saman dan kwalina kamar yadda na saba idan zan fita. Na isa katafaren gidan nasu ban samu wani matsala ba son a yanzu masu aikin gidan sun saba dani ko don ganin mu tare da sukeyi lokaci lokaci. Wanda ke tsaron kofab shiga falon shi na tambaya idan oga ya fito ya sanar dani cewa yana ciki yau tun safe yake karban bakin shi. Kafin in shiga saiga Felix ya iso wurin tun dags nesa yake washe min baki yana fadin wa nake gani kamar beauty don haka yake kirana idan ya tashi min sheri. Har ya iso inda nake yana fadin kai kai kai kinga yadda kika hadu kuwa kamar wace zata gasan kyau haka gaskiya kayan nan sun matukar karbi jikin ki sosai. Na watsa mai harara ina fadin kaifa baka rabuwa da zolaya ni bashi ba don Allah kiran me oga ke min a yau kuma ? Kafada ya daga tare da ware hannayen shi yana fadin ni ina zan sani yarinyar Oga na sani ko wani sirin zaku tatauna a yanzu wanda baku son kowa ya sani. Sake hararan shi nayi ina nufan kofan sai kuma naja na tsaya don ban yarda ya sakani gaba ba haka shi yana bayana ba. Muje mana ya fada yana nuna min kofan nace ka fara shiga kayi min iso sai na biyo ka a baya ya kwashe da dariya yana tura kofan. Bayan shi nabi muka shiga banyi zaton yasan ina bayan nasa ba saida nayi sallama cikin zazzakan muryana duk da bana ji koda ya amsa min saboda girman falon da nisan da muke dashi a tsakanin mu. Waya yakeyi ga wasu tsofin yarbawa guda biyu zaune a gefen shi da irin rigan sakin nan nasu nada a jikin su cikin natsuwa nake tafiya har na dan karaso inda suke suna bina da kallo a cikin harshen yarbanci na gaidasu suka amsa . Felix ya nuna min wurin zama nakai zaune shima ya zauna daga barin gefena na hagu har lokacin tunda yai muna kallo daya ya dauke kanshi bai sake kallo inda kowan mu yake ba. Kaina a duke yake ina kallon zanen kafet din da aka malala saman ties din falon mai ban sha,awa zakace hakine ba sakashi akayi ba idan ka ganshi don kyau. Jin yayi shiru ya gama wayan yasana dago kai don ganin me yakeyi muka hada ido dashi a daidai lokacin da yake mikawa tsufin nan kudi. Da sauri na dukar da kaina a cikin kunya kamani da yayi ina satan kallon shi shima idon nasa ya kawar yana magana da tsofin a hankali duk da muna falon ba zamu iya jin me suke fada ba a lokacin. Tsofin suka mike suna mashi sallama kafin su juyo garemu suna muna sallama nabisu da idanu har suka bacewa ganina na nisa ina juyowa gare su.
Chapter 141 · 0% Book details