Sashe 251
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
a kotun haka akaiwa daddy din shima tambayan bayan an karanto mashi laifin da ake tuhumar su dashi din. Ya dan girgiza kai na dan lokaci saida ya danyi dan shiru irin na manya kafin ya dago kanshi yana fadin zan bayar da sheda akan abindana sani iya gwargwado in Allah ya yarda. Kamar yadda kowa ya sani marigayin abokinane sosai kuma kanina aminina haka muka taso dashi a gidan mu yai rabin rayuwan shi kaf kafin ni na fara aiki shi kuma saboda kwazon shi gwautin jaha a lokacin ta turashi karatu waje. Bayan ya kammala karatun kuma yazo ya samu aiki a can sai rayuwan shi kancan kaf ya koma can waje saidai kaf din mu yan family din mu dani yafi yarda . Don haka yana turo kudi nan ina masa tanadi kamar yadda kowa ya samu akeyi har wani tafiya da yayi ya samo wasu mahaukatan kudi ya turo na sai mai filaye manya kudu uku masu girma. Wanan ne abinda ya fara jawo muna matsala a tsakanin mu nidashi don yace zai yi manyan gidajen mai irin na waje na nuna mashi ba haka ba komai a sannu ake binsa. Duba ga yadda yake matashi a lokacin ko aure baiyi ba tun daga wanan lokacin ya fita zancen filin kuma bai kara min maganan shi ba har sai bayan yayi aure har matar ta haihune yayi wani fita sai gashi wanan fitan ya dawo da mahaukacin kudi irin na wancan shekarun. Sai a lokacin ne ya samu waiwayan filayen shi ni kuma duba ga yadda muke dashi lokacin har na taba filin nayi amfani dashi wurin nawa bukatan. Na nuna mashi lokacin kwara daya ya rage a cikin filayen kuma shine mafi girman aka a ciki take ya nuna min nacin ranshi ya dai wuce a hasale abinda bai taba min ba. Nima nasan ban kyauta ba gaskiya sai hakan ya dan fara jawo matsala a tsakanin mu dashi ya daina kulani ya daina dai yi dani kamar farko. Wata rana ina maiduguri nazo weekend da yamma yan uwan haihuwan shi su Nuhu suka sameni bayan mun gaisane suke fada min ai sunzone su kara ji a bakina wai ashe Sambo shike da wanan katon filin na hanyan fita gari nace eh ai wanan bashi kadai bane ma akwai wasu filayen bayan wanan kuma manya ne suma . Nan muka buge da fira dasu abinka da dan uwa nan nake ta labarta masu irin dukiyan daya samu da abubuwan da yake dashi. Allah ya gani ban fada don wani abu ba lokacin amma bayan kwana biyu sai ga Sambo din yazo min rai bace yana fadin bai taba zaton zan masa hakan ba. Don me zai bani amana kuma inci inje ina fadan duk wani siri nasa ga jama, a a lokacin dai dukkan mu kurciya yaci mu don nan muka rabu baram baram dashi kowa na fadawa dan uwa bakar magana duk irin hakkurin shi ranan bai raga min ba. Bayan munyi hakan dashine da kwana biyu muka wayi gari an kashe shi saidai amatsayina na dan sanda binciken farko na gano cewa yan uwane suka halakashi lokacin. Nayi yunkurin yin wani abu sai ga batar matan shi abinda ya kara daga hankalin kowa na ahalin mu ke nan kuma . Shiru har wata uku babu labarin ta sai ranan sukazo suka sameni da zancen tunda Sambo ya rasu iyalin shi kuma sun bata abinda zaifi a raba dukiyan shi kawai tunda dukiya bai azuwa tunda ba, a san ranan dawowan iyalin shi kaduna. Haka yasa na kara zargin su na kirasu a sirce nayi masu magana sai suka so su mussanta hakan karshe dai da sukaga na gane gaskiya duk da basu fito filin sun amsa laifin su ba lokacin. Sai cewa sukayi in ma son dukiyan shi dake hannunane banson in bayar in tafi da dukiyan in rike amma sai na basu wanan filin ko kuma dukkan mu a tuhumeni nima. Inda ni kuma naga hakan ba karamin banan suna bane a wurina yasa naja bakina nayi shiru a lokacin tare da fatan duk lokacin da wanan case din zai taso ya kasance ina raye a yishi . Don a yadda na kula Nuhu dai gashi nan tsaye idan bai ci arzikin nan na Sambo ba zai iya samun matsala lokacin don yadda yabi ya zare kan abinda dan uwan nasu ya bari kuma a yanzu bashi da wanda zaici sai su din don diya mace ce ya bari a duniya a zaton mu. Sai dai duk da rufe wanan case lokaci zuwa lokaci nakan tuno da wanan nauyin dake saman kan mu don haka na samu lokaci na ware daga cikin dukiyana iya abinda nake ganin nasune a wurina na debe masu shi. Amma kuma daga baya sai kuma na fara wasu harkala da kudin sai dai ban yarda na hadasu da nawa ba har lokacin . Kwatsam wata rana saiga iyalan marigayin sun sauka a gidana dana daya gano su a lagos yazo dasu. Nayi iya kokarina wajen yin shawara da zuciyana in baiyana din na boyesu ga kowa a lokacin suma kuma din na hanesu da baiyana kansu ga kowa. Nayi kokari a lokacin naga na hada kan dukiyan su in basu saidai na kasa hakan a wurina gashi lokacin na fahinci su Alh nuhu kamar zasu gane su kashe su ni kuma bazan so in zama sanadin hakan a garesu ba lokacin. Yasa na umurci dana da na shirya wa plan cewa ya kwashesu ya mayar can lagos din har zuwa lokacin dani zan shirya fitar masu da dukiyan su in danka masu a hannun su . Sai kuma rai da dukiya wanan yasa na sha,afa da zancen su gaba daya don kudin da yanzu nake juyawa sai ga wanan zancen ya taso don haka naaan za a kawo kaina yasa na tsaya saida na cire masu komai nasu na dawo da shirin danka masu abin su a yanzu. Humm, umma dake gefena ta fada tana dan jijiga kafanta a cikin takaicin jin wanan cin amanan da tasan duk shirin magana ce kawai don ya kare kan shi a yanzu daga tuhuma. Saukin shi dai dayane shine baya cikin kisan amma makushe dukiyan harda shine don ai bai taba fadawa kowa wanan zancen ba haka sai yau.