Sashe 313
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zubur na mike zaune don tunawa da inda nake kwance a lokacin jin motsin mutum a bayana yasa na juya da sauri shine azaune saman gadon nasa da nake kwance a dakin. Yana zaune ya tasa laptop a gaban shi yana aiki a cikinsa kokarin tashi nayi zaune naji yace lokacin sallah bai karasa ba da saura a nan. Don haka kwanta ki huta kinada sauran lokaci har yanzu na hutu is just past twelve now duk maganan da yakeyi hankalinshi nakan aikin da yakeyi a lokacin bai daina ba. No i want to easy myself na fada a dan kunyace naji yace you can go ga bandaki nan a nan kaina girgiza masa tare da fadin zan tafi wurina in kewaya daga nan na duba fatima. She is OK here so kada ki damu da ita but you can go don naga you are not safe here yadda kika tashi a firgice din nan . Kunyan kaina naji don nagane ya kula da yadda na lalubi jikina bayan na waiga na ganshi zaune yana aikin da sauri nakai hannuna saman jikina najini nade a cikin lafayana dana kwanta har lokacin dashi. Kunyan kaina naji ga fahintar abinda nayi din saidai na basar haka na mike ina gyara jikina kafin na waigo ina fadin nagode na fita zuwa waje. Gidan shiru babu kowa a main falo din da zai sadaka da sauran part din gidan sai karan nauran dake aiki a lokacin gashi kuma an gyara ko ina sai kamshi ke tashi duk illahirin gidan baki daya. Fitana yayi daidai da sake danna mashi kira da hjy falmata tayi a lokacin wanan karon ya dauka kafin ya katse babu sallama sai cewa tayi mukhatar ina ka shigane tun dazun na kira kuma baka dauki wayan ba ? Kai tsaye ya bata amsa da fadin ina gidan amaryane ba tare da jin wani nauyi ko kauce kauce ba ya fada. Ashar ta lalaiyo ta kundumawa gaba dayan mu lokaci guda duk da mamakin hakan ya kamashi amma haka bai hanashi sake dan murmushi ba tare da fadin mun gode ya kashe wayar. Nan kuma wani haushi ya sake kamata lokaci guda ranta taji ya baci ga baki daya idon taya rufe wani bala,in kishi ya danne mata zuciya. Mikewa tayi da tare da figan dan gyalen kayan jikinta da zumar ficewa gidan zuwa gidan da akai mata kwatancen nan ne gidan da nake. Kannenta na ganin yadda ta fito suka tsare ta da tambayan ko lafiya muka ganki haka hankali a tashe zaki fita ba tare da kowan mu ba ? Zanje gidan wanan yar iskan naci masu mutunci don naga tun yanzu suna son raina min hankali ganin irin kallon bamu gane wa kike zance a kaiba da suke mata yasa tace a hasale gidan Amaryan wanan munafukin mukhatar man. Ehyyah anty please kada ki badamu mana tun yanzu mutune su samu abin fadi a kanki jiyan nan fa ta tare a gidan yau kuma ace kinje kina masifa ? Koma meye ai dole ya dawo gidan nan ya sameki babu ruwanki da ita a yanzu don game din ai bai fara ba ko tunda baiko kwana a wirin ta an gani ba amma yanzu da kije an samu abinda ake jira a kanki ke nan ai. Wani kallon hasala ta watsa masu kafin tace dasu a fada mana na isane idan da ban isa ba aiba zasu fada ba tana magana a hasale cikin yaren kanuri. Kwat ba zamu bariki ki fita a yanzu ba karamarsu ta fada daga inda take fitan kina nufin zubar da kiman kine a idon mutane ai basai kinje kin sameshi a can ba dole dai ya dawo gidan nan komai tsiyan su eh,heh. Ranta ne ya kara baci sai kawai ta nemi kujera takai zaune don kafarta bazai iya daukanta ba yadda takeji. Shima brother wani irin zuwa gidan amaryane yanzu da ranan nan haka aina zata saida darene zai tafi can din yau ko ta kalli yan uwan ? Shine ai kawai dai halin maza yake son ya fara nunawa tun yanzu waishi ga mai amarya wanan farin fatan yake rudin shi kome a jikinta mace hakama ba wani fasali gareta. Kallonta yar uwan tayi sai kuma ta kumshe dariyan ta dake cinta kada yayan nasu dake zaune hasale tace bata damu da damuwarta ba ita . Amma da badon hakan ba data bawa yar uwan nata amsa da cewa ki kalli kanki keda kike baka kirin ba fasaline kike zagin wata haka wace duk da a rufe muka ganta alama ya nuna cewa ita din mace ce har mace fuskantane kawai basu gani da kyau ba. Gashi duk wani memo din buki iya hannayen su a hade kawai ake nunuwa babu fuskokinsu a jikin abubuwan da aka raba na bukin. Wanan kuma duk aikon sister ce don bakin sanin da tayiwa hjy falmata din ko a photo zata iya shanmatan mutum karamin aikintane wanan din. Sanin hakan yasa sister tasa komai da aka buga bata yarda anyi amfani da photun muba a ciki amma duk da hakan saida suka gane dalilin sister din. Da kyar dai suka samu ta koma daki bayan sun gama surfa muna zagi ta uwa ta uba cikin ma wai basu da tarihina ke nan amma duk da hakan saida nasha zagi iya inda suka tsaya. Shima a nasa bangaren abinda ya guda ke nan tun farko bai daga wayan ba tunda ina dakin ina barci lokacin yasan zatayi mai fitina sai bai dauki wayan ba don kada injisu. Hakana rai bace ya fito zuwa sallah daga masalacin bai dawo nan ba gidan mahaifiyarshi ya nufa suka gaisa nan take fada mai su gwaggo sin bugo waya sun isa lafiya suna godiya kan karamcin da akai masu . Alhamdullahi ya fada dan jin sun sauka lafiya kafin ya mike yana fadin zai karasa gida tun safe daya fito rakiyan su bai koma gida ba. Har ya bada baya yaji hjyn na fadin kadai san yau a wurin sahibs zaka kwana ko dan ina tsoron halin da falmata ta fito dashi yanzu kan auren nan. Yanzun ma daga gidan ta nake ya fada tare da dan juyowa yana fuskantar mahaifiyar nasa yaci gaba da fadin tundana raka bakin nan airport ban koma gida ba har yanzu shine ta bugo waya tana surfa min zagi waini dan cin amana azzalumi tun yanzu na fara da hakan dukkan mu zatayi maganin mu ai dagani har sahiban . Ka gani ko wanan dalilin yasa banso zuwan falmata wanan sha,anin ba tunda bata kasan nan sai gata kamar an jefota saukin abin ma dai anyi an gama lafiya bata tada wani fitina ba a gaban mutane. Murmushi ya sauke a fuskanshi yace Allah dai ya sauwaka dadin abin ma anty hafsat tana wurin itace ke hanata yin wani abin idan tasoyi. Nima zuwan hafsat din yayi min daidai tunda na ganta sai naji dadi a raina amma bayan ita ai duk sauran irin su daya da falmata din kamar ba Lamice ta haifesu ba. Ni zan karasa yacewa mahaifiyar nasa kada ka biyewa shirmen ta don yanzu an tabata komai zata iyayiwa kowa musanman ma kai da kaimata laifin. Ya kara dan murmushi yana shafo fuskanshi a hakan ya fice daga gidan mahaifiyar nasa tabishi da kallon tausayi don har ya fada ya danyi baki tasan shi shi mutum ne wanda baison yawan hayaniya dama. Suna falo har ita ya shigo tunda ya hangosu ya daure fuskan shi tafiya yake a natse yayin da duk suka bishi da kallo saidai ita madam din ko kallo bai isheta ba. Da kyat dayan kawar nata ta iya budan baki tace dashi sannu da dawowa ya amsa mata ciki ciki yana jin madam Falmata najan uban tsoki yasa kai yayi part din shi. Yana shiga kwanciya yayi a yadda ya shigo dakin takalma kawai ya iya cirewa a lokacin tace ba abinda ke yawo a kunnen shi sai kalman azzalumi data kirashi dashi. Ta ina ya cuceta har tayi mai furcin wanan kalman mai muni haka amma zai nuna mata tayi babban kuskure kan fadin hakan . Shi duk sauran babatunshi bai taba damun shiba a yanzu amma wanan kalman na azzalumi shine ya tsaya mashi a rai yanzu. Yaso ta bashi hadin kai a zauna lafiya a yadda ya fara fahintar sahiba da alama tana da saukin kai tare da biyayya ba kamar yadda ya zata zaisha wahala a kanta ba. Kofan ta turo a fusace yasan itace don ita kadai ta isa ta shigo mai daki a yanzu kuma koda bayab shine don ds farko ta dauko kannen nata su shiga amma ya takawa hakan burki sun daina a yanzu. Ka dawo daga cin amanan naka ai sai ka koma can ka karasa don kwananta ya fara ke nan daga lissafina bazan yarda a kawo min wanan cin amanan ba a ha,inceni kan wata can da bata da asali. Sai lokacin ya dago da mamaki karara a idon shi ya sauke a kanta kafin yace Falmata kada in kara jin kin kira wanan yarinyar da mara asali koda kuwa a gidan karuwai na dauko ta. Ai kinfi kowa sanin tana da asali asalin ma da yafi nakowa tunda ke din shedane da arzikin mahaifinta nz gina nawa a yanzu. Kin sanin kinsan gidan mau me nake dashi kome ke akwai a gidan mu dacan baya lokacin da kika fara guduna don bamu da komai ? Yanzu kan itama din da mamaki ta fara kallon shi kafin tayi karfin halin fadin au ashe don dukiyan mahaifinta ke nan ka aure ta ? Yes of course don shi na aure ta saboda itama din dorne ce tana da kudin ta tana da kaddarori ga ilimi kinga ashe ba don kudi ta aureni ba sai don biyayya ga iyayye. And by the way kalman azzalumin na kada in kara jinshi a bakin ki me na rageki dashi a rayuwa ko me na ha,inci rayuwan ki dashi don kawai na kara aure a yanzu shine zaluncin nawa kome ? Ko nayi maki alkwarin cewa zan zauna dake ke kadaine a rayuwana bazan kara aure ba me kike so a rayuwa da ban maki shiba. Nakai kowa naki