← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 337

Sashe 124

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kuma. Daddy bai tanka ba yayi shiru kamar mai nazarin wani abu itama dai shirun tayi na dan lokaci kafin ta mike tsaye ganin baida niyar kara fadin wani abu kan zancen. Fitan mommy falon daddy din yayi daidai da shigowan hjy karima falon itama tare da yarta na goye ta zauna tana gaidashi. Ya amsa yake tambayan Amira ya jikin ta tace da sauki dama ai itace tajawa kanta ciwo idan ta tashi fitinar tsayan ta wai wani sabon iskanci Sahiba take kira tun wayewan garin nan data tashi sunan Sahibane a bakin ta. Sahiba kuma ita har yanzu bata manta da zancen su sahiba a rayuwan ta ke nan daddy din ya tambaya. Ai gaba dayan su basu manta da itaba a rayuwa kullun zancen su dai shine yaushe Sahiba zata dawone mami sai na masu tsiya suke barin zancen ta a gidan nan. Shiru daddy yayi wani abune ya fado mai a rai game da su sahiba dai wanda ya kasa saita zuciyar shi a kan hakan. Ban taba sani ko zaton akwai office a wurin ba haka kuma ban taba sanin cewa wanan wurin haka yake da girma ba sai wanan ranan. Ashe duk wunin da mukeyi a cikin sa iyakar mu inda aka ajemu ne don baka zawa wani part don kanka sai idan an mayar dakai wurin yasa bamu san kan wirin ba ko dai nice da ban damu da komai ba sai abinda ya kawoni ban sani ba. Wanda yazo kirana ya fara shiga ina biye a bayan shi muka shiga office din suna zaune kowan su ya kurawa computer dake gaban shi ido a lokacin. Na shigo na gaida su da aiki ba tare da sun dago ba suke amsa min gaisuwan mutumin yayi min nuni da wurin zama nakai zaune daga barin shina dama inda suke zaune. U are wellcome dayan ya fada min yana miko min takardan dake saman taburin shi na karba a sanyaye yake fadin nabi bayanan dake ciki na turawa chief sakon baiyanan dana gani a cikin takardan. Hankalina na kwantar na fahinci me ake nufi duk bayan kawai zan tura a dayan suein shi shine abinda zanyi nan take na fara turawa kafin dan lokaci na gama na dan dago da zumar fadin na gama idanun shine akan yadda nake aikin kamar wace ke tsoron laptop din ko kyama haka nake dannawa na hada komai har na tura mai. Kaina na dukar kasa yace cikin dan saurin maganan shi kin gama turawa na kada mashi kai alaman eh ya kara turo min wani takardan kuma aikin dai da muka wuni munayi ke nan har akai sallah azahar na dubi lokaci a wayana dake aje saman table din koshi wayan umma ne da nake amfani dashi duk ya tsufa yaji jiki sosai. Tsab na mike tsaye daga zaunen da nake suka dago kai lokaci daya suna kallon inda nake tsaye din asalat kawai nace dasu ina kokarin fita daga wajen kujeran. Sai lokacin ya dago kai ya kalleni jin abinda na fada kafin kuma ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannun shi fari da gashin jiki yaiwa addo dasu ko ina. Dan magana yayi a cikin muryan ruwa naji wanan yace dani daga can na wuce restuaran din wurin akwai abinci an hada naje naci kafin in dawo. Ban iya furta komai ba na fice daga office din direct dakin da aka warewa mata don hutawa na tafi ban dakin na nufa nayi sallah kafin na fito na tayar da sallah har lokacin komai da nakeyi kamar a mafalki nakeyin sa nake gani don ban iya gaskanta hakan ba. Na dade zaune ina tunane barkatai ga umma ba waya a hannun ta balle na kirata in fara sheda mata halin da ake ciki kan na dawo haka dai na daga na koma office din ban samu kowa a ciki ba lokacin duk sun fita basa ciki. Hakan ya bani daman karewa ko ina kallo na dan lokaci kafin na mayar da kaina a waya na dauko earpiece dina na makala na fara shan free kira,a dana kan sha. Na daga kaina sama na mayar da kai bayan kujera na mike ina bin karatun a hankali ko zanji sasauci a zuciyana lokacin ga sanyin AC da aka sake yana ratsa ko ina na jikina sai kamshi ke tashi a lokacin. Har suka shigo banji motsin su ba saboda bakon yanayin dana tsunci kaina mai kama da mafalki a wurin har saida wanan din mai mun magana ya dan daki table din dake gabana na dago da sauri ina bude idanuwana da suke a lumshe kamar barci na son daukana a lokacin. Da sauri na kai hannu na cire wayan a kunnena na mika kuma ina kashe kiran da nake saurare din ina gaida su da dawowa. Wayan ya kara kallo karo na barkatai yana kaiwa zaune a mazaunin shi har lokacin bai magana da kowa a cikin su bamu muka bar wanan wajen ba sai gab da magariba. A gajiye na isa gida daga shiga na wanka na fada nayi na fito na tayar da sallah ban daga wajen ba saida nayi isha,i na fito daga dakin. Umma na sama falon tana sallah na samu wuri na kai kwance ina jiran ta idar ina gaida ita ta amsa min tare da tambayana ya aiki ? Saida na lumshe ido na dago daga kwance ina fadin umma idan na fada maki abinda nake ciki yau ban san ya zaki dauki zancen nan ba. Cikin damuwa take cewa dani Allah yasa lafiya ba wani abin bane ya faru kuma ba Sahiba ina jin tsoro da fargaba akan ki ako wani lokaci. Eh to umma abin kan da fargaba kuma da mamaki ace duk manyan matan da muke aiki tare sai nice kadai a yau na samu karin girman da ko mazan wurin basu samu ba shine abin mamaki a wurina kuma yake damuna. Nan dai na labarta mata komai daya faru ban raga komai ba na fada mata duk yadda abin yake har aikina. Shiru umma tayi na dan lokaci kafin tace dani Abdulhamid ya kamata yanzu mu nema akan wanan maganan idan ba wani makarkashiya aka kulla maki ga hakan ba. Amar ta kwalawa kira ya firo ta turashi wajen Abdulhamid din anyi sa,a yana gida bai fita ba ranan zuwa asalatu wurin daukan karatun da yake zuwa da yaran shi. Mikewa nayi zuwa kitchen na dan zubo abinci kadan na fito na fara ci ke nan yayi sallama part din umma ta bashi izzini ya shigo. Bayan sun gaisane take fada mai duk abindana fada mata yana jijiga kanshi har tagama fada mai komai yana sauranta kafin yace. Hakane umma komai data fada maki tabbasa haka ya faru ba kuma komai yasa haka ba sai cancantan Sahiba. Akwai masu takarda a hannu da suka karanci wanan fanin amma kuma sai Allah ya zabo sahiba a cikin duk dako ilimin nasu saboda gaskiyan ta da warware matsala irin nata tabbas nasan wanan shine kawai dalilin ba wani abu ba. Aikin nan alheri ne ga yar ki dake dama mu baki daya haka kuma sai kinyi hakkuri sosai kin sa yarda da Amincewa ga tarbiyan da kika ba yar ki a rayuwa. Don aikin ta yanzu zai iya kaita ko ina da Sha,aban yake a vikin kasan nan don gyin aiki tare dasu idan har bukatan haka ya taso. Jin abinda ya fada yasa na dago kaina daga cin abincin danake dan cakula da cibi na kasa cin abin kirki ina sauraren su lokacin. Barin gari akan aiki ita daya Abdulhamid yace kwarai kuwa don zasu iya tashi daga garin nan zuwa arewa ko kudu duk aikin zai iya kaisu wanan wuraren . Ina sam hakan ba zai yuyu ba gaskiya aiki idan ya wuce fadin lagos din nan gaskiya saidai a bari yaushe zan bar yar marainiyar Allah tana wanan gararin don kawai rashin gata. No no no anty ba haka bane ina sam na tabatar kuma na yarda wanan ba zasu cuta mata ba a nan Allah ma ba zai yarda wani abin kyama ya faru maki da yarki ba. Ki yarda dani don Allah ina rokon ki ki bar yarinyar nan rayi amfani da daman ta data samu a wanan lokacin wanda zai kawo mata cigaban rayuwa idan Allah ya yarda. Shiru umma tayi na dan lokaci tana nazarin kalaman shi kafin kome ta tuna tace na yarda dakai da imanin ka Abdulhamid don na tabbatar ba zaka taba barin yarinya na ta cutu ba ga hakan.
Chapter 124 · 0% Book details