← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 337

Sashe 38

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

so har ka koma waje a yanzu ba tare da aure akanka ba kuma. Ya dago idanun shi da suka canza launi yana fadin zan shiga kafin na tadi daddy insha Allahu ya fada a gajarce. A gundure da jin zancen mahaifinasa ya samu ya mike tsaye yana fadin zaije ya karya don tashin ke nan daga barci yazo nan gaidashi. Bin bayan dan nasa yayi da kallo don ya fahinci akwai damuwa a tare da Abubakar din dole akwai wani abinda ke damun dan nasa. Ya dade a dakin hjy yana nuna mata rashin son wanan hadin da suke son mashi amma ta nuna mashi ai bakin alkalami ya bushe a yanzu don ba zai hadata fada da yan uwan shi . Mikewa yayi yafice daga dakin kai tsaye motan shi ya shiga ba tare da yasan inda zai nufa a lokacin. Daga wanan fitan sai mota aka dawo dashi gida shi ya wuce hakan ya kara sa daddy zargin akwai wani abu ke nan da dan nasa ke nufi. Wai sabo turken wawa nikan ai ban saba zama wuri daya ba gashi ina ganin dan abinda ke garemu umma ke zara munaci muna sha a cikin sa wanda nasan zara bai barin dami. Sai faman shawaran mafita nakeyi a raina na kasa cin ma mafitan abinda zamuyi don wanan ungywar kan kamar garine komai kake idon wasu ba akan ka tundai ace neman na kanka yanzune sun gama dakai kamar yadda naji ladi tana fadi da bakin ta. Hakan yasa gaba daya garun ma nikan ya fice min a raina ga baki daya yanzu zama dai nake a cikin sa ga ba karatu garemu dagani har kanina muna neman kwashe wata uku zaune a gida muna zaman banza. Duk da karatu ni ba damuwa na bane illa neman abinda zamu rufawa kanmu a garin shine kullun tunane. Zaki ce fa ko ni din wata babbace mai shekaru a yadda nake wanan bakan wahalan sha hudun dai nake ina harin sha biyar ga shekaru a lokacin . Hakanan kuma nake buga buga a cikin wahala don umman mu bata da lafiya da za tayi wanan wahalan a yanzu. Safiyane na gama muna abin karyawa na kaiwa umma na aje ba wani abu bane taliyane dai muka dan sulala da safen don ciki ya dauki nauyi ba komai a cikin sa sai manja da dan attah dana jajaga na dafa sai kamahin attah ke tashi a ciki kawai ba wani nama ko kifin ice fish da yai banza a can. Na dafa ya fita raina sai dan cakula nake ina kaiwa baki suko sai kwasan abin su sukeyi hankali kwance suna ci. Saida na daidaici umma ta kusan gama ci nace umma dama ina son muyi magana zaman nan ya isheni haka kudin mu ya kusa karewa a yanzu gashi bamu komai da kudi zai shigo muna a yanzu. Cire hannu umma tayi cikin abincin tana kallona tare da sauraren abinda nake fadi din sai da nakai karshe tace akwai Allah sahiba shi zai duba muna Insha Allahu. Nasan kina kokari sahiba baki gajiya da kula damu ga komai nima kuma ina wanan tunanen da kikeyi a yanzu. Sai dai na barwa Allah zabi akan hakan yanzu ke wani shawara kike ganin zamu bi don dai gaskiya ban yarda da sana,a acikin semi ba kuma. Zan dinga shiga cikin iko ina neman abinda zamu ci nayi maki alkawari duk inda na taka zan tsare mutuncina kamar yadda kike min addua a kullun. Sam ba zan yarda da wanan ba ki shiga cikin iko ke kadai ki yawats iko ba karamin gari bane sanan kiji ance akwai masu neman a can cikin iko din wanda bamu san suwaye ba kuma akan me suke neman mu din. Nasan ds haka umma kuma ba zan taba yarda in koma ajagule ba zan canza unguwane wanan karon . A lokacin naga umma tayi dan ajiyan zuciya tana fadin yanzu na danji sanyi zan iya yarda da hakan. Ta ina zaki fara da garin nace zan koma ikoyi na duba ko zan samu abinyi a can din daga gobe zan fara shiga insha Allah zan shiga da dubu biyar na duba nagani ko zan samu abin juyawa a wanan side din. Nayi murna jin umma bata hanani wanan shawaran dana kawo mata ba sai albarkan data saka min a karshe wanda naji dadin hakan har kasan zuciyata. Washe gari tun safe na fara shirin shiga gari in zaga inga abinda zan kama a cikin garin. Nayiwa umma sallama na dauki hanyar sai ikoyi kamar yadda nayi alkawarin anan zan fara gwadawa. Tafiya nake ina bin layi layi a cikin kasuwan ina kallon ko ina tare da nazari har naje na tsaya gaban wani shago sayar da kayan miya ciki na shiga na samu mai shagon akan ya ban sari. Ya gaya min dokokin sari a wurin nace na yarda ina dauka na nufi cikin unguwar gadan gadan na fara ihun buy fresh vegetables fresh tomotors . Sai gashi Allah yaban sa,a lokacin dama mutumin yaban in dawo dashi bai ko yi ba na sayar da wanda na dauka duka har ana nema. Ban koma ta kanshi ba na dauki pure water na zagaya inda motoci suke cinkoso sai gashi na sayar kwara biyu suka rage min na zauna a wani innuwa nasha daya na wanke kafa da hannaye da dayan na koma kasuwan nayiwa su umma sayayyan da zankai masu gida nakuma yiwa mai shagon dana dauki kayan miya don ba karamin riba na samu ta hanyan daukan kayan da nayi ba a wurin shi. Don jin dadi har diban min yayi nakai gida nayi godiya na wuce zuwa semi boda shidda na isa gida a cikin farin cikina su umma suka tareni suna tambayana ya kasuwa ina washe baki nake fada masu irin sa,an dana samu a ranan. Na fitar da abinda nasayo daki na shiga na sako dan guntun wandon da nakan saka idan zanyu aiki na dauko doyan dana sayo muna na zauna na fara ferewa kafin na tashi na hada suta ranan dai munyi girki da kanmu munci abinda bamu faye yi ba sai lokaci lokaci. Na kwaso na kawo daki kamshin ice fish yana tashi da danyen Attarudu irin dai miyan yarbawa din nan dan shi na iya shi kuma muka saba dashi. Haka nake fita a kullun kuma ina samo sa,an da umma ke kira min idan zan fita zuwa wurin sana,a na din. Sana,a sun kai kala goma da nakayi hakan zan wuni a wahalace wurin neman kudi inayi ina share zufa dake tarso min idan na dawo kuma nayi girki muci . Wani lokaci zan samu Amar ya danyi min jajage don yanzu bamu rasa kayan miya a dakin mu don haka yakan diba ya dan gyara min ya kuma hura wuta ya rage min aiki ke nan kafin in dawo din. Ga zancen makaranta dake raina ko wani lokaci nakanyi wanan tunanen koda ni banje ba Amar shi ya samu ya tafi ni din a yanzu ba dole bane karatun a gareni Bukin ya taso gadan gadan kamar yadda daddy ya fada don tako wani bangare sai faman shiri sukeyi don lamarin bukin . Wanda tun bayan wucewan Abubakar sau daya yazo gida koshi sai da daddy yayi masa fadan hakan bayan hjy ta fadawa daddy din dalilin fushin shi dasu da yakeyi. Cikin fushi daddy ya mike yana fadin wanan wace irin maganace bayan mun tsayar da zance yazo zai kawo wani magana daga baya. Dama kin san baku shirya hakan da dan naki ba kika bari har nakai ga zuwa na tsayar da magana gaban manya. Hjy a cikin lumana ta kalli mijin nata tana fadin menene na tayar da hankali haka Alh ina dai dani da modibbo duk a karkashin ka muke. Auren nan kuma haka akaiwa kowa shi ko yana so ko baka so aka kuma hakkura aka zauna mutum nawa a cikin family din nan suka nuna basa so daga baya kuma bayan anyi aure a zauna lafiya. Alh ya dago kai ya kalleta kafun ya zauna dakyau yadda yake zaune ada yana sauke ajiyan zuciya yana fadin shike nan ai na dauka kema zaki mara masa ne ku mayar dani mutumin banza a idon mutane. Tace ni na isa in hakan tunda nasan wanan abin ba fashi tunda yaki nemowa da kanshi a wuce wurin . Ya gyada kai cikin zafin zuciya har lokacin yace ki fada mai ya tabbatar da yazo garin nan kafin satin daurin auren yaji bukatan da suke dashi a bangaren yan matan dashi da abokan shi.
Chapter 38 · 0% Book details