← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 305 OF 337

Sashe 305

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni dai tun kan gari ya gama haskawa nayi nawa wankan na shirya na koma na zauna a can kuryan dakin da muke ni dasu Faiza da sauran yan uwa ina bin kowan su da kallo tare da nazarin su da abinda suke fadi lokacin. Sai bayan sun gama karyawa ne su gwaggo Amina suka shigo suke fadin in saka mayafi zamu gaida hjy mahaifiyar su mukhatar din. Buje da rigan atamfane yar super a jikina da akaiwa dinkin buje da riga fetet daya dane jikina ya fito da shekaruna a fili sai kamshi dake tashi ko ina a jikina. Mayafi na yafa daya shiga da kayan sai flat shoes a kafana simple makeup ne a fuskana da nayiwa kaina don nasan abinda zai min kyau a fuskan nawa. Tsakiyan su nake sun kewayeni mukayi sallama a kofan falon da zai sadamu da dakin hjy din idan mun shiga daga cikin part din gaskiya ginan ya hadu duk da kaina a dan duke yake amma ina ganin yadda ginan ya tsaru. Tana zaune falonta tare da bakin su da gani basu jima da gama karyawa ba suma a lokavin don anata fita da kayan abincin da akai amfani dashi a falon. Sallaman mu yasa su kara dan natsuwa suke fadin sannuku da zuwa muka shiga muka zauna su gwaggo suka zauna a saman kujera yayin dani da yan matan muja zauna a kasa daga gefe aka shiga gaisawa. Nan su gwaggo suka dora da fadin toh hjy ga yarki nan mun kawota gareku amana yo ai wanan gida tazo don nan gidan sune itama. Kada wanan yasa kuji komai a rayuwan ku kan zaman ta a tare damu ni dai bukatana a zauna lafiya su bawa mijin su kwanciyan hankali da natsuwa. Don shi din dan ujulane da balaguro yau yana nan kafin gobe zakajishi a can haka sana,an shi ya kumsa hjyn ta fada. Don haka Sahiba ban son naji komai ya fito na rashin hankali a wurin ki ki godewa Allah kin samu yabo sosai daga bangaren ki nima din shedane ga hakan. Da sauri hjy halima ke kallon wadda aka kira da sunan data dade da sani tana kwankwanto a ranta kafin a natsu tace wai Sahiba dai dana sani a baya ko watace wanan din ? Kaina dago a hankali ina kallon wace ke magana din nima din na shedata hjy Halimace dai dana sani a logos shekarun baya idan baki manta ba. Matar da muka hadu asibiti da ita tana jinyar danta har tace muna ai dan nata ya rasu itace yanzu nagani a gabana dakin sarukata din tare dasu. A zabure take fadin lalai kuwa Sahiba ina kuka shiga duk wanan dadewan haka ina mahaifiyar ki da kanin ki take tambayana a cikin mamaki tana min kallon bazata. Nan ta shiga bada labarin haduwan mu da ita shekarun da suka wuce kowa saida ya tausaya muna nan suke fada muna cewa ai mijintane dan uwan mukhatar din ne. Don da mahaifiyar mijinta da hjyn su mukhatar ya da kanwace suke nan aka shiga gabatar muna da yan uwan mahaufiyar nasa da suke zaune a falo din . Mukaji kuma ashe su zamane yakai iyayyen su can suka zauna suka saje dasu an dai dan kara tataunawa kafin mu bar su zuwa wanan dakin muka barsu gwaggo tare dasu a part din. Sai bayan dawowan sune suke fadin wai karfe hudu zasu kaini dakina sam ban taba zaton hakan zai sani fargaba ba sai wanan lokacin don wani iri naji a zuciyana tunda suka fadi hakan. Suke fadin ance gidan a gyare yake basai munje munyi wani gyara ba a cikin sa komai an zuba kunga ko tunda har sun nuna kamar suma sun isa da itane ai sai suga kamar muna kwankwanto akai. Nasiha sosai suke min tare da kara lurar dani a dakin da suke idan kinga yadda gwaggo Hari da yar uwanta gwaggo Asiya suka zake suna min fada zakice basu bane masu min bita da kuli a baya. Yanzu sun nuna cewa ni din kan tasuce yar uwasuce ta jini dole yan uwan mahaifina suka dan rakube a gefe wanda saini din ke nuna sune nawa don komai zanyi ko nakeso su nake kira in tambayesu. Nasan hakan yana dan taba zuciyar su saidai basu nuna min a fili ba amma suna kebewa suna gulma don anty Amarya ta rutsasu suna gulman a tsakanin su tazo tana fada min. Kai mutanen halinsu saisu wallahi suwa ke nan na tambayeta wanda ba halina bane tsoma baki a maganan manya. Su gwaggonin nan naku dai hjy hari man da tawagarta yanzun na samesu a can dakin suna gulma cewa Allah yasa dai ki iya zama yadda kika saba da harkan bariki. Gadai gida kan kin samu amma bariki ba zai barki ki zauna a ciki ba dama watace a cikin diyansu ta samu wanan aida su tasu ta yanke ke nan. Jimun fa mutanen nan wai har hari na fadi saboda idon ki daya bude da barki yasa ta shiga tsakanin ki da danta tunda wuri don ba zata yarda ki rabi danta ba. Hakama modibbo shima ya nuna ra,ayinshi gareki amma sam ba zasu taba yarda da hakan ba a tsakanin ku don kin bude ido a bariki. San nan kuma ai gashi ya tabbata kan camfin da akai maku tun kakannin duk inda kuka shiga sai kun dara kowa lokaci guda kema dake bariki za ace wai kece kika samu wanan daulan hakan amma nasu diyan suna zaune a gida. Jimjn mutane da son kai haka don Allah ko me zakiyi da danta balle shi modibbo ma dayake da matarshi a gida harda yara. Kawai dai son kaine irin nasu na banza da baida dalili su a ko ina saidai sufi mutum badai kafisu ba da zaran suga Allah ya doraka akan su shike nan a dauki karan tsana da sherin duniya a dora ma saboda hassada. Lokacin nan shiyasa na rufe ido nayiwa baby aure saboda irin yadda suka fara nuna min waiga su Nabila gida amma zaice baby yake so shi. Yanzu kuma da Allah yakawo rabuwa a tsakanin su ba abinda basu fada ko yanzu din nafi bukatan ganin ta koma dakin ta ta zauna don dai kawao badai aikin yine a yanzu din. Don haka sahiba ki daure ki rugumi auren ki da hannu biyu kibi mijinki ku zauna lafiya daduk wanda ke kewaye dashi don Allah. Nisawa nayi kadan ina fadin nagode anty insha Allahu zanyi yadda kikace din zan zauna lafiya da kowa insha Allah. Kada kibi takan wanan uwargidan naki ki barta da halinta idan ba tashiga harkan ki intashiga kan ki nuna mata kema kin iya sai a zauna lafiya. Yanzu bakiga gidan mu ya dan samu sauyi ba don yanzu na gama fahintarsu abudai ne idan yazo ya kama nabawa kowa hakkin shi na bayar idan mutum yabi shike nan. Idan nace banji haushin zancen su gwaggo ba gareni karya nake fada maku don gaba daya nikan sun kara zubemin a idona. Antyko taci gaba da fadin wai ga dukiya har dukiya amma bai samu mata ba sun san indai kece kwana biyu zaki fito ki koma barikin ki da kika iyane ai. Jifa wai dan dan uwanka kake wa wanan fatan haka murmushin karfin hali nayi ina fadin ba komai tace don Allah sahiba ki daure ki zauna a dakin ki. Kinga dai yadda Allah ya rufa maki asiri a cikin makiyan ku har gobe kune sama garesu ni yanzu na gama fahintar kowa wallahi. Su mutanene masu dan banzan son kansu da mugun hassada a zukatansu basu son suga wani ya karu yafi ko yaushe su dai ace sune ke samu ko sune a gaban komai. Wallahi kaf din su indai ba na bayan nan ba sune zance maki suna da dama a cikin su amma kusan manyan nan wallahi duk halin su dayane gaba dayan su saidai na wani yafi nawanine kawai a cikin su. Wallahi shiyasa nake son modibbo Allah kinganshi sam bai kwaso wanan akidarba ko kadan yanzu ki duba duk da ake cewa komai ya wuce a zauna lafiya a tsakani. Kinga dan gidan Alh nuhu a nan ko daya ko dan kidan Alh gyade bafa wanda yazo ko dayan su ai idan gaskiyane ko yadda kikai masu din nan zasuzo ko diyan su su turo amma mugun nufi ya hana . To wallahi kaf dinsu kusan haka suke sai ka zauna dasu zaka san halinsu sosai shiyasa sam bamn dagawa Gwaggon ku kafa koshi Alh. Nisawa nayi tare da fadin Allah ya shirya dama naga yadda take kallona idan mun hadu da ita tun a kaduna nayi mamakin ganin tazo har nan din duk da tasan kwana biyu za ayi kafin a koma. Wanan ai sunyi ne da biyu wa yan nan da sai hannu mai mai suke bi idan baka dashi basuyi dakai . Idan ko kafisu kaida su zaku koma kamar Annabi da kafirine a fili zasu nuna maka kiyayya ba gaira ba dalili don kawai hassada dasa abu arai irin nasu. Anty amarya harta gama tafita ban samu abindana fada mata ko daya ba lokacin bayan nisawa da nakeyi ina tunanen zumuncin zamani yadda ya koma yanzu ga mutane. A gaskiya bazan lamunci zancen wai ummana ta dawo cikin su kaduna ta zauna ba a yanzuma . Don naji sun fara fadin wai ya kamata tunda nayi aure saita dawo gida itama su zauna a gaban yan uwa zaifi watau dai a can din sun dauke mu bariki muke shekawa kawai a zaman can din. Haka har karfe hudu yayi kowa ya shiga shirin tafiya zuwa gidan da zan zauna din a cikin sa wanda ba kowa yasan da sanin cewa ashe ba gida daya zamu zauna da hjy falmata ba dama har danginshi basu sanda hakan ba sai lokacin da aka dauki hanya daban ba wanda suka sani ba zuwa wani sabon gida nashi dake gaban unguwar da mahaifiyarshi take kadan nan nawa gidan na Maiduguri. Gidane na gani na fada wanda shine wanda ya gina a baya bayan nan don ba kowa yasanda cewa gidansa bane a garin . Tsarinshi da komai ginan kasan wajene ba irin fasalin ginan mu
Chapter 305 · 0% Book details