← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 337

Sashe 30

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Likita ya shigo ya duba jikin Alh yaga yayi yadda yake so sai kawai ya rubuta mashi sallama don shima bai son su kwana a nan gara ya koma gida zaifi mai sakewa da wakwala don sanin halun Alh da yayi bai son kwanciya asibiti ko kadan sai in ya kama dole.
Aka tataro aka dawo gidan dashi Modibbo ne ya jawo shi a hankali tare da matan shi su biyu suna bayan motan a zaune.
Har suka iso gida motan shiru ba wanda yayi wani magana sai maigidan ne da dan sa ke dan hira jefi jefi a motan.
Shiya kama mahaufin nasa har zuwa dakin shi ya zaunar dashi saman gado kafin ya kunna mai Ac da bai sake sosai yana kokarin fita.
Ji mana modibbo sai ya juyo da sauri inda mahaifin nasa yake zaune yace tambaya nake son yi ma tsakanina da kai a yanzu.
Daddy akan me ya tambayi mahaifin nasa yace akan wanan yarinyar dai ta lagas da kace kaman su yana zubi na diyań gidan baba namadi.
Shikan modibbo da nai san kai ba yace wallahi daddy kamarta dasu har ya baci harda dan lutsawan nan na kuma tun su duk tana dashi a fuskanta.
Sai dai ita wanan din ko hausa bata iya sosai ba shine maraban su da yan gidan kuma ita wanan din ta dara su haske sosai gaskiya.
Kasan gidan ita wanan yarinyar a lagos din na sani don dani aka tafi karbo wayan gidan gidan hanya din nan ne mai girma sosai don mutanen gida suna da yawa sosai gaskiya daddy.
Zaka kaini in gansu ya fada abinda yasa modibo yayi saurin juyowa ke nan yana kallon mahaifin nasa a cikin mamaki.
Lafiya dai kake son ganin ta daddy don ba yar nan bace fa na fada ma ita din yar nan bace kama ne kawai da sukayi a fuska.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANA DARA GA, , , , , , , ,

1️⃣3️⃣

BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI, , , , ,

PAID ONLINE NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA KADA MU RIKI JUNA DANI DAKE, , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALLAHU, , , ,
Chapter 30 · 0% Book details