Sashe 44
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tafi gobe zan dawo. Na samu hjy a gida tayi murnan zuwana mun gaisa a cikin dadin rai ta tambayeni ummana da Amar nace duk suna lafiya. Abinci tasa aka kawo min naci saida na koshi nace zan wuce take fadin tun yanzu nace eh da akwai kuma ida zan tafine yasa zan wuce din. Tace in jirata tazo ina zaune ne nake jiyo muryan maza suna shigowa gidan ban damu in san kosu waye ba har suka shigo suna dan hiran su na gaida su a cikin turanci suka amsa min tare da zama a falon duk sai naji na takura da hakan. Gashi ban taba matsawa daga falon ba ban ma san kan gidan ba ga baki daya don haka na zauna a takure suna magana akan zancen kayan da suke tuhuma din an shigo dashi. A lokacin kuma hjy ta fito daga ciki dauke da leda a hannun ta ja tayi ta tsaya wuri daya tana fadin wa nake gani nan kamar ango a zaune ? Ya dan dago kai tare da kallon ta yana murmushi ya fara gaida ita mijin ta na fadin wanan angon ai an kwareshi don baiyi hutun angwancin nasa ba a dole ya dawo bakin aiki ba shiri. Sin dan dade suna magana yayin dana shiga zurfin tunane don ina tsuntan wani abu a cikin zancen nasu da sukeyi da hausa. Naji hjy ta ambaci suna tana fadin sorry Sahiba mun barki a zaune ko gashi kina sonki tafi nayi murmushi ina mikewa tsaye. Take fadin gashi ki gaida maman ki zanzo wata rana idan Allah ya yarda ya kawar da kai da sauri kuma ya juyo inda nake tsaye din. Ya mike da sauri yana nunani a cikin mamaki tare da waro ido wajr yace you a razane nima na dan ja kusa da hjy na tsaye cikin tsoro suka bimu da kallon mamaki dagani har shi. Sai da hjy ta miko min leda take fadin kasantane a cikin hausa komawa yayi ya zauna shima tare da dan basarwa ai kafin suyi haka koda hjy zata juyo bana wirin har na fice da sauri ba tare da mun tsaya munyi sallama da ita ba a lokacin. Cikin mamaki ta kara kallon shi tana fadin kasan wanan yarinyar ne sai kuma ta juya wurin mijin ta haroon tana fadin itace muke baka labarin su da muka zauna asibiti tare. Abubakar yace itace daddy ya zo nema kwanaki garin nan duk su suka hada baki wurin fadin itace suna tambaya yace itace sai dai gaskiya a yanzu na fara tsorata da yarinyar nan gaskiya ko dazun fa a agege na ganta tana talla anya ma mutunce kuwa wanan din. Hjy tace mutum ce don nasan har mahaifiyar ta da kanwarta mun zauna a asibiti daya dasu ga kwanakin bayan kanin ta baida lafiya. Da sauri suka bi bayana saidai ko mai kama dani basu gani ba a wajen sun rasa hanyar dana bi na tafi sai mijin nata ne ke tambayanta kisan gidan da suke zaune ne ? Tace nasan dai inda tayi min kwantace a baya don yanzu sun ajagule sun koma semi boda a can suke zaune yanzu ta bashi amsa. Da sauri ya kawar da zancen da fadin yanzun dai sunyi nasaran shigo da kayan kasan nan ta haramtaciyar hanya illa iyaka abinda zamuyi shine musan su waye wa yan nan masu kayan kuma wani jaha aka kai kayan a yanzu. Sun dade suna tataunawa da haroon din kafin suyi sallama ya mike don zuwa gida zuciyar shi cike da tunane kala kala. Nima haka na isa same ina son fadawa umma komai ina tsoro fadan da za ayimin din a lokacin don nasan yadda umma ke fada idan ranta ya baci dani. Don haka na faki idon umma din na fice zuwa waje can na samu wuri na fitar da kudin na kidaya sai da gabana ya fadi ganin dubu dari cur din su ya ban ashe da kuma dubu dayan dake saman kudin da suka sayi abu wurina da dayan ya bani. Jikina har yana ciri na mayar da kudin a cikin gwagirina danayi dan mara dashi ko ina nake bana rabuwa da shi a jikina dama don tsaro. Ai kuwa ina shiga umma ke fadin ina nafito nake cewa na manta ban sayo muna maganin sauro ba da muma magani insha na shige kawai abina na kwata cike da tunanen mafita garemu. Tabbasa shine wanda ya taimaka muna da asibiti kan matsalan Amar da yanzu yaro ya samu lafiya haka kuma umman nawa itama tayi lafiya sosai do manyan maganin data samu tana amfani dashi yanzu. Wurin ya cika sosai da masu tashen arziki yan kasuwa da masu smogling din shigo da kayan nan Nigeria. Sune zallah a wurin suka taru don nasaran da suka samu kayan su ya shigo lafiya ba kamar yadda suka zata zasu samu matsala ga hakan ba. Tun daga wajen wurin zaka gane hakan don irin manyan motocin da suka cika a haraban wurin taron nasu da sukeyi a ranan. Don duk wani dan kasuwa daya amsa sunan shi shi a nan suke hadu suna taron su idan hakan ya taso. Gidane babba na gani na fada da kayan more rayuwa a cikin sa suka hada a wurin kana gani kasan kudi yasha kashi a wurin hada ginan nan. Ga security nan ta ko ina tun daga bakin layin a banza har mazauna unguwar sun da haka don idan zasuyi taron su kowa na wanan unguwar yana natsa kanshi ne. Don yawan security din dake zama wurin saboda tsaro da kariya ga ubangidajen nasu don wata rana fada kan barke a tsakanin su yasu yasun su har ajiji ciwo ko rasa rai duk da a yanzu sun shawo matsalan hakan a tsakanin su tun bayan shigowan yaro karami a cikin su yanzu wanda yake kamar jagora a garesu. Bayan wa yan nan katai din yan ko ta kwana din ga wasu tsalalan yan mata a wurun suna kai da koma suna raba abinsha dana ci da aka tana dan hakan. A yau din duk wanda ka kalli fuskan shi a cikin su a sake fuskan shi yake wurin duk dako zaman jiran mutum dayan da suke wanda ya jawo masu wanan nasaran da suka samu din a yanzu don kayan da suka shigo lafiya. Sannu a hankali suka koma jan tsuki a tsakanin su don bata lokacin da sukeyi a nan din har yakai dai sun soma maganan kan zaman banzan da sukeyi din a wurin duk akwai komai na more rayuwa a wurin har mata. Sai can suka fara hango mutanen shi na hannun daman shi dakan shigo suyi dan kuskus kafin ya shigo surin ke nan lokacin hankalin su ya fara kwanci da zaman nasu. Kamar yadda kowa ya shigo ta kofan gaba shi sabanin hakan don ta kofan dake baya na dakin taron ya shigo masu duk suka maida kallo su gareshi. Don Allah yaba yaron zati da kira na halitta duk inda irin su suka shiga ansan da suna wurin ga kuma kwazo da Allah ya bashi na neman kudi duk da gwaunati na ganin sana,an nasu haramtaciya ce ga kasa shigo da kaya a bayan idon jami,an tsoro ba kasa. Ga wani dan saje daya aje a fuskan shi wanda ya kara fitar mai da zatin shi a fili yayi masa kyau ainun a hankali yake takowa tako irin na kasaita da isa da izza da gani shi kasan abinda ya taka a hakan. Taken shi suka fara mai na young billoniear yana dan daga hannu a hankali yana jinjina masu a hankali zuwa wurin da yasan shine wurin zaman shi din. Bai zauna ba din sai da yaje gaban wasu tsofi biyu da suka girme masa yakai runsune kasa yadda ake gaida manya a cikin al,adan hausawa ya gaida tsofin kana yabi sauran da hannu yana mika masu suka gaisa. Kafin ya dawo wurin zaman nasa ya zauna bakin shi na cike da adduan don yasan komai sai bawa ya danganta da Allah yake samun galaba dama kuma ko can abinda ya dakatar dashi ke nan bai fito da wuri ba. Haka kuma yasan cewa lamarin nasu saida hakan don duk wanda ke daki toron nan yasan abinda ya taka kafin ya shigo wurin. Tun mikawa wani dan maiduguri hannu wani lokaci yaji kanshi yayi mai nauyi wasa wasa har abin yaso ya kayar da kasa sai gyaran Allah aka samu baikai kasa din ba shi wancan din ya kwanta a lokacin. Bayan shugaba mai suna shugaba yayi adduan bude tarone suka shiga tatauna abinda ya kawosu wirin a lokacin. Daya bayan daya suke tashi kowa kuma a cikin su yana da inkiyan sunan da ake kiran shi dashi a cikin su wanda kowa yasan da take nasa. Alh baba shine uban gungiya shiya fara magana sai Alh Rabi maliya mai bi masa sai shi Aliyu yayyayafi don yawan alherin sa ga mutane su suka laka mai sunan ko su kirashi da dollers boy. Shine na uku a cikin kungiyan tasu a yanzu dama duk wani kwaran shike karban su ya fiddasu a hanya har a cin ma nasara. Yaro ne da kudi abokin manya don shekarun sa baifi sha takwas zuwa sha tara ba a lokacin amma ya kerewa sa,anninsa dama wayanda suka girme masa ga shiga kasuwanci a yanzu wurin harkan kasuwancin su. Aliyu ga kyau ga kudi ga ilimi duk Allah ya hada mai uwa uba ga kyau ga kwarjini sai dai kallo daya zaka dauka shi din miskiline na gaske don yana da wuyan sabo da mutane. Sai dai idan ka ganeshi baida girman kai mutane ke masa wanan fasaran do rashin ganewa saidai sam Allah bai sako mai tsoro ba ko fargaba don irun mutanen nan ne da idan sun tasa abu a gaba sai sun sameshi. Yadda yake da kafiya da naci yasa yayi fice a cikin abokan harkan nasu dan shi Allah ya bashi tausayi da jin kan nakasa dashi sosai ga taimako idan yaga mabukaci har sukai ido biyu da maishi. Kudi kan zamuce gadon su yayi a wurin mahaifin shi da yanzu tsufa da ciwo ya riskeshi saidai sun raba hanya da mahaifin nasa don shi smogal