← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 259 OF 337

Sashe 259

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallaman hjy ghana da yaran ta mata a falon ya dakatar dasu daga hiran da suka dauko a cikin fara,a suka amsa masu sallaman tare da nuna jin dadin ganin su a lokacin. Hjy ghana dake tafe tana fadin ashe ko shawaran autana yaci gashi ko mun sameshi a cikin gidan kamar yadda ya fada. Nan dai suka karasa shigowa aka gaisa a cikin raha da nuna jin dadi daganin juna hjy din ke fadin dayaya muka samu shiga gidan nan ? Mukhatar sai mu kara godewa Allah da wanan baiwan da yai maka a yanzu lumshe idamuwan shi yayi a lokacin zuciyan shi naso ta tuno mai da wasu abubuwa da suka wuce a baya amma yana tausan zuciyar nasa don kada ya tuna hakan a wanan lokacin. Yare ya barke a tsakanin su wanda kowa ke ji a cikin su hjy ghana babban yayace ga mahaifin shi mukhatar din na uwa daya uba daya. Suma suna da nasu rufin asirin tun can baya amma yanzu nasa ya taushe nasu har suke ganin suba komai bane a yanzu kinsan halin mu yan adam da hangen nisa. Bamu waigen baya kullun idon mu a samane muna hango wa yanda suka zarce mu maimakon mu dinga kallon wa yanda muka fi don haka zaisa mi dinga godewa ubangijin mu kullun. Zancen autan tane da suka fara dashi a baya ya kawota yanzu sai kuma yaran ta mata dake son su gana dashi kan wasu bukatu nasu. Yaya kamar yadda suka saba kira a bakin su don yadda mahaifiyan su ke kiranta ke nan suma suka dauka ya tsaya masu a bakin su kuma. Ban manta da zancen autan ki ba idan yadda nake so ya samu nan da dan lokaci autan ki zai bar kasan nan ga baki daya zamu zauna dashi acan inda nake zama a yanzu. Wani irin dadi dattijuwar taji don wanan albishir din da yai mata duk da tasan a baya basu kyautawa yaron ba amma shi sam ba rikesu da komai ba asalima sai nuna yake kamar wani abu bai taba faruwa dasu na rashin mutunci ba can baya. Abinda basu sani ba shine yana iya danne zuciyar shine baison ya tuna da wanan abin daya zama mai sanadin alheri a yanzu don su nashi sun kishi wani bare yazo ya daga rayuwan shi. Nazone nagane ku a yau din nan kuma zan juya don na bar tarin aiyuka a gabana jin hakan yasa mahaifiyar shi ta dago kai da sauri tana kallon shi cikin mamaki. Yace eh ummi yau din nan da yamma zan wuce lagos ina son a yau in gana da iyalan marigari na gansu su san ina nan ban manta dasu ba a raina inda taimakon da zan masu sai in masu kuma. Taimako kan ai kayi masu shi yanzu tunda ka taimaka dukiyan su yana fitowa hannun azzuluman mutane a yanzu. Ummi zan daiyi ni yanzu wancan din su sukayi kokarin koma da kansu har gaskiya ya baiya saidai zaluncin ya hana su fadi inda suka shiga da kudaden shi na baya wanda yafi komai yawa kuma don shi suka kashe din. Wai wa kuke zance haka akanshi hjy ghana ta tambaya cikin rashin fahintan su a lokacin sai ummi din tace wanan bawan Allah daya tallafawa rayuwanshi da aka kashe shi a kaduna wancan lokacin . Dan tunane hjyn ta tsayayi kafinta tunoshi tace duk tsawon wanan shekarun dama ana bincike a kai ? Dama hjy ai baka kashe mutum ka zauna lafiya komai daren dadewa sai Allah ya tonama asirin kan Alhakin dake kan ka Allah dai ya tsare ya karemu daga miyagun kaddarori kawai babban yar nata daga cikin su ta fada. Abin takaici ma wai ace yan uwan haihuwan kane sukai ma haka kuma suka wawashe dukiyan nasa iya tsakanin su basu tuna da iyalan shi va ummi ta fada Yana jin su idanuwan shi a lumshe ba abinda yake tunowa sai ranan daya fara haduwa da Abba lokacin da suka amshe visa ga koran wullakaci. Kan laifin data san cewa dasune ya aikatama uban laifi amma aka dora akanshi don yana matsayin dan cin galihu a wurin su. Jin yayi shiru bai magana sai faman tunanen da yake yi yasa wace ake kira da anty shuwa take cewa dashi dan uwa nazone kan zancen muna baya dakai. Sai lokacin ya bude idanuwan shi yana dan kallon ida suke zaune din cikin kokarin son ya tuna da alkawarin da take nufi sunyi dashi. Nan dai suka dan tatauna abinda ya shafi rayuwan ko wanen su da irin taimakon da suke nema a wurin shi yace daya koma ummi ta tuna mashi . Bayan tafiyan sune ya kara yiwa mahaifiyan shi bayanin abinda yake son zuwa yi lagos din da irin taimakon da yake sonyi din idan yaga halin da muke ciki a can. Karfe biyar yabar maiduguri zuwa lagos bayan ya gama ganawa da duk wani wanda ya samu ganin shi saura kan hakkuri ya basu kan hakan. Hjy karima ta dawo ta samu abinda ya faru hankalinta a tashe kafin kuma ta fara sababin cewa an munafunce ta tunda ba a kirata ba tun lokacin. Ba dai wanda ya biye mata don bashine a gabansu ba su yanzu dole kuma ta dawo aka hade kan jin yaya za ayi dole su baffah ne da modibbo zasu biyan shi. Anan kuma suke jin labarin cewa suma din su Alh Nuhu har baffah buhari ma ashe an tafi dasu Abujan ga gidajen su da aka kulle zance ya gama bazuwa cikin gari ko ina ko a lokacin. Da farko sun dauka zancen wasane duk kazafine ko barazana don mahaifin nasu zai iya fitar da kanshi kan ko menene ya tasa haka kuma su basu yarda cewa wanan laifin shi ya aikata ba dukda wa yanda suka san lokacin sun fada masu gaskiya kan hakan. Hankali yakai kololuwan tashi kowa ya nufi inda yafi mai sauki ya zauna inda mafi yawan su a gidan gadon su suke don matan ga baki daya nan suka nufa suka zauna a nan diyan nasu da suke ganin basu iya zama cikin wanan gidan a yanzu suke samun su ayi maganan da za ayi din a lokacin wanan rikicin. Sauri nakeyi na isa gida dan hold on daya tsayar dani a hanya don nasan lokacin umma tana can ta tayar da hankalin ta ganin ban saba kai hakan ba gashi kuma na kasa samun layin umma din. Ina mamaki tun lokacin dana sawo kai na hango motoci a kofan gidan don motocin kawai kansu abin kayar da gabane saidai sanin dan filin namu in baki mata ba na fada a baya cewa motoci na yawan parking a wurin don hilan dake akwai garemu na parking. Haka na karaso a gajiye na parker motana dab da gidan mu inda nakan aje motan in shiga gida har Abdul duk a nan yakan aje motanshi. Haka kawai na dinga jin gabana yana yawan faduwa ban yiwa wa yanda na sama tsaye wajen magana ba . Ila dai nafito da ledan dana sayo masu tsaraban idi,iroko dana tafi din ledan a shake yake da kayan marmari sai dayan da tsaraban Ammar ne a cikin sa daya dameni in sayo mashi unders na maza . Tun daga dan matakalan steps din mu wani kamshi ya daki hancina amma haka na daure na karasa ina mamakin wanan wani irin kamshine kuma ko maniyace ta saka a part din su. Na turo kofan da sallama kamar yadda na saba shiga da sallamana gidan umma i am back na fada tun turo kofan don nasan ranan zansha fada sosai a wurin umma kan rashin kiranta in sanar da ita inda nake a lokacin. Saida maganan ya makale min don hango umma zaune tana sharan kwalla da nayi ga wasu mutum biyu a zaune tare da ita . Saidai sam basuyi kama da iyalan jinsin mu ba don mu din ba bace muke ba don daga hancin mu da giran idanun mu haka manyan idanuwa. Ban damu da ko suwaye a zaune ba lolacin na karasa da sauri zuwa wurin umma din ina tambayan ta da yarbanci su waye me sukazoyi me sukai mata kuma ? Kabo anty sahiba Ammar ya fada daga inda yake zaune a takure na amsa da Ele wooo sai na juya da pigin ina tambayan shi . Waitin dey come do here sunyiwa umma wani abune maimakon umma din ta ji dadin damuwan da nayi da ita din sai kuma ta juya fada dani kan in natsu mana. Wanan shine wanda yasan komai na mahaifin ku sai yanzu ya gane inda muke da wanan maganan ya taso ya dade yana neman mu sai yau ya samu zuwa inda muke. Oda na fada ina mikewa don ni na gaji da burgan mutane a yanzu garemu basu nememu ba a cikin wahala sai lokacin da dadi yazo muna kowa ya taso yana fadin shi shine . Duk bina sukayi da kallo yayin da umma ke fadin ba zaki gaida su da zuwa ba wai meyasa kike hakan wani lokaci. Sai lokacin na dago kai na kallo inda suke daga inda nake tsaye nace you are wellcome ina wuce wa abina . Cikin kunan rai umma din ta kara dakatar dani lokaci guda cikin daga murya lokacin har nakai kofa ina daga labule zan murda handle din kofan dakin. Na juyo ina fadin e dakun umma bafa wurina sukazo ba wa yan nan asalima ban taba jin ko labarin su ba don haka me zan tsaya nayi duk a cikin yarbanci muke magana suna kallon yadda muka juye a yanzu muka zama yaren karfi da yaji ba zakace mu din jinin Abbamu bane mutum mai turaci da rike kabilan shi na fulatanci. Yau sai ga iyali shi sun gani sun gani sun rikide sun koma wasu kabila ko al,adanmu sun juye mun koma kamar kabilun kudu sak. A take idanun shi suka kawo ruwa lokaci guda ya fara magana da tun da ya gabatar da kanshi gun umma basu samu daman yin wani magana ba suke kuka daga shi har ita kuwa din. Look miss Sahiba munzo nan kan pieces ne ba wani abinda kike tunane bane ya kawo mu
Chapter 259 · 0% Book details